3 NIDA AMEENATU.

2.3K 138 2
                                    

A jirgi suka tafi, inda ko a jirgin ma abincin ta daban yake, Yaya nikam nagaji dan Allah kabani green tea naka nasha, juyowa yai cikin tausai yace haba Meenatu kina jin magana mana, lafiyar ki tafiyemana komi, wallahi da'ace bayada matsala arayuwar ki zan baki kisha, kuma koda ace ciwon ki zai dawo kaina wallahi zanso, kici sald dinki kawai da berries tunda akwai plx, hannun sa takama cikin lallashi tace haba Yaya na ai cuta ba mutuwa bace, kuma ai da sauki ma ciwo na akan wasu, kalli babu abinda ya sauya ajiki na, kamar ba ciwon saidai idan ko ya tashi, haka ne amma ninasan mece cancer, tana raba mutane ne lokacin da suka nutsa a kauna da dokin ganin juna koh?, karshe kace mutuwa to ai ba zama mukazo ba dama, duk jimawar da zan zan tafi wataran na barku, ko nabar wasu, Meenatu canja topic naga kinfara sakin layi.
Naji na canja, yauwa wai har yanzu shuru wallahi idan kuka tsufa bamai auren ku, nak'agu naga bikin ku wallahi, nagaji da ganin bikin jama'a , ke muke jira wai?, tab kenan zaku mutu bakuyi ba dan......ke ya isheki haka, Ya Mohd yafada cikin fada duk da zuciyar sa cike take da rauni da tausayin yar kanwar tasu, a haka suna hira har suka kai kano ta dabo. Gidan kakar su suka sauka inda itama kakar saidatasha kukan ciwon jikar tata kana akai shuru aka dasa hira. Kwanan su uku suka juya inda awashe gari ita kuma hutun ta zai kare, ta zagaya dangi sosai kafin Ya Musty ya maidata hade da dan fadan nan na yayu na a kula da addini.
Shekara kwana gash sannu a hankali kuma yau da lafiyar gobe babu a haka Allah yacikawa Ameenatu burin ta na zama cikakkiyar likita, bayan ta shafe shekaru biyar tana karatun ta, kuma Alhamdulillah ga karatu ga hadda da wasu hadisai suma duk ta samu, kuma alokacin nee cuta tafara kamata gadan gadan, dan ko a ranar da zasuyi graduation ita nata agadon asibiti tai, inda kana ganin ta kasan taji jiki, hannayen ta duk sun sage bata iya komai, oxygyn cema ahancin ta, Dr John da yarsa sunkasa hallartar taron saboda yadda sukejin Ameenatu aransu, sun dauketa kusan yar uwa shiyasa ko a asibitin bible ne a hannun su sunata yimata adduar dacewa. Kwanan ta uku sauki yazo, inda kuma kasan bata taba cuta ba, da karfi saukin yazo, aranar kuma sauran students zasuyi nasu partyn, haka suka shiga akai dasu, amma anan ma saida akagayyato manyan mutane dan nunamussu yarinyar data dauki fist class, tasha kyauta ankumayi pics sosai, turawan nan kowa kuka yake na rabuwa da salahar kawa, mara son kanta.
A gida Nigeria Ameenatu hutun lokaci kadan ta dauka tafara samun iyayen ta da maganar tanason abudemata makarantar Islamiyya, kuma tanason tafara lecturing da kuma aikin asibiti amma kyauta tana fatan ladan yaje kabarin ta kafin itan taje. Ameenatu bakyaganin yadda jikin yake?, kinason sawa kanki abinda bazaki iya ba, gaskiya aguna kiyi hakuri ki zauna mu kula dake da shan maganin ki rayuwar ki na cikin hatsari da tension din jikin ki zakiji kodana dalibai, ko majinyata?, Baba naji bayanin ka na kuma gamsu, amma inason kamin alfarma ka barni nai abinda nai niyya, Baba rayuwa ta gajeriya ce kuma kanaji Dr yace ina matakin da idan nakara kwanciya za'a k'ayyademin kwanakin da zanyi ko shekaru, ina stage na 3 yanzu kaga kenan saurana last stage shine na 4, Baba aljannah tame rabo ce amma inason samun ta tun a duniya, inason nabawa al ummar annabi ilimi wanda zasu amfana ko bayan bana nan zasu taimaki kansu, kuma zasumin addu'a, Baba inason na taimaki marasa lafiya marasa karfi ko bayan bana nan zasu tunani, Baba inason nai hakan kodan nabar bayana da kyau, Baba har yanzu bankai shekara 25 ba, babu kuma abinda naiwa addini na hidima, bankuma san kona kyautata sallah ta ba, bansan ba kona muku biyayya wadda zatasaka ace yau banda hakkin ku, amma kagan idan nai haka ko babu komai inada yakinin zan samu addu'a, Baba kataimaka kabarni al'umma su mori ilimin danai, kataimakan kodan farin cikin da zanji, ka yarda kodan zan samu sanyin rai idan naga jama'a, kuma koda ina cuta addu;ar su zatakamin sauki. Da kuka sosai Baban ya rungumota yace Ameenatu wallahi nabarki, wallahi Asibitin ma gina miki shi za'ayi kowa yazo kyauta, Amenatu na yarda da maganar ki kuma koda dukiyata zata kare ne wajen kyautatamiki wallahi saina cika burin ki, Ameenatu Allah ya inganta lafiyar ki, Ameen Baba na kacikan buri na na duniya.
