6 NIDA AMEENATU

1.6K 95 1
                                    

  Cikin wahala Ameenatu take rayuwa amma ko kadan bazaka gane hakan ba, dan tana iyakar kokarin ta ganin ta karfafa jikin ta kodan samun kwanciyar hankalin yan uwan ta. Yaukam tun safe ta tashi da wani mugun stomach pain together with trouble swalling tayi kokarin kare kanta da shan magungunan ta Oxymorphone, Mathadone sune wanda take sha a yanzu dan tun kwanaki taga Codein da Morphine sundena mata wani aiki a jiki. duk yadda taso ta karfafa jikin ta takasa dan wani tari ne ya sarke ta wanda dole saida Maman ta tajiyota duk son ta da rufe bakin ta da gudu ta haura dakin ta a yashe ta ganta akasa duk ta galabaita numfashin ta ma kokarin daukewa yake dan kaiwa da komowa yake, ihu Maman tasaka tana Alhaji kazo zamu rasa Ameenatu Ya Allah ka kamin dauki ban shirya ra buwa da yata yanzu ba, Allah kashiga lamurana Ameenatu itace sanyin idaniya ta kuka sosai take  duk wanda yake gidan saida ya zubda mata da kwallah, Yayun ta kaf zagaye suke akanta amma ita kanta batasan wanda ke kanta ba, Abba yakamata akaita asibiti aji wani abu zasu ce? Mustapha narasa hankali na ne bany tunanin akwai asibiti ba yafada cikin kuka, Maman kam gaba daya ta rungume ta tana jijjigata Ameenatu kidaure kada narasaki cuta ba mutuwa ba ki cigaba da karfafa jikin ki banson narasaki kowa na gun kuka yake a haka Ya Musty ya dauke ta sai Redding Ton Hospital, da zuwan su daa gudu likitocin suka dauke ta sai ICU danbata taimakon gaggawa.
Cikin ikon Allah da kuma adduar jama'ar ta wanda sukaji cutar tata agun masu aikin gidan su da iyayenta jikin ta yafara sauki amma dole saida aka samata oxygen dan breath dinta yai short she cant breath well. kwanan ta shida jikin ta yai sauki amma fa a fuska dan a yadda takeji kamar ana sassaramata jiki ne gabban ta sosai sun raunata dan komai slowly takeyin ta, Abinci kansa bata iya ci dan babu appatite a bakin ta kwarai, Deep fried sai cinnamon da vegetable sutake iya kaiwa bakin ta wataran kuma Meatless. Yayun ta takan rasa wane yafi son ta dan kaf gidajen su suka bari suke kwana da ita tana cewa wash kowa zai taso Ameenatu menene? wani gun namiki ciwo ko zakiyi fitsari ko tashi zakiyi? irin wannan tambayoyin a kullum su suke mata.
A yau aka sallameta inda yan dubiya kamar sa tsaga gidan, Deedoh dasu Husnah kawayen ta kullum suna gun ta hakan ba karamin faran ta ranta yake ba, tasan ko yau ta utu akwai wanda bazasu manta da ita ba. Iyalan Alhaji Abbas kaf sune cikin katafaren parlour din inda suke tattaunawa akan matsalar kanwar su bayan sungama yanke shawara da Baban Antonia Dr din ta na LOndon, cikin sayin murya Babban Yaya yace ni nama yi magana asamomana visa dan ba tsayawa zamuyi ba, jikin Ameenatu yafimana komi, hakane Yaya amma kafin nan yakamata mu tambayeshi yaushe yake ganin Doctor din zai dawo? bakaji ba yace nan da kwana uku zai dawo shine chief fa na BLK CANCER CENTRE SPECIALIZE, baban sane ya bukaci yadawo kusa dashi shiyasa ma zai dawo London din, kace babba ne? sosai kuma muna saka ran zamu dace acan insha Allah, Allah ya yarda. Ameenatu najin jiki dan ma tanada kokari, sosai ma shiyasa take ban tausayi wallahi, yanzu visar ta mutum nawa kabada? kaf din mu ne, hakan yayi sai afara shiri, Maman ce tace Allah yamuku albarka kuma Allah yabaku masuyimuku, Ameen Maman mu Ameenatu tafada bayan ta sauko daga upstairs, hannu kowa ya mikamata tazo gunsa dariya tai ace kujiku ga uwata gunwa zani kuja can, tab ni kikaiwa haka? yo har Baba ma namasa bare kai.........zakice ai nakaiki unguwa ko shan coffee? hhh Yaya ainazama vegetarian nadena shan coffee kuma ko yanzu nace dole a siyamin da gudu, banda ni kam bacci na