1 NIDA AMEENATU.

8.5K 311 10
                                    

SHORT STORY.

   Da gudu motar ta shiga Mega plaza shopping mall dake Idowu Martins street, cikin yin wani mahaukacin ribos akai parking d'in motar da kudin ta yakai kimanin 50M Ameenatu 3 shine lambar motar, cikin girmamawa motocin bayan ta suka tsaya, inda saidata dauki mintuna kusan goma kafin ta sanyo kafar ta waje, ido samarin gun suka zubawa kafar tata ganin gaba daya sunan tane a jikin takalmin kumakalar motar kalar takalmin, kamshi ne ya buwayi gun saboda uban turaren datake using dashi.
Riga ce doguwa ta super da akaci mutuncin ta gun dinki tasaka orange sai mayafi data yane kanta dashi, cikin takun ta na kasaita tai wajen shiga mall din, kowa dake ciki saidaya fito sannan ta shiga. Ahmad dake tsaye a gun ransa ne ya baci yace mene haka?, mutane na fitowa kuma wannan securities d'in fa?,  cikin takaici wani guy wanda babansa babba ne a embassy na China yace wai wannan wacce dakikiyar yarinya ce, ina yawan ganin ta a Lapointe coffee ko a winner super markets na kopo abayomi street  wace itane? hmm ai kaidai kawai kai shuru wani abin takaici koh, wallahi da ace wani zai taba jikin motar can ko waye ubanka saitace talaka yataba mata mota akawo wata bazata hau ba, hmm ni kuncikani da magana wace ita ne, me takeji dashi dan naga kowa tsoron yakeyi?, jikar governor ce, kuma baban ta shine Dr Hakeem, 'ya ce kuma ga governor na kudi baki daya,  hmm jika kawai amma take wannan abin, hmm Allah ya kyauta amma wallai akanta sai adaure mutum, kuce ana tsiya kawai. anayi kam. Amma baban ta mutum ne dayasan kansa, dan ko....basu karasa maganar ba saboda jiyo
kas kas kas karan tahowar tane yasa suka dakata da maganar, magana take a waya tana haba Bayyah gaskiya kana yawa da yawa, yanzu ka rasa ina zakaje sai gidan marayu aikamma kafin kazo ka tabbatar da kai sabon wanka dan ban jerawa dakai wallahi kana warin su, tab no zan jiraka kawai, ok saika karaso. Cikin fushi ta fara danna wayar ta kai bakada hankali ne gaskiya talaka bai iya samun waje ba, banda hauka ma kana ganin ina tafiya basaika karaso da motar nan ba, mts ina Lidiya din tafito takamin jakana. Cikin sassarfa wasu yammata guda biyu suka fito daga wata mota da jaka ahannun su, har kasa suka tsuguna suka mikamata, a wulakance ta amsa cikin tsawa tace kunga ga wasu can ku kaimusu sadaka Allah yaiwa Mama na rahma, tana fada wasu hawaye masu zafi suka sauko mata. Duk abinda taake agaban Ahmad ne wanda shi haka kawai yaji tamasa, amma Aliyu jiyake kamar ya kasheta amma ganin yadda tai sanyi lokaci daya sai tabashi tausai. To amma meyasaka take fada akan Yayan ta yaje gidan marayu?, hmm kodan da kansa yaje ita kuma badawa tai......dont know yace aransa.
Lidiya ki kamin kujera mana ku komai sai anfada muku? afwan madam, haka dai. Kyakyawa ce sosai yafada aransa, dan murmushi yai ganin yadda ta tashi a guje tafada jikin wanda take ganin yayan ta, identical twinc yafada domin babu abinda yarabasu komai nasu daya ne, cikin shauki Yayan nata yace My Sisi yane?, inason muje UK gobe fah nagaji da zaman Lagos kwanan nan, hmm kingaji da ganin mu zakice kawai?, haba dai Yaya wanake dashi a duniya sama dakai da Abbu kune komai nawa indai kana ganin dan nagaji dakune yasaka nace zani nafasa wallahi, hmm sai kace gaske? da gaske wallahi. Ko kauye muka koma zaki iya zama?, iyawa kai except if u are not present, but if u where aound zan iya rayuwa can gaba daya...wow sis tafara hankali, ok da bandashi?, bance ba fa bare ki hadamin bomb. Yauwa Abbu fa yace yana neman mu, amma baya gida yana gidan sa na Adetakumbo Ademola street, saikiyi sauri dan inaga ma zan tsaya a Banana  Island gun Abba Mohd, ayya naga kiran sa kam, ok saikizo muje plx idan muka dawo sai muje koma inane.
