Nine 9

1.7K 120 0
                                    

Ammy ita ce fevourit din Hajjajo, sai matan Uncle sulaiman.

Fist wife din shi yar uwar Ammy ce, amaryar kuma yar Abokin sheikh ce.

Hajjajo na son surukanta, bata gajiya da hidimta musu, Kamar su daddawa, kuka, kubewa, yaji, garin kunu, garin danwake dasauran su, Duk ita ke musu ta aika musu. Amma banda yahh Kuma hakan bai taba damun taba, tunda tasan tsakani da Allah take zama da ita, kuma tana iya kokarin ta wurin kyauta ta mata fiye da sauran surukan. Tsakanin yahh da Hajjajo daga gaisuwa, ya yaran shi kenan, In yah zata wuni a gidan surukan nata, Hajjajo bazata ko zauna dakin ba balle suyi dan hira.

Saba nin sauran surukan nata da in sunzo ta fara hidima dasu kenan, ana hira ana dariya. In kaga ta sake da yahh to, tare sukaje da Ammy.

Sheikh na son yahh duk cikin surukan nasa, yafi sonta. Saboda dattakonta, hankali da natsuwa, sannan akwai sanin yakamata, Bata gajiya wurin yi masu alkhairi, musamman turaruka, Sannan lokaci zuwa lokaci zata yi abinci Mai rai da lfy ta aiko musu dashi.

"Aliyu kar in sake jin irin wannan maganar a bakin ka, kaji ko ?" Yahh ta fada tana dan zaro mai ido. Aliyu ya tura baki, tare da daga kai, alamar yaji, Fada yahh tayi ma Aliyu sosai.

Asma da Ashty ne suka shigo dakin sunyi kyau, cikin riga da skeet na atamfa red and yellow, sunyi kyau sosai kamar ka sace ka gudu. Suka daura red din hijab mai hannu. Suka gaishe da yahh, Tare da yi mata sallama, zasuje gidan hajjajo. Daki ta shiga, ta fito da turaren wuta kwalbal bama babba guda biyu, da humra su kaiwa hajjajo. Sannan ta basu humra su kaiwa ummi.

Aliyu na zaune yana home work, ko kallonsu baiyi ba, suma yau basu kula shiba. Asma da zasu fita ta kalli Aliyu, akai saa shima ita yake kallo. Ta watsamai harara, tabe bakin shi yayi, ya cigaba da homework din sa.

Maganar Aliyu ya tsayama asma a rai, Tabbas tasan hajjajo bata son mahaifiyarsu, ita kanta abun na damunta.

Amma yahh kullun takan nuna masu, Ba ruwan su da tsakaninta da surukar tata. Ta sani duk sauran yayyun nata, ba wanda yake shigewa hajjajo kamarta. Don ma yahh na musu nasiha sosai, saboda gudun samun baraka. To amma mai ya sako ta a ciki, da Aliyu zai dubi tsaban idonta yace bai sonta.? Alhali duk yan uwanta ba wanda take jinshi a ranta sama dashi, ko Ashty da suka taso tare, bata mata son da takewa dan uwan nata, yawan tsokalan shi da takeyi ma tanayi ne don son jin muryarsa, da yadda yake shagwaba,
Abin na burgeta, Sai yanzu ta gane, rashin son kulata, da shan kamshin da yake mata, ashe shi son tane bayayi. To laifin tane don tayi kama da hajjajo ? Allah yasa sauran yan uwan nata, basu tsane taba? Ta fada a zuciyarta,  tare da share kwallar data zubo mata.

Sun fito, suka tarar da Ya babba da m bello, Da alama wani wurin zasu. Suka gaishe su. "Sai ina ? "Ya babba yatambayesu"

"gidan hajjajo" cewar Ashty

M b ne yace "ok kuzo mu tafi, in mun sauke ku sai mu wuce." Asma kam tai kici- kici da rai, kamar zata fashe. Yaya babba yace "oya ku shigo mu tafi kuna bata mana lokaci." Ashty kam tuni ta bude kofar baya ta shige, ganin ba yadda ta iyah, yasa itama ta shiga.

Ya babba kam hirarsu kawai suke yi,
Banda su Ashty da suka zam kuramen karfi da yaji.

Asma a takure take, don duk lokacin da ta daga kanta, Idon m bello na kanta. Duk haushinsa ya cika ta, Allah Allah takeyi su isa. Dai -dai kofar gidan sheikh sukayi parking su Asma, suka sauka. Ashty ce tace "mun gode."
M bello yayi murmushi. Tare da kallon mutuniyar tashi da ta hade fuska, abin ma dariya yaso ya bashi.
"No prob" agaishe min da Hajjajo"

Tsokana na cin Asma, Amma tana jin nauyin m bello, da yasa mata ido,  ta madubin mota. harta juya zata tafi, ta dawo dai- dai kunnen yaya babba, da yake glass din window din a sauke yake. "Zanje yan zunnan in ba Amra labarin wannan fitar da za'ayi" tana mai kunshe dariyar ta. Zaro ido yayi, kafin yace komai har ta shige gida da gudu.

"Allah yarinyar nan troble ce, kasan bom din da takeson tada min ?" M b yace "mai ya faru ?" Zataje ta ba Amra labarin wannan fitar tamu, kasan mai take nufi da hakan ?"
Dariya Mb ya fara, "Lallai Asma ta wuce yadda nake tunanin ta."

"Yanzu dai bar wannan maganar, nasan wasa kawai take maka baza ta iya fada ba."

Yaya babba ya nisa, " tama fada, In da rabon in babbala yarinya too."

"Matar tawa zaka balla?"
Ya babba yace "nafa gaya maka yadda mukayi da yarinyar nan."
"So ka rabu da ita kawai ka nemi wata, Ga yan mata nan masu sonka, ka zabi daya kawai mutunina."

Mb ya jefeshi da harara, "Kasan yadda nake sonta kuwa?" Ba zan iya hakura ba, Kawai ka nemo min mafita." "Asma akwai taurin kai, na rasa wacce irin yarinya ce." Inji ya babba ya kara da. "Ka cigaba da addua in rabon kace shikenan, don ni kaina zan so hakan."

A harabar gidan ta tarar  Da Ashty na jiranta. Ashty taja hannun ta, "muje mu fara gaishe da ummi tukunna."
Asma ta dan tura baki, tare da tsaki.
Ashty dai bata kula taba, inda sabo ta saba, Saboda Asma tsakaninta da Allah taya Hajjjo kishi take, bata son abinda zai hadata da ummi.

Hafsat suka samu a falo tana note, Da fara'ar ta ta fara musu sannu da zuwa, suka nemi kujera suka zauna.
Hafsat tace naji dadin ganin ku wallahi, Ashty tace "akwai labari kenan?" "Not much." Ta fada tana murmushi. Bari in kawo muku ruwa, ummi tashiga wanka, amma yanzu zata fito. Hafsat sa' ar su Ashty ce, duka duka wata daya taba Ashty,
yarinyace kyakykyawa, Suna kama sosai da Ashty sai dai ita coculate color ce, sannan tafi Ashty jiki kadan,
Hafsat a kwai kyan jiki sosai.

Hira Ashty da Hafsa sukeyi sosai, jefi jefi Asma na jefa nata, Duk ta kosa tai arba da hajjajonta.

Invitation card ne hafsat ta mika musu," guest what ?" Asma tace "what ?" Hafsat tai dariya "read the card."

Wani ihu suka sa gaba daya........

KUSKURENMU ( Completed )Where stories live. Discover now