Chapter 004

1.9K 113 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


✍by Haleematu💕meemartjj💕





*I dedicated this page to u sweet sister(fa'izartjj)ina godiya da irin shawaran da kike bani, Allah ya saka da alkhairi.*
*Bazan manta da kuba members na groups ,jinjina ta a gare ku,your special advice is always welcome,tnx alot nd luv all.💋*












*page 004*

――――👀sune abin dana zuba a gun da naji an kira da backyard din gidan domin ya koma wani irin hadadan open place event duk inda nake tunanin abin ya wuce nan,yaji 🎈decoretion🎈ta ko ina sai dai kujrerun da aka shirya basu da yawa daga baya baya sai can gaba gaba ne aka ije wasu glass standard tables na musamman,gefe can left side mc🎤ne da mutanan sa🎧,sai can right side din,masu saving🍽,tsakiya kuma inda aka shirya gun unban gayya,dan kofa ne kawai a tsaye saman wasu dan steps ,sai aka mishi decoretion da wasu irin flowers banda spakling ba abun da suke yie,sai fili da aka bari a tsakiyar field din,kai gun yai matukar haduwa,baki kawai na saki ina kallo,don mutum ya shigo gun zai manta a cikin gida yake,a haka muka sami guri muka zauna,tare da mamakin irin dukiyar da aka kashe,sameera ce ta kalle ummi tana fadin,ummi lallai an kashe kudi a gunan,zarah tace,ke dai bari,waje kaman ba a naija muke ba,ummi tai far da ido tana fadin,kai ni duk ba wannan ba,shin ina wajan da uban taron zai zauna,zarah ta kwashe dariya tana fadin,kai ummi sai kace bakije demo ba,irin wajen taron nan ba'a fiye zama ba a tsaye ake yie har shima tasyuwa zai yi har a gama,kujerun ma an sane saboda irin mu masu saurin gajiya da tsayuwa,gaba daya muka kwashe da dariya,sameera na fadin,ko ina dai aka zo sai anyi.....,da sauri ummi ta kaste ta da fadin,kai kumu natsufa na lura an fara shigowa kar a raina mana class,nan muka koma muka natsu muna kallon shigowar kowa da kowa har sanda kakarsu,Haj.mairo(maman dad dinsu)ta shigo da yen rakiyarta tsohuwa wanda ta jiku da hutu idonta sanye da wsni siririn glass alama na kara ma ido karfi ne,fara sol da ita,ta zauna a inda aka tana zan mata na musamman,a haka dai jama'a suka dunga shigowa,police da soldiers dama ba'a magana sai karan🥁na police ke tashi,banda 🍸🥃kala🥂kala🍷da waiters ke yawo dashi mutane da dama a tsaye suke,jama'ane sosai a gurin don haka ya rage shigowar ogan ake jira,kowa dai ido ya yasa a hanyar shigowa.
Aunty mariya ne suka shigo tare da mijinta da last born dinta fadeela,bayan mc ya sanar da shigowan nasu,suna cikin shiga ta alfarma,tana sanye cikin wani lace mai suna lace golden da mayafin sa sai nadin daurin da akai mata tasha gold,shima sanye yake cikin wani shadda golden sai kyalli take yer ciki da malun malun,yana rike da hannun fadeela wanda akai mata adon cikin gown na readmade,suka wuce gu na musamman suma suka tsaya ana basu👏🏻,sanda suka shiga kuma gaisawa da wasu bakin,nan kuma mc ya shiga sanar da shigowan Abdulmajeed,don haka gun yai shiru sai karan bullet dake tashi a speakers,tunkan ya shigo naji wani irin faduwar gaba zuciyana taci gaba da bugawa na rintse ido tare da budesu fes a kansa ina karanta duk addu'an da tazo bakina.
Ya salam,tafiya yake cikin natsuwa sanye cikin wasu black din suit sai fari ta ciki,duk yanda na ganshi a hoto ya wuce nan,abu daya ne kuma ya dada ma kyakyawan fukarsa kyau,shine murmushin daya ke dauke dashi mai cike da annuri,so gent dashi, bayansa kuwa wasu escort ne har su hudu,ya kariso ida aka tana zan masa kowa na bashi👏🏻ya tsaya yana daga ma mutane hannu tare da mika ma wasu su gaisa,na sani da dama enmatan dake wajan mutuwar tsaye suka yie ,kai ba mata ba har mazan ma nasan ya burgesu kuma za suyi sha'awar a'ikin irin na en sanda,ni dai meenal dama bani da tacewa daya wuce na zuba idanu inga irn abin da zai wakana.
Haka aka shiga gabatar da program din da aka shirya bayan an bude taron da addu'a enuwa da abokan arziki sai zuwa suke suna taya shi murna hoto kake jie ta ko ina,anci ansha kuma an walwala,maryam tare da wasu enmatan ana tsakiya ana cashewa