14 NDA

3.1K 129 13
                                    

Hakeem gaba daya rasa inda yake yai, abu daya ya iya fada shine akai Ameenatu 9ja, can ne mahaifar ta. Tunda ya fadi haka baikara sanin ina kansa yake ba sai bayan sati biyu kuma a Lag yagan shi. Yana faduwar kafin a daukeshi ma akaga yana mana jini guda guda, wani saboon tashin hankalin kuma, amma cikin ikon allah aka gano ciwon zuciya ne yamasa kamun farat daya, kuma har suka taso bai farka ba, asati biyun.
Fadin tashin hankalin da fam din suka shiga bata baki ne, dan babu mai uhm bare uhm har aka share zaman makoki. Lokacin da Hakeem ya farka yakara gasgata Ameenatu ta barshi, hawaye ne ya sulalo masa ''from Allah we are, and to Him we shall return'' Mom it is true Ameenatu has passed away? cikin kulawa tadagamasa kai....I have lost my happiness, i lost my heart, i will be there if u are there, zan zauna a 9ja har mutuwa ta. Take heart Hakeem, may her soul rest in peace, ameen Mom...i miss Ameenatu, she has gone and leave me... we too we miss Her, and feel the pain of her lost, Mom she's nice and reserved, we all know. Sati biyu sukai bayan farfadowar sa suka juya gida, yana kuka sunayi, saiya tuna lokacin da za'a kaimasa ita, kamar haka yan uwa suka taru.
Rayuwa sabuwa dan Hakeem yazama wani miskili na masifa, baya ko magana daga shi sai yaran sa kullum cikin kuka yake na tunanin Ameenatu, baci basha yazama maraya na karfi, ganin halin dayake ciki yasa saida aka kara da addua da rubutu kafin yafara saukowa. Watan sa uku a lag ya tarkata zuwa UK kayan sa yahado kaf yai risining yadawo Lagos da zama dan kula da amanar da Ameenatu tabashi, sunsha kukan rabuwa shida Fam nasa da kowa, amma ya suka iya dole ce tasa zasu bar juna.
Mohd yaran wajen Mom yana gunta, tana kaunar sa sosai, uwa uba kuma su little Ameenatu suna ganin gata matuka, dan uban su baya aikin komai saina kula dasu. Ka'ida kullum ne saiyaje kabarin ta, zuwan safe daban na yamma daban, anso hanashi amma akaga za'a iya rasashi, dan antaba cewa ya hakura aranar kwanan asibiti sukai shiyasa aka zubamasa idanu.
Bayan wasu shekaru. Taj yai aure inda ya zauna kusa da Mom, Hanadi tanada kirki tana kula da Mom sosai Mohd kuwa kusan komai nasa yana gunta dandai shine ma yaki komawa gunta, sannu itama Allah ya sauke ta tasamu baby girl, sunan AMeenatu aka saka dan akwai shakuwa tsakanin Ameenatu da Taj. Ba karamar murna sukaji ba, Hakeem yafi kowa murna yaiwa dan uwan sa godiya ba kadan ba. Ya Musty ma matar sa ta haihu AMeenatu aka saka sun dauki son duniya sun doramata, Husnah kullm batada zance saina AMeenatu, Ya Musty ma haka. Kaf cikin family din idan kanason asoka ko amaka komai kake so to ka nuna kaunaga ga sunana Ameenatu,ko kanuna zafin rashin Ameenatu ko kace kullum inaiwa Momy Ameenatu addua, kaima yanzu zakaga kauna.
Little Hakeem da Little Ameenatu kulawa ba magana dan suntaso cikin gata da nuna kulawa, baban su shine cinsu, shansu, duk wata dawainiya da uwa takeyi yazama shine, Mama wataran har zubar masa da hawaye take ganin yadda ya sadaukar da rayuwar sa akan yarta. Asibitin ta yana nan kuma yakan shiga sosai tare da yaran sa. Ko da su Babban Yaya suka tuntube shi akan aiki kuka yasaka yace inada kudin da zankai ma shekara dubu basu kare ba, mezanwa aiki, kula da yaran AMeenatu shine aiki na...tundaga lokacin ba'a kuma masa maganar ba. Zancen aure kuwa duk randa akamasa to fa sai ankwana akan sa, saboda ciwon sa na zuciya tashi yake, tunda yarasa Ameenatu yarasa kwanciyar hankalin zuciya. Mohd yana zuwa 9ja suma suna zuwa dan susan juna da yan uwan sa. Shakuwa tsakanin su da Hakeem dan Aunty Zainabu ta Bahrain ba magana kaikace gari daya suke, yo abu na kudi duk karshen 3 months yakai musu ziyara shida yaran sa.
