4 NIDA AMEENATU

1.9K 142 2
                                    

 
                                                     4 NIDA AMEENATU

Tafe take cikin motar ta kirar Ranjrober red colour tanajin karatun al'qurani cikin sautin Malam  Ja'afar tanayi tana bi a duniya babu yanayin dayake mata dadi, irin yanayin datake ciki a yanzu, ba go slow kamar yadda ta zata dan ba'a wajen su Agege take ba bare tace zata wahala, kuma gidan su victoria island  dake anyi gada bama saika hau wani kwale kwale ba, can ciki ne dai wajen beatch saika hau. Unguwar su dake Adeniran Ogunsaya taiwa tsinke dake cikin Sureleri katafaren gidan su kawar ta ta Husnah ta dosa inda horn daya tai aka budemata, cikin tafiya a hankali take shiga hatta tsaya a parking area, da gudu Husnah tafito taa oyoyo mara zumunci, lahaula kaico na kuwa idan har akace anwayi gari bana duniya kuma aka kasamin shaidar zumunci mezancewa Allah?, hmm Redy kenan wasa nake miki, a rayuwa ta na tsani kalmar mutuwa da kike ambata raina kuna yakeyi wallahi, to naji ni mushiga nagaida Mama, kuma yau da yunwar wannan mahaukacin shayi nazo mai sirri , mai madara koh? oo mai kayan hadi,  ba'agidan nan ba kam, dariya sukai nan suka shige.
A kasa sukaga Maman Husnah nan suka gaisa kana suka haura sama, hira sukai sosai, daga nan suka fice sai gidajen kawayen su, ranar taji dadi sosai domin kuwataga kawayen data manta dasu, saida taga Mama ma na buga mata waya sannan Husnah tasaka driver nasu tace yabiyo bayan su ita kuma tarakata har gate din gida, bazaki shigo bane?, ke rufamin asiri ....hhh wai kunya bah, to nagode sosai Husnah sai munyi waya.
Asibitin ta ya kammala, so yanzu Ameenatu batada zama kullum tana hanya ganin patients da kuma lecturing sosai tai keeping kanta busy, kuma anasamun cigaba dan jikin ta sauki sosai yakeyi, sai abin da ba'a rasa ba, ga biki ya matso ga Husnah ta dage itace kan komai gashi kuma lokacin ne take samun patients wadan da basuda yadda zasuyi, dole dai tabawa Husnah hakuri dan taimakon marasa lafiiya shine burin ta, kuma ya cika bazati wasa da damarta ba.
Yau ne dinner kuma yau takeda operation na wani mai ciwon hanta, kuma ayau din zataiwa wata yarinya chemo da Gene therapy mai irin cutar ta, shiyasa hankalin ta sam ba'a kwance yake ba, ga tausayin kanta ga tausayin yammatan  da baifi da shekara biyu ta girme su ba, ita anso amata amma ta karanta tagani kuma bala'in da azabar dake cikin chemotherapy shine the most things da idan akai dace akaiwa mai cancer yake samun relief na 50p na cutar, ko shi ko Immunotherapy.
  Ameenatu kinason kice bikin mu bayada muhimman ci a gunki da kika zabi bare damu?, nashiga uku wallahi Husnah ko daya, yanzu Ya Mohd ya kirani ma nace masa zanje, hmmm ko kunshi bakiyi ba bare saloon, ohh Husnah kinga baranaiwa Dr Jafar shida Dr Tasiu {my Emirates guys} magana nace su hada kayan aiki, sukuma sanar musu su shirya yanzu za;a shiga. Ke kuma uwar masifa saiki kaini kunshin, amma ba saloon, saboda me?, so kike gashin yafice, ko kin manta cancer....plx is ok zo basaikin sakarmin da gwiwa ba. Haka akai kam gidan kunshin takaita dan matar yar Chadi ce kunshi takeyi sosai har gida taje taiwa su Husnah, ita tazata Ameenatu tayi saida Ya Musty yagayamata shine ta biyo ta. sosai aka zanamata ja, awa daya da rabi yai tasaka rigima dole aka cire akasaka baki, ana gamawa zata mike Husnah tace wallahi sai anmiki gyaran jiki da wankan kamshi, ba yadda ta iya dole haka ta zauna akai, amma ita kanta tasan tai kyau sosai, batai gida ba illa waya datai asibiti tace su shiga da wadda za'ayiwa chemo gata nan zuwa. Husnah yau zanga mai irin cuta ta zanmata aiki zanmata kokari ko zatai rayuwa mai tsaho, kafadun ta Husnah tadafa, cikin kwantar da murya tace inamiki fatan nasara, tnx Husnah....amma jikina fa a sanyaye yake...dont be afraid zakiyi cikin nasara har mai Gene din.....tnx much.