Salam wannan guy din mai suna Haidar yace, cikin sakin fuska Abdul hakeem ya amsa kana yabashi hannu sukai musabaha, cikin dakiya yace sannu fah ke baki amsa sallama ne? nasan ka, kasanni, kai family nane, ko kuwa abokin yaya nane da zan amsamaka sallamar ka?, plx  stay where u are, nagan kana wani fisga, Yaya idan kagama shakan warin saika zo mu wuce. idan ransa yai dubu ya baci, cikin fushi yace ke wace da zaki kallan kigayamin haka?, hmm kanason sanin wace ni?, dont worry u will know who am I now , text kawai ta tura, Meenatu mene zakiy? plx kiyi hakuri kina daukan komi da sauki a rayuwa ita duniya ba madawwama bace kuma fadan Abbu kullum kiyi hali irin na Maman mu amma sam ke duniya ce gaban ki, cikin tsawa tace ya isheka yaya, akan wannan banzan hallitar zaka faramin wa'azi?, kabari zan samamaka aiki a gidan radio saikafara wa'azin, cikin lallashi yace Meena plx mana saboda yaga shigowar motoci sunfi 20 na police hade da soldiers. Arrest him kawai tace aka budemata kofa ta shige bayan ta janyo hannun dan uwanta.
Duk yadda yaso tasa asaki guy en taki, nan shiima yai fushi suka fara musayar baki wanda takai Hakeem saida ya zabgamata mari abinda baitaba yi ba, tunda ta dafe kuncin ta bata dago ba har suka isa gidan su na Naira land dan sunyi waya Baban yace ya koma gida, yau basu sha'awar kwanan gidan governor wajen kwanan su uku a nan gun Abbun su. Meena ki........kyaleni tafada da tsawa....cikin gida tai da gudu duk yawan securities din wasu ta kansu ma tabi ta shige daidai zata shiga Abbun ta ya hango ta, cikin rawar jiki yafara Ameenatu lafiya waye yatabaki? da gudu ta tafi tafada jikin sa.
Abbu wallahi bada sani na mareta ba, cikin fushi baban yace Hakeem harta kaiku ga haka?, amma kaico na ni Hakeem da har nakasa rike amanar da Ameenatu tabani na tarbiyyar yaran ta, Kaico na dana kasa bawa yaran Ameenatu kyakyawar tarbiyya, sai kuka......jin Abbun su na kuka nan fa hankalin su yatashi da sauri suka jashi sukai cikin katafaren parlor din, kallon su yai yace yau zan baku labarin Maman ku, Maman ku bantaba ganin fadan taba, meyasa mutuwa kika rabani da Ameenatu mai sona da sani farin ciki, gashi kin barni  da yaran ki zasu kasheni. Yaran ki basuson talaka duk da nuna musu danai important din dan adam, Yaran ki basu zamo masu hali irin naki ba.
Abbu kadean fada kayi hakuri zamu canja wallahi, hmmm hannun su yakama yabi wani lungu inda haskene kawai ketashi agun da walwali na wani rubutu, AMEENATU VILLA. shine sunan da aka saka. tunda suke basu taba ganin wannan dakin ba, bude pasword din yai nan ma Ameenatu yasaka, ahankali kofar ta bude suka shiga. wani wawakeken parlor ne da k'ayatuwar sa zata daukeni lokaci bangama fada ba,  pic, ribboms, duk wani kaya na amfani na mata, wayoyi, laptops, kayan sport, duk shine agun. ga litattafai nan birjik komai an kawatashi, pics kam wasu tun tana baby da yarinta da girma da aure abindai abin shawa'awa ga dakin wani sanyin kamshi yakeyi, cikin hawaye yace ku kalla duk wani abu da Amenatu keso ina sonsa ina kuma adane dashi, hata cingum karamin abu wanda Ameenatu keso ina sonsa kuma shina koya muku cinsa, bana tare da gangar jkin Ameenatu amma ruhin ta yana tare dani, ina kaunar ta.
  Abbu mun yarda kanason Maman mu amma me Mama take dashi da kakasa manta ta, ka kasa auren wata?. Hmm Ameenatu ta hada komi, kuma our love is from God. Son Ameenatu yasaka nabar kasata Uk nadawo 9ja da zama, nakasa ganin kowacce a mace, saboda ku nake zaune amma idan har bazaku gyara halin ku ba, zan kashe kaina nabi Ameenatu inda take, ruhina yana gareta, saboda kune na tsaya a duniyar nan dan na kula daku.

IF KUNASO ZANCI GABA, YA KUKAJI SHI?.

NIDA AMEENATU. {Completed}Donde viven las historias. Descúbrelo ahora