Salamu Alaikum. Suffer I'm happy for the support you give me. I'm new
writter but Alhamdulillah. Thanks for the voters I'm wetting for your comments also. I love you all. Thanks
***
DEDICATED TO ALL READERSYusra kin debo ta da zafi, kinaga wannan hadadden guy din zai saura reki?"
Numfashi taja, "Gaskiya nima jikina yayi sanyi, wannan daga gani yafi karfina, amma tambaya a nan ya zanyi da son shi a raina?" Taja numfashi tare da furzar da iska Mai zafi daga bakinta. " bani da zabi, Illah in jaraba in gani,Ki tayani addua sis."
"in sha Allah zan tayaki, sai dai ina baki shawarar karki zurfafah soyayyah, Ki kuma nemi zabin Allah"
*********************
"Kamshi ya isheni, Ashty ki bude ledojin nan mugani." Asma ta fada tana Kara Jan numfashi.
Harara Ashty ta wurga mata, tare da tabe baki. "koma menene a ledar nan ki sani ba rabonki."
"Kin ma isah?" Asma ta fada tana hararar ta.
"Har nayi yawa!!!! Don daga hannun yayanmu ya fito, Sai ki bari, in sauran yayas suka ba da Abu, a raba dake Amma any thing da ya fito daga new brother hara miyarki."
"daga baya kenan? Maryam miko min ice cream dina, kiga in fara dashi, In ga Wanda ya isa ya kwace!! Ya hanani sha."
Maryam ta kwashe da dariya. "Kin makara."
"Kema iskancin zaki min?" "No kawai dai ina bayan gaskiya."
"Naji miko min leda ta!!!" "Ashty tayi kyauta da ita."
"Kam biji biji iskar dari!! A yaushe din akayi haka ban sani ba?"
"Kina can kina shish - shigi." Ido ta zaro, "nice mai shish- shigin.!? "
"inba shish shigi ba, menene? Ke ki kace ba yayanki bane, to meye na cewa zaki nemo mata number din shi, in ba shish-shigi ba." Ashty ta fada itama tana zaro mata nata idon.
"Kuma kinga ledojin nan? Yahuxa suya ne aciki, chicken, liver, kidney,
Kin gani ko, tana nuna mata Kwale lenki, Kinga wannan kuma, farm fresh yeghut ne."Yatsina fuska tayi, "to sai me?"
"Sai kika sha haushi."
"Wai ku don Allah wasu irin yara ne? Kubar mana kunne ya huta, kun ishi mutane da surutu." Asmau ta fada Tana tsaki.
"In dai waannan ne, baki ga komai ba, Yauwa dama ina son tambayarku, a ina kuka San wa Annan yan matan.?" Zainab ta juyo tana tambayarsu, Kasan cewar suna sit din tsakiya, su kuma suna baya.
"Anty zainab kenan, kin San mu da farin jini, kawai sun ganmu a zaune, suka zo muka zauna tare, a haka muka saba." Ashty ta fada tana dariya gasa gasa.
"Tabe baki zainab tayi, Wahala bata ishe suba, Na tabbata basu San the real you ba shi yasa."
Dariya sukayi. Ta tabe baki, ta juya abinta.
Juwaira tayi murmushi "kina son shiga harkar su, bayan kinfi kowa sanin what there capable of."
"Ehimmm ke kanki kina ganin yan matan nan kin san daga gidan wani hamshakin Mai kudi suka fito, Kina ganin su kin san they a classy ladies, In ba rigimar kannen kiba, Waannan ai ba ajin su bane."
Juwaira da asmau su kayi dariya, " Ke kike ganin haka, Amma ke ma kin san kanne na akwai kyau, Wankan ma baza a gwada musu ba." Juwaira ta fada.
"Dama nasan bayansu zaki bi. Allah ya Baku sa'a."
YOU ARE READING
KUSKURENMU ( Completed )
RomanceLabari ne da ya kunshi ilmantarwa, fadakarwa, tare da nishadan tarwa. sannan yazo da sabon salon da yasha banban da sauran labaran da kika/ka taba karantawa.