Yaukam Hakeem Abuja yai saboda kiran da president yaimasa, baisan akan koma mene ba amma yaji kiran ba alkahairi, lokacin dayaje ansan waye shi daga ina ya fito girmamashai akai kana akaimasa jagora har zuwa office nasa. Hakeem dama nakirakane akan 'yata Fannah tunda ta ganka tace atafau kaitake so, shine naga aigara asanar da kai, murmushi yai mai ciwo kana ya dubeshi yace nagode sosai da tayin ka, amma ni mijin mace daya ne, kuma namiji baya auren namiji, kamar yaya ya tambaya?, eh tun tashina bana ganin mace wata aba, saidana hadu da Ameenatu, tunda tabarni kuwa nakoma rayuwata ta baya, mace ta mutu sauran matan duk muna mata ne, kai hakuri yana fadamasa ya mike sai waje. A cikin jirgi kuka yake yana mesa kika tafi gashi kamar talla ake dani ma, saidayaji kansa na neman ciwo sannan yai shuru yacigaba da nemawa Ameenatu gafara gun ubangiji. Badan yanaso ba yarage tunanin Ameenatu, saidan tace bata yafemasa ba idan ya kuntata kansa, kuma idan ciwon zuciya ya kasheshi ai bai danka amanar yaran Ameenatu ba a hannun wanda yake burin damkawa, hakan na nufin yaci amanar AMeenatu shiyasa yake sausotowa kansa.
Shekarar su little 14 su Ya Omar da babban yaya suka tsindima harkar siyasa, sunso na shiga amma naki, saboda siyasa cinye lokaci ne nikuma lokaci na na yaran Ameenatu ne. Dangin Ameenatu mutanene masu kirki da karamci, Mama ta dauken matsayin Musty komai kuma tare muke dashi. Siyasa ta karbesu dan duk sunci kuma kowa na kaunar su, ahaka shima Baban Ameenatu yafito dan takarar majalisar dattaijai kuma yaci shima......
Mom tawa na kaunar yara na, Mohd da Ameenatu yar gidan Taj komai nasu tare dan waje daya suke, shike mata komai yadda yakamata, familyn mu kullum cikin farin ciki suke... amma kasan zuciyar kowa akwai wani miki da bazaitaba cike gurbin ba.
Gata da kulawa nabaku, na kaunace ku, ko makaranta da kukai a a US tare mukaje daku, aikina kuma wataran nakanje Royal ko BLK nadan duba wasu baran masu cancer kodan tunawa da masoyiyata. Gidan da muka zauna a Royal hospital anbarmin shi kyauta saboda kwazo na da kuma dama saboda ni aka gina shi. Kakan ku yazama governor saboda talakawan gari badan yanaso ba, Babban Yaya wato Ya Mohd yazama governor na kudi. Saboda haka kunji labari na na NIDA AMEENATU, inafatan zaku zauna lafiya da junan ku, zakuyi koyi da kyawawan halayyen Ameenatu kunna musu video din da akaiwa Ameenatu yai lokacin da zata mutu.....tunda yafara gani zuciyar sa tafara harbawa, a hankali yafarajin ciwo amma daurewa yai yacigaba da musu nasiha.
Kuka Ameenatu tasaka tana Dady kayafeni insha ALLAH zanzama kamar mama na, nadena kyamar talaka, ko gidan marayu ka kaini zanje, Yaya Hakeem kayafemin plx baran kara ba na tuba, calm down Ameenatu nayafeki kinji, bakimun komai ba, burina na rike amanar dana dauka da kyau. Amma Dady meyasa kakeson Sweden?, garin yaiwa Ameenatu dadi, Paris fah? shima Ameenatu nason garin baran Eifell tower, da seine river yanayin garin yanasakawa naga murmushi a fuskar Ameenatu, Dady kanada cancer?, bani da ita, amma meyasa kakecin abincin su muma haka?, saboda shine abincin Ameenatu, Dady kace kome mukeso zakamana amma kaki kaimu Dubai?, ba laifi na bane Ameenatu bata tabamin zancen tanason taje ba duk da kyan garin da ake fada, Dady madara fah?Ameenatu batashan ta shiyasa bazan koyawa yaran Ameenatu shanta ba, ohh Dady kaida Ameenatu sai Allah kenan?. NIDA AMEENATU sai Allah kam, Allah yahadaku a aljannah akarasa soyayyar nan da sauri suka juya ganin family nasu sukai duka harda Mom dasu Aunty Zainab, hanadi, Taj gasu nan dai, Mama dasu Ya Omar, harda Ameenatu {Antonia}aminiyar Ameenatu tabiyosu dan ganin yaran Ameenatu, Baban ta yarasu shima....bayan mutuwar sa cikin ikon Allah da girman sa ta karbi musulunci,...ta kuma amsa sunan Ameenatu saboda kaunar datake tsakanin su, wani dan uwan Baban Hakeem ta aura.