  A asibitin ta sauketa tai gaba ita, alwala tayi ta jima tana adduar samun sauki wa yarinyar da kuma samun nasara, uwa uba fatan ta samu kwarin gwiwar shiga ai aikin tare da ita, dan ta sare jikin ta ya mutu saboda yadda yarinyar kafar ta ke wari ga shi kanta duk ya sauke, idanun ta sunyi wata kala, bakin tama haka shiyasa take tausayin kanta kenan ita da bata samun kulawa haka zata koma,  tana cikin addu'ar Dr Ameera Aminu Bako ta shigo itada Dr Jaafar, sauri tai ta shafa, yauwa ni ake jira bah?, kansa ya sunkuyar cikin kunan rai yace Dr Allahn da yayita yafi bukatar ta a gunsa akan yabarta damu, cikin kidimewa tace me kake son kacemin?, wa'adin data dauka ya cika, name fah?, alkawarin Allah yacika akanta, kuka Ameenatu tasaka, nashiga uku nima nasan ina hanya, Allah yajikan ki F'atee kinyi shahada Allah yakai hask'e kabarin ki, kasa zuwa gun gawar tai, illa ta'aziyya dataiwa iyay'en ta da kuma kudi data basu, Maman yarinyar kanta tausayin matashiyar likitan take baran da taji irin cutar su daya da 'yarta, sosai taji mutuwar adaddafe aka shiga da na biyun sukai masa aikin sha biyu na rana suka fito daga aikin kuma aikin was succesfully.
Gida ta koma tta hada kayan da zatayi amfani dasu ta tafi gidan su Husnah, Maman taso ta zauna azo amata amma tace Mama zanji dadi idan naje can kuma ma .......uwar tsari Allah ya kiyaye, dariya yan uwan ta sukai, itama hakan kana ta fice.
Mai make up ce taje Amalili wadda tundaga kasar waje takoyo kwalliyar yar uwa ce ga Husnah shiyasa ma tazo gidan da bazata je ba, kwalliya tagani ta fada ta zauna tana tsantsara musu hatta gyaran kai style iri daya akai musu kaf har sauran matan yayun ta dan sunsan juna sosai, sunyi masifar kyau, Ameenatu kam kamar ita tayi kanta dan kyau gold kam yai aiki a jikin ta kayan ta kam yafi na amaren kaf tsada da kyau, pic suka dauka daidai nan kuma motocin daukan su sukazo.
Ameenatu cikin motar Ya Musty ta shige tunda Husnah ce kawar ta, wow sis Allah kaimu naki haka kinyi kyau over.....saidata karkace tace nasan nai kyau ai.....murmushi yai mata kawai amma hannun ta na cikin nasa kwarai yau takara bashi tausayi kyau har kyau amma cuta naneman kashemata kyan ta. Amaren da angwayen ne karshen shiga inda MC yafara kirari da roko na sanar da shigowar su, kowa idanu ya zuba ganin yadda shigowar tai tsari, haka amare suka zauna a inda aka tanada dan su, Maama ce tace ku nibanga diya ta ba?, zata shgo ne inji wata kanwar Maman, itakam tana can, amsa waya take akan anduba wani magani babu, cikin nutsuwa take musu bayani akwai Lamivudine ko Zidovidine tunda babu Tenofovir din duk aikin su daya zasuyi treating din virals infection kuyi using dasu, acan kuma kawayen amaren da abokan angwayen ake kira dan subada biography din su, kowa yatashi ana zuwa kan husnah aka fara kiran Ameenatu..... ita kuma daidai nan tagama tana shirin kara amsawa wata wayar tajiyo mc bashiri ta juya ta shiga. Hasbunallah kalmar datake tashi kenan cikin hole din, dan gaba daya ta ruda samari da yammatan wajen, Mama kanta kusan batagano yarta ta ba, tsayawa tai cikin wani danyen english tafara bada tarihin amarya Husnah tanagamawa aka dau tafi saboda ta burge, nan kowa yafara kasheta da flash a haka ta sulale tai gun Mama.
Anci ansha ankuma danse, Ameenatu mutanen da sukamata liki bazasu irgu ba, danma ita ba gwanar rawa bace da wani sakewa da jama'a anjima agun kafin aka tashi.

plx vote, share and more comments, yanzu labarin yafara....muje zuwa NIDA AMEENATU.

NIDA AMEENATU. {Completed}Where stories live. Discover now