zansha na more. Mama kinjishi koh? rabu dashi dolen sa ya kaiki koma inane.....dariya taimasa nan suka shantake sunata hira har 4 tayi inda Ameenatu ta nuna zataje Asibiti cikin lallashi Maman ta hanata ta nunamata tabari takara warwarewa, bataki ba illa cewa datai nidai to gaskiya nagaji da zaman mudan fita koma muje Surelere gun Adda hafsa kagan mun kwana biyu bamuje ba< Autata naga jiya tazo fah? auu na manta fah bikin Sodangi da Sdiyan gwaggo ya matso inason siyan takalmi a Ikko sai muje kawai? kuma zani Oshodu nasai lace, haba yammata any kind of shoes and colour kinada mezakiy dasu? ihu tasaka na shagwaba tace wallahi saimunje nagan so kuke ku hanani fita dariya akai duka kafiin Baba yace Ameenatu zakifitamana jeki sanyo mayafin ki dakaina zan kaiki koina kike so....thats my Dad u are the best tafada kafin ta mike da sauri tai sama da idanu suka bita duk yadda Ya Musty yaso mayar da hawayen sa yakasa baisan lokacin daya fashe da kuka ba kafin ya mike ya shige dakin Maman su, murmushi uban yai kawai yabi yaran sa da idanu wanda sukabi bayan dan uwan nasu.
akwana atashi na Allah gashi har visar ta fito kuma sai shirye shiryen tafiyar suke. Ameenatu jikin ta yanabata abubuwa da dama atafiyar dan kusan doki ma take idan ance Amenatu murnar ta mece? takance nai missing franca, Antonia jacks.....da kowa ma, zangan su ai dole nai murna. sosai sukai sallama da duk wanda yakamata kafin jirgin su ya lula zuwa UK. D a saukar su suka hangi Dadyn Antonia kwarai sun yaba da kirkin sa, gaisawa sukai kafin ya rungume Ameenatu a jikin sa yanamata ya jiki sosai tabashi tausayi ada yayi tunanin blood transplants da akemata zaisaka cutar ta ragu kodayake ta ragu ciwo ne dole yataba mutum kuma ko a haka andace dan ba kowanne mai Blood cancer bane zai iya samun lafiya da ginuwar jiki irin Ameenatu ba, Hormonetherapy shima ya taimaka wajen kareta daga wasu abubuwan da duk mai cancer ke fuskan ta.
Gidan sa yai dasu, duk da sunso suyi masauki a Hotel amma ya nuna musu anzama daya yanzu dole suka bishi gdan sa. Abinci ne jere a dining kala kala sai kuma wanda Antonia taiwa Ameenatu special irin na masu cutar ta. sunci sun koshi sunso suyi abinda yakawosu amma Dr John yace su huta dan ko sunje ma baya nan yanzu. hakan akai kuma dama agajiye suke baccin su sukai yamma nayi kuma suka dan zaga. Ameenatu kam cikin school sukai nan kam tahadu da friends nata da lecturers sai wajen 10 nadare suka dawo. 7am a idanun su tayi saboda aman da Ameenatu ta tashi dashi wanda tunda suke da ita bata taba yin irin saba idanun ta duk sun kafe kwayoyin hallitar ta wasu duk sunyi blocked since ma bare yanzu, cikin tashin hankali Dr John yai kanta a yadda ya ganta yasan lokacin ta yayi dan duk wasu bad condition sun nuna cikin tausayawa yace Antonia pick my phone and call Dr AbdoulHakeem for me be fast, cikin sauri yai yadda Dadyn nata yace.....bugu daya biyu aka dauka, cikin tashin hankali Dr James yace hello Dr we need ur help wadda kace muzo yau by 12 t jikin tana yai worst kataimaka ka dubata zamuzo yanzu, cikin wayar mutumin yace Im sorry sir oga na bacci kuma ba'a tashin sa and koda yana nan baya saba ka'idar yadda yace...kataimaka zata iya rasa ranta .........sir is not my fault and umarni ne daga oga na shiyasa, kataimakan dan Allah zan rasa yarinya ta ita kadai garen.....masinjan zaikara magana daga daya bangaren aka bashi umarnin yace sukawota, cikin girmamawa ya amsa da toh, sir ku kawota amma kuyi sauri, cikin sauri suka ciccibi Ameenatu wadda itada matacciya babu maraba suka fice da ita zuwa ROYAL HOSPITAL LONDON.

#anatare kwarai da gaske. votse and comments
 

NIDA AMEENATU. {Completed}Where stories live. Discover now