Yadda mahaifinnta yaimata alkawari haka kuwa akai cikin sati guda aka tashi gini, wanda kwana akeyi anayi, wannan idan sunyi wasune zasuzo a haka har asibiti ya kusan kammala, Dr John ne yai jagaba wajen siyan manyan injina na aiki da sauran abubuwa. Islamiyya kam ta kamalla ansaka tallan ta a gidajen radio cikin kwanaki kadan ajujuwa sunfi goma yara da manya, Malamai aka debomata wanda zatana biyan su 50k duk wata, kafin wani lokaci makarnta ta bunkasa da daliba, kuma kowanne aji ita kemusu karatun alkur'an domin shine burin ta.
Baba yau dai inada lokaci inason nakaiwa Husnah ziyara da kaina zan driving, a'a Meenatu keda....Baba nifa lafiyata lou, to Allah ya kiyaye, ai Mustapha ma yanacan, kamar Yaya?, yace wai yasamu matar aure, masha Allah nai murna yasamu mata tagari kam, ai yarinyar nada hankali wallahi, gaskiya kam. Hmm ni Ameenatu tadena yayi na komai Baban ta yanzu, wace ni da cewa haka, Mama na aike ta daban ce, kullum kan na kwanta saina tunaki ko ya zakiji randa akace bana nan?, kodayake ga Husnah kinsamu, Meenatu bar maganar nan ai cuta ba mutuwa ba, kuma sanin gaibu sai Allah, nawane masu lafiya suke mutuwa subar mai lafiya, nawane wadan da akasakamusu rai da mutuwa suke kuma cigaba da rayuwa?, na yarda da batunki Mama, amma ai ita cancer komai nata daban ne, indai tafara cinka dole ne bazakai tsahon rai yadda mai HiV ZAIYI ba, Ameenatu i love u baraki mutu ba sainagan jikoki na, tashi maza kiyi sauri kije, Mama na batason gaskiya tafada da dariya, dakuwa ta aikamata dashi, cikin sauri sauri ta mike tace Baba kana gani Mama na zagin ka......to sharri kika koma kuma?, ba wani sharri.
dakin ta ta haura wanda tundaga bakin kofa komai nata ya sauya, red paint ne, kofar ta bude, wani sanyin kamshii ne ya ziyarci hancina danake dauko muku rahoto, wow iya tsaruwa dakin ya tsaru, komai red ne sai adon frames na sunan Allah da Ayatul khursiyyu da su Yaseen duk sune a dakin, suma kansu cikin su red ne, kayan jikin ta tacire ta dauka towel da dan waken ta tashiga toilet din, wankan ta tai cikin annashuwa kafin ta fito tajanyo kujera tafara kwalliya sosai tai kyau, doguwar riga tasaka wadda ta fiti mata da ainihin kyawun ta, kuma ta boye ramar datayi, gashin ta ta kalla, a hankali hawaye ya zubomata saboda ganin har cutar takai matakin da gashin kanta ma yafara cinyewa, idanun ta takalla suma sunyi ciki amma hakan saiya karamata kyau, jikin ta kam tabbas ya rame saidai dake tanada kira ba wanda zaigane cuta ce ta ci karfin ta, hatta tari idan zatayi saitaji ajikin ta, kwarai takeshan wahala amma yazatayi idan bata tsaya tai yaki da cutar ba, bazata barta taiwa al'umma amfani ba.
hawayen ta goge kana ta dauki jakar ta da kudi sosai ta fice, Mama nai kyau?, sosaima kam kamar a India, hmm nafi yan INDIA kyau fah, lahaula inji wani makaryacin Ya Musty dake shigowa yafada, a'a Ameenatu na fa mai kyua ce kaidai dan tafika kyau ne, yauwa gayamasa dai Mama, aini madarar kyau ce, dan a cuta tafara cinyewa, kodayake ba kyawu a fuska ba, kyawu na zuciya akeo koh, koda nazama skeleton indai har zuciyata zata buga da kaunar ma'aiki bazanyi kuka ko kaico akan haka ba koh Mama?, haka ne Meenoono na, ooo banson wannan sunan, Yauwa Ya Musty ashe.....eh Husna nakeso shikenan kema fah kin iya gulma, nidin aikam zakaga gulma zanje ai yanzu zance kai dukan mata gareka, rufamin asiri yarinya nagama yad'a manufata kice zaki ruguza?, hmm to kuma bikin yaushe?, wata biyu Ameenatu na yamiki?, aikam yayi amma dama sunjima suna son juna?, sunjima sosai, ok ni zan wuce saina dawo, tom.

votes.....comments....share.

NIDA AMEENATU. {Completed}Where stories live. Discover now