Murna sukai gaba daya anan aka sha kuka aka gama, Hakeem ne yace Dady kasata tai waya asaki wannan guy din, cikin sauri tadauka tace asakeshi, Dady nima ina zan nemo mata mai hali irin Ameenatun ko wace zata soni haka? a hankali Ameenatu ta taso yar gidan Ya Musty da Husnah tazo gaban Hakeem karami tace nice zan zama zan kula dakai daidai iyawata, ina kaunar ka kasoni kaji Hakeem?, idanu ya zaro kana yabita da kallo wanda nakasa tantance kona mene, cikin murya mai laushi yace acceptence daga yanzu muma NIDA AMEENATU.
Mohd ne shima ya tsuguna gun Dadyn sa cikin kwantar da murya yace Dady kayi sa'ar mata nima inason kamin addu'a Allah yaban mata wadda zatasoni dangin ta su soni, Allah zaibaka Mohd dan idan nagan ka inatunawa da Ameenatu sosai, halinku iri daya ne da ita, duk da kai bakai kama da ita ba sosai amma halin ku, hakuri, kawaici kahada komai nata, kuma na tabbata da Ameenatu na raye zata soka sosai kodan ganin fuskata ataka fuskar, Dady amma ai dukkan mu muna kama, haka ne nikaina ina hangar kamata da Ameenatu lokuta da dama....Dady kaunar kuce tazamana fuskar ku ta koma haka. Mohd zaka samu mata tagari as far as if u don't change kodan halin ka nagari. Yana rufe baki Ameenatu yar gidan Hanadi da Taj ta matso hannun sa takama cikin husky voice tace Yaya Mohd gida daya muka tashi, kaine kaban tarbiyya kaida Mom, kaine malami na kuma aboki kuma yaya, idan har tarbiyyar da kamin ta cancanta danazama matar ka nima najima ina kaunar ka.....cikin murna yace acceptence fav sis.....wani abune ya doki zuciyar Dadyn nasu na tuno fav sis dayai da lokacin dayakirata da haka, nima daga yau ko kwatance zanyi zance NIDA AMEENATU.
Daddy ni babu mai sona kenan, bola za'a kaini nayi kwantai duk kyan danake dashi?, wayacemiki kinyi kwantai?, fav sweety, baby luv sis like no other, my angle, other half, hayatee, ruhee, damee, lahmee, jasadee gani gaban ki idan har ni Hakeem da ga Auntyn ki Zainabu na miki zaki iya aure na zan aureki, zan kula dake nabaki kulawa daidai iyawata, zan zama bawa akanki, zan kyautata miki nai hakuri dake, kodayake bara nadena fada amma ni ina kaunar Ameenatu inason tazama tawa kodan nima nace NIDA AMEENATU.
Kuka Dady yasaka cikin kuka yace tabbas zanso ganin wannan ranar da zan aurar da amanar Ameenatu, pics nata ya kwaso yasa a tsakiya yace kowa yana nan bazaiyuyu ace babu Ameenatu ba kema zauna cikin mu, dukda ni kece, kema nice NIDA AMEENATU mutawace tamana yankan kauna....a'a kowa shida AMEENATU nima NIDA AMEENATU baban Marigayya Ameenatu yafada tunda shima matar sa sunan ta AMeenatu.
I LOVE U AMEENATU, I vow to live for u... KO YAU NA MUTU BANDA KAICO TUNDA NA DAMKA AMANARKI DA KIKA BAN TA YARAN KI AHANNUN MASU AMANA.....Yana fada wani tari ya sarkeshi nan da nan sai aman jini, hotunan ta na kirjin sa yana kara rikeshi, hannun sa na cikin na Mom nasa, kuka suka fara cikin murya mai laushi yace kubarni naje gun Ameenatu, tunda na cikamata alkawarin ta meyai saura?, idan kunyi aure da wa zan zauna?, Mom ina kaunar ki Taj ga amanar Mom nan, Ameenatu ina sonki, kiyi biyayyar aure irin na mai sunan ki, Mama hakika ke uwace, Ya Musty na gode da karamci, ciwo na bana tashi bane kamar yadda ciwon Ameenatu bai barta ta tashi ba....NIDA AMEENATU yana fadin haka yafara kalmar shahada ana rai yai halin sa dama yace ciwon rashin Ameenatu ne zai kaishi lahira, kuma gashi ya mutu cikin dangin sa akuma cikin dakin Ameenatu Villa.

Masha Allah nan nakawo karshen wannan labarin nawa mai suna NIDA AMEENATU, fatan kuskuren dai za'amun afuwa, dan Adam ajizi ne......Allah yadamu da masoya nagari.
hakika ni Zainab bantaba littafin danaso ba, na kaunace shi, na rubutashi hawaye na jikani, yakaryamin da zuciya irin NIDA AMEENATU. Kutayani sharing din book din NIDA AMEENATU kodan masoyana su karu da wani abun.

Mutuwa dole ce, kuma zaka tafi alokacin da baka shirya ba, zaka tafi koda ka shirya, mutuwa ce kadai mai rusa gidaje, mai raya kaburbura, mai raba masoya, mai raba da da uwa, banda mutuwa waye zai dauke da acikin mahaifiya?, banda mutuwa waye zai dauke mata a jikin mijin ta, Allah kamana maikyau...love u all.

NIDA AMEENATU. {Completed}Where stories live. Discover now