13 NDA

1.7K 107 8
                                    

Kamar kullum Hakeem yana zaune a kusa da ita yaga ta motsa, da sauri yakara dubawa yagan da gaske ne, da sauri yai kanta ya ciremata oxygen din, kamata yai yana salati itama tana tayashi, cikin dauriya tace sannu fav Allah yabaka ladan jiyya, Ameen yace kawai. wanka yamata yasakamata wata simple doguwar riga, kyau yaga tamasa hakan yasa ya matso a ita jikin sa yanamata pics...Fav nafika kyau fa a pics din nan?, aidama Ameenatu na maikyau ce tafini komi....magana zatayi yakadamata kai, dole ta tsuke bakin ta.
Mama ce ta shigo saiga Yayun ta ma haka, My Husnah glad to see u, me too sweetheart tafada da hawaye, mene na kukan bayan gani kuma kibari na mutun saikiyi, zama sukai nan kowa yasata gaba me take so all her wishes suke neman ji, kuma idan tana musu magana basa katseta har saita gama, sosai suke hira idanun tane ya kallar mata Hakeem wanda kallo daya tamasa tagano what he feel, cikin sanyi ta matsa kusa dashi tace fav zo muje gida inason nunamaka wani abu, Ameenatu........nidai kawai kataso, ba yadda yai kodan farin cikin ta haka ya dauke ta a hannu suka fice bai direta koina ba sai bedroom din su, kallon juna sukai cikin ido, hannun ta tasaka a gashin sa tace i need u, cikin kidima yace bakya ganin halin da kike ciki? wannan shine last wishes dina a duniya plx kajiyar dani dadin da bantabaji a atare da kai ba.
A wannan ranar sun more junan su, wata kulawa sukabawa junan su ta masifa ma, saida suka kimtsa jikin su kana wani mahaukacin son junan su ya shigesu, kasa magana sukai illa kankame juna da sukai suna kuka na mutuwa ma, sunjima a haka kafin ta lallashe shi suka koma asibitin wanda zuwan su yai daidai dafara nakudar ta, ganga ganga akai da ita labour room, wani masifa kuma numfashi yace baisan wannan ba dan already ma her breath is shortness, ga heart rate goma da ashirin, amma karfin adduar yan uwa cikin sauki Allah ya sauketa lafiya inda ta samu triple 2 boys one girl, murna kamar zasu kashe kansu, wannan ya rungume wannan, wannan ma haka, shikam hakeem da Mama suna gunta, matar sa kawai yake kalla. Da kansa yakaita dakin hutu duk wani abu shiyamata, zama yai kusa da ita yakasa matsawa ko nan da can hawaye kam ba magana yauce ranar dayake tsoro a rayuwar sa, baitabajin inama inama ba sai yau, da'ace ana bada rai wallahi zaibawa Ameenatu nasa ta rayu, da zai iya kuka da birgima ya roki Allah ya jirkintawa Ameenatu kwanakin ta da yayi, dayasan wannan ranar Ameenatu take tsoro da tun farko baibari sun zama abu guda ba, da ace zai iya sakagon roba ya ajiye da yayi, amma Ameenatu tafi karfin haka gunsa, ga yara Allah yabasu amma uwa ranta na hannun wanda yayi ta.
Kansa ya kifa a jikin ta yanata kuka ahaka kowa ya shigo ganin yadda yakene yasasu komawa da murnar su ciki, yaran su tubarkallah biyu suna kama dashi macen kamar Ameenatu tayi kaki ta ajiye. Kasa karbar su yai illa idanu daya zuba acikin haka AMeenatu ta farka cikin halin ciwo da azaba da radadi tace Fav mena haifa?, yaran aka mikamata masha Allah abainda Ameenatu ta haifa kenan?, Allah yarayaku cikin islama. Naso zanyi tsawon ran da zanga girman ku, naso dama ace ni zan muku wanka nakama wa babyn gashin ta nasakamata ribbons, inama zan kai wani lokaci naga yadda zasu ringa rigima muna sasanci, Mama naso ganin yadda zanfara kishi idan naga kinfi sonsu akaina, Ya Musty harna hangoka kana musu wasa kanacewa baby tafini kyau. Mom dama zanga lokaciin da zakice mubaki baby fav yace a'a nabaki naga fushin sa, Fav yanzu duk saidai kai zakamusu komai, mafarki na naganin muntafi saudi da shiga malls nida yaran mu bazai tabbata ba, amma babu komai tunda har Allah yaban ikon haifar su, naso na shayar dasu naji yadda akejin zafin, yanzu duk dawainiyar da zanmusu ta koma kanka fav, kamusu tarbiyya tagari, ka sosu, amma kada ka musu son da zasu lalace, ka kula da kawayen da zasuyi, Mama kada kimin kuka ranar da akace bana duniya, adduar ki itace nake so. Mama plx kuyi yadda ruwan Nono zaizo inason nabasu su sha ko yayane....cikin sauri Hakeem yatashi ya fita wani magani ya dauko..yadda yakemata da can saiya tauna saiya bata haka ma yamata yau....bata jima ba kuwa nono yazo, nan aka bata yaran duk zafin datake ji hakan bai hana murmushi bayyana a fuskar ta ba. Saidata tabbatar sun koshi sannan tabadasu, nacika burina , na haifa, na shayar, kuma nazauna da miji na lafiya, zan mutu Mama na na raye, zan mutu ba hakkin uwa dan nasan Mama zata yafen zan mutu ba hakkin yayu da miji nagari, nasan da ana bada kyautar Aljannah Hakeem tuni yaban koh?, kai ya iya kadamata kawai saboda dacin da maganar ta takemasa a zuciya da baki.
