2 NIDA AMEENATU

3.1K 181 5
                                    

Lagos shine tushen Ameenatu, AMEENATU itace d'iya ta hud'u wajen iyayen ta, wato Alhaji Abbas da mahaiifiyar ta Hajiya Ameenatu, su hudu ne wajen iyayen su, uncle Mohd, uncle Omar, uncle Mustapha sai kuma ita. Mahaifin su attajiri ne mai dukiya ta gaske, harkar cange yake yi kowacce kasa, yanada gidajen mai kuma sosai, kowanne dansa ba'anan yake karatu ba, Ya Mohd  yai karatun sa a Cambridge university, inda ya karanci Account, Ya Omar kuma Bristol university yatafi, sai Mustapha wanda a Istanbul yayi nasa a Bezmialem vakif universitese.Alhaji Abbas  Mutum ne mai kaunar talaka, yanada saukin kai, kullum burin sa yabayar, ko yaga mai bukata yabashi, wannan halin nasa shiyasa kowa ke son shi da kaunar sa, ba garin sa kadai ba hatta garuruwan da yake zuwa ko yakeda gidan mai acan suma kansu sun sanshi wajen tausayi da taimako, Tsakanin Mustapha da Ameenatu shekara kusan tara yabata shiyasa kusan ita daya ta taso dan lokacin duk suna makaranta, shi Mohd ya juya Malaysia yin Phd din sa akan account din dai, Unguwar victorian Island unguwa ce ko nace yanki ne a garin na Lagos da baraka taba samun mai kudi a cikin sa ba, sai hamshakin mai kudi ko Attajiri, unguwa ce ta Senates, Ministors da manyan kusosahi na Nigeria, yawan cin yankin ruwa ne dan ko wani street din zakaje ba lallai mota na wucewa ba sai kwale kwale amma fa na gayu, akwai Parks sosai, da malls a ciki, uwa uba makarantu da Asibitoci masu kyau. unguwar Adeola Adeku street nan suke zaune.
    Asalin su duk yan kano ne, kuma akai akai suna zuwa saboda dangi duk suna can. sana'a ita takawoshi Lagos tun samartaka har kawo yanzu.
Duk inda akace kafadi mai kyau to kuwa zaka saka Ameenatu a sahun farko, ko jinsin larabawa kafin kasamo mace mai kyanta saika tona, yanda kasan yar kasar ethopia ko yar Brazil, Haka duk inda ake neman yar gata kasamu Ameenatu kawai ka rufe baki, yarinya ce mai addini, hakuri, tausayi, kunya, kyauta, duk wani hali na iyayen ta kaf Allah ya hadamata shi, tai karatun ta na nursery a WHITE LIGHT MONTESSORS dake Akin Ogunlewa street, ita makarantar daga shekara shida suke yaye dalibi, tana gamata aka maidata  Walter carrington crescent inda anan tagama primary nata, kafin ta tsallaka  NATHER LAND INTANATIONAL SCHOOL, duk a yankin cikin Victoria Island din suke shiyasa suke karatu sosai, makarantu ne na sai dan wane da wane. primary, tanada tsantsar tarbiyya, wadda hakan yasiyamata kauna gun kowa.
Ameenatu tun tana SS2 take fama da zazzabi, yawan kasala da kuma rashin appatite, gata bata sha'awar abinci irin na sauran yara,  wani lokacin ma numfashi nema yake yagagare ta, bata taba fada ba a gida, kuma Maman ta kodata tambaye ta meyake ramar da ita nan tace ba komai, Abban ta kam kin yarda yai nan yakaita asibitin su na Lagoon hospital, nan likita ya danyi checking din ta, ya nuna tanadalimonia, ya bata magani, haka dai  tacigaba da rayuwar ta, kuma jikin ta yai sauki sosai saidai rashin apatites da su ciwon mara wanda aka ta'allaka shi da cewa na al'ada ne, amma ana kulla da ita sosai.
Yayun ta suna alfahari da ita duk wannan gatan da take dashi hakan bai sauya tarbiyyar ta ba ko ya sauya mata hali, tanada  kawaye ko nace kawaye na sonta, shiyasa gidan su kullum baya rabo da jama'ar ta, Redy baby wasu ke cemata saboda ko batasaka kaya red ba dole kasamu red cikin undeerwear nata data sanya, duk weekends saitaje WOOLWOETH PLAZA dan siyan kayan da zatayi ado, yar gayu ce sosai, shan coffee kam ka'ida ne dan daga LAPOINTE ake kamata sun iya sosai, batada surutu sam, idan kaga maganar ta to fa sai gun Yayun ta, Azumi na alhamis da juma'a da sallahr walaha da nafilfilu basa wuceta tun tana shekara goma sha biyar.
Zaune take a cikin laboratory na school din su tana hada sample na wasu chemical sai jitayi bayan ta ya rike iska kuma tana neman gagarar ta shaka, da sauri tafara ta'awizi tana janyo numfashin da karfi, amma inaa dole dai saida takai kasa, ba kowa a gun bare akamata taimakon agaji, kusan mintuna ashirin ta kwashe a haka kafin Feedoh da  Husnah kawayen ta  suka shigo suna Ameenatu anjiki shuru where are u uwar son karatu dole dai ace u are the best, cikin dariya Husnah tace ai ko kinki sai anfada tunda she's serious than u, abeg move before na fasa miki kai wallahi Feedoh tafada da haushi, sorry Deedoh...bakin tane ya makale ganin Ameenatu ayashe a kasa, da gudu ta tafi Ameenatu lafiya jijjigata suka fara yi amma inaa ko numfashi batayi, dole Husnah taje tai report wa malaman su, cikin sauri akazo aka dauketa akai clinic din makaran tar, duk yadda suke da good and intelligent doctors a school din, amma wannan karan aikin nasu yazama na banza sunyu iya yin su amma takasa farfadowa, Husnah do u know family hopital na su Ameenatu wani malami ya fada?, cikin sauri tace i think REDDINGTON HOSPITAL since is the best hospital in this area, lets go, cikin kuka Husna taiwa yayan ta waya akan Ameenatu ba lafiya, suma iyayen ta cikin  tashin hankali sukai asibitin wanda aranar ne mafarin komai, yana fada yasaka handkachief wanda yake tashin kamshi kuma red ne da sunan Ameenatu a jiki yashare hawayen sa, cigaba yai da magana.
Sosai akai bincike akan AMeenatu aga meyake damun ta, shi kansa doctor din saidaya girgiza ganin abinda ke damun ta, BLOOD CANCER. kasa gayawa iyayen yai amma da suka matsa ido ya rufe yagayamusu yarsu na fama da cutar Cancer wadda akalla takusan shekara biyu a jikin ta, suma Maman ta tai kowa na gun kam  kuka yafara suna mamakin ta yaya cancer ta shiga Ameenatu, kenan du kariyar da suke bata  saida cuta ta shigeta, a wannan ranar iyalan gidan Alhaji Abbas da masu kaunar su basuyi kwanan dadi ba.
Kwanan ta uku a wannan halin tasamu sauki, kamar bata kwanta ciwo ba, lokacin da taji abinda ke damun ta, mumushi tai tace tawa qaddarar kenan, ina fatan Allah zaiban ikon cinyeta, tana fada ta rufe idanun ta. CANCER cutace mummuna datake zama cikin cells din mutum, tana farawa ne da idan wata kwayar hallitar aikin ta yakare, kafin wata tazo ta maye gurbin nan cancer ke samun damar shiga, ko kuma jinin dan adam na wani barin baya gudana yadda ake so nan ma cancer kansamu damar shiga, cell kuma shine jigo na rayuwa, idan yafara gazawa to kuwa rayuwar ka itama zata fara gazawa, wata kuma kan shiga mutum ne ta hanyar wani tsiro dake jikin ka, idanbaka nemi magani ba, to kuwa cancer  maraba da zuwa gun da yawan gudun jinia jikin mutum batare da dalili ba. Yawancin cancer nazama a hunhu, breast, brain, Injury, mafi sauki idan kanada hali itace ta blood wadda za'a iya yimaka juyen jini. kwarai akabata kulawa ta musamman, aka dorata kuma akan magani irin su, MOEPHINE, CODEIN PENTAZOCINE dan kariya gareta.
  A stage na biyu take shiyasa taji jiki sosai, kuma daga lokacin aka canja mata abinci zuwa na masu cancer, beans, carrot, cinnamon dan su kusan sunfi wani maganin aiki, sosai suke karya alkadarin cancer, salad, fruits, naman saniya, bread,  duk shi aka kafamata dokar cin su, atakaice tazama vegetarian dai tunda haka ita kaddarar ta take. Anso ayi mata HORMONETHERAPY Ya Omar yace a'a magani ma zai wadatar. bayason kanwar tasa ta wahala ne shiyasa yace sam bara'amata ba, amma wani bangaren hormonetherapy yana sawa cutar tai kasa.
Sati guda tayi kafin ta koma school, tundaga lokain rayuwar ta ya sauya, yau da lafiya gobe babu, amma hakan take kwarara jikin ta take ayyukan da suka dace, Yayun ta kulawa sosai suke bata, wataran ma tare zasu kwana suna kasa tana gado dan duk su debemata kewa kuma kada ta zanna haka, a haka da jiki jikin Allah yasa ta kare school din ta.
  Husnah ta zamar mata yar uwa dan kullum takan kamata ziyara da kuma duba jikin ta, result nasu ya fito kuma yai kyau sosai, nan tasaka rigima itafa Medicine zata karanta, kuma ba a LagUni ba aOxford London University baban yaso ya lallasheta amma ta kafe, dole akafara mata processing school a Uk din.Dake Ya Mohd yasan wasu da yawa a can ba'a dauki lokaci ba akaimata komai, Ansamama ta cikin nasara,  ranar da zata tafi kaf yan uwan tane suka rakata, a jirgi tana like da Maman ta har suka sauka duk da saidayai tranzit a wata kasa, Koda suka sauka hutawa kawai sukai kafin baban yanemi asibiti nagari na FREEMAN HOSPITAL, sosai ya yaba da asibitin amma kuma basuyi wani karfi a can cancer ba, dole yaje yanemi wani a BEDFORD TRUST can  yaje yai reporting akan cutar ta, yasamu doctor nagari wanda ya dauki alkawarin dubata a kullum kuma yaranyar sa na university din nan yace zai hadasu. Bakaramin jin dadi sukai ba, tare dashi aka gamamata komai, kwanan su uku  sunyi yawo sosai, sune BRENCH PARKS, GREENWHITCH MARKET, BROADWAY MRK, VICTORIA AND ALBERT MESSEUM SUN ZAGA KAM BA LAIFI kafin suka juyo bayan sunsha kukan rabuwa da tausayin tilon kanwar su.
Sannu a hankali Ameenatu tafara karatun ta a makaran tar, kuma sosai take ganewa, tare da yarinyar Dr John suke, mai suna Antonia, jikin ta sam baya tashi saboda ta dage da shan magani kuma tana bin duk wata doka da aka kafamata. Islamiyya ta nema can mai kyau wadda asabar da lahadi tun safe ake zuwa sai yamma, nan ta shiga tafara daukan darasi wanda yawanciin malaman daga Madina, Rasha, Ajman, Bahrain, Yeman suke. Kawancen ta da Antonia ya mika babu wani nuna banbancin addini, kowa  nasa yakeyi ba ha'inci a zaman su. Ada zaman hostel take amma saboda yadda da juna baban ta ya bukaci tadawo inda suke da zama kodan lafiyar ta a BIG HEN.. Iyayen ta sunji dadin haka, duk bayan wata daya wani yake zuwa yaganta daga gidan su, hakan yana kara sata cikin jin dadi ganin hatta malamai ma sun kula da ita da lafiyar ta.
Duk hutun ta a gida takeyi, inda wani hutun su tafi Saudiyya wani kuma suyi a Kano inda yan uwa suke. hakan nema yafaru wannan hutun a kano zasuyi, Baba amma a gidan Granny ni zan zauna gaskiya nai missing fadan ta fah, to Ameenatu yadda kike so haka za'ayi, kaji Baba wani yadda nake so, yadda kake so dai, Allah yamiki albarka kinji?, Ameen, Allah kuma yabaki lafiya ya kareki duniya da lahira, Ameen tafada amma kasan zuciyar ta tausayi ne fal na iyayen ta yadda suka damu da damuwar ta.

COMMENTS, VOTES....AND SHARE...LOVE U ALL, #ANATARE KWARAI DA GASKE.

NIDA AMEENATU. {Completed}Où les histoires vivent. Découvrez maintenant