Taj yanzu duk labarin Hanadi da ake ban bazamusha biki ina nan ba?, Taj ka rike Mom ka nunawa Hanadi muhimmancin mom, ku yafeni duk wanda naiwa laifi ya gafartamin, Kakus kiyafeni kema, Baba da Mama kuce kun yafen naji da kunne na, dan ALLAH KUYAFEMUN shurunku yana nuni da namuku laifi kenan?, amma duk girman laifin da zan muku tunda na bukaci yafiya yaci ace kun yafe.........wani irin kuka ne na tausayi yake tashi a adakin, Hakeem kansa ma ya kwance gaba daya yarasa mene a duniyar da shima mutuwa bazatazo ta dauke shi ba.
Mom na nemi alfarma agunki?, Ameenatu komene wallahi zanmiki dan kin cancanci komai, Mom idan nabar duniyar nan ki taimaka kibawa Mamam na Hakeem yakoma 9ja da zama, Mom yaron nan nawa daya ki daukeshi mun baki shi, Mama ga Ameenatu nan da Hakeem kirikesu keda fav kuyi rainan su kuduka harda su Yaya kubawa yarana tarbiyya tagari wadda zanyi alfahari cikin kabari na, kubasu tarbiyyar da alumma zasu amfana dasu sai kuka yaci karfinta anan hade da wani ciwo wanda takasa tantance daga ina yake tasowa ina yake tsayawa. Hakeem kuka yake na zuciya da ace zai iya zukar jinin ta yasaka ajikin sa shima cancer ta kasheshi da zaiyi, amma Ameenatu tabashi amana idan yai haka zai rasa lafiyar da zaibawa yaran Ameenatu tarbiyya da kulawa.
Taj kamana pics mana, nan sukaita hoto wani videos ne duk na bankwana, yaran ta daukan su tai, AMeenatu kece karama inason kiyi halina duk da bansan ko maikyau bane, kibi Dadyn ku, kiso kowa ki kaunaci talaka kada kizama mai dagawa da girman kai, kisaka aranki Maman ki na snki dole ce tasaka zata barki a lokacin da itama takeda bukatar zama tare dake. Kaf yaran haka tagayawa kowa duk Taj na dauka, saidata gama sannan ta lalubo hannun Hakeem, cikin hawaye mai narkar da zuciya tace fav fatan banmaka shishigi ba?, danasawa yaran mu sunan mu, kasawa babban da kanka....meenatu komai kikai daidai ne shima kisakamasa, ni na yardar maka kasakamasa, cikin kunci da radadin zuciya ya kautar da kansa gareta saboda bazai juri ganin halin da take ci ba yace nasakamasa sunan Dady na, murmushi tai tace hakan shine wishes dina, love u....hannun Mama takama tahada dana maleek dana yaran ta rike sosai daga nan ta riko hannun kowa har su Hsnah da Deedoh Aunty Haleema da Zainab duk kuka suke kowa yana inama zai iya bata nasa ran daya bata.
Fav wani laifi namaka da bazaka kallen ba?, bakimun laifin komai ba kawai dai idanun bazasu juri ganin ki a halin da kike ba, nikuma nafison ka kallen, juyo da fsukar sa tai kiss tamasa kafin ta rungumeshi sosai, wani tururin zafine ya daki jikin sa, cikin dauriya tace tell me how much u love me?, i love u morethan enought, thats my lovely husband, wacce mata zaka aura?, ke daya ce, Fav akwai pain acikin mutuwa?, death is not always painful, some died without any pain at all, good girl like u zaki mutu ba wani ciwo yanafada yasaki wani kuka ga kirjin sa na masa suya shi kansa numfashin sa kokarin daukewa yake.... plx fav stop crying, when i see u shedding tears, my heart aches for u, i stop it Ameenatu yafada yana toshe bakin sa, cikin kulawa tace fav before i first saw u, I meditated for more years, but those years, were worths lessthan a moments with u, u make my day and my dream, i promise i will not married till my life, for the presents of u i made, ganin ka yasanafara jin feeling and wishes i love u.
Rungumeta yai sosai yana kuka da karfi yana jijjigata yarasa ina zaisaka kansa yaji dadi duk inda ya juya maganganun tane suke masa yawo, Ameenatu ur eyes linger in my mind, i can bear any hardship to be with u, our love should remain in our minds, nothin can change our love in my heart, nothing at all, i vow to live for u till the end of my own breath....numfashi yaji tana jaa da karfi kamar kokawa suke dashi, hannun sa ta damke, dayan kuma Mama ta rike kallon su take......Hakeem yana ganin halin da take ciki yasan alkawarin Allah yazo karshe, kwanakin data debo sunzo karshe, shan ruwan ta da numfashin ta ya yanke, kalmar shahada yafarayi yanayi yana kallon ta amsawa tafarayi idanun ta na cikin nasa.......wani irin ajiyar zuciya tasaki daga nan rai yai halin sa.
Ihu suka saka kowa yai kanta yana jijjigata, amma inaa Ameenatu lokacin tafiya yayi, tazama gawa, tazama da ita da babu duk daya tunda bazata amfanu ba....Ya Musty kansane yasara wanda yasashi zubewa shida matar sa a tare. Hakeem mutum mutum yazama ga hannun sa dake cikin nata, wani annurin haske fuskar ta ke fitarwa, yakasa dauke idanu da kant, saida Mom nasa ta taboshi.

Plx kuyi hakuri masoyan AMeenatu, nikaina littafin na taban zuciya, inaji kamar nice Ameenatu........ba'a komai ake happy end ba a rayuwa akwai jarrbawa.+

NIDA AMEENATU. {Completed}Where stories live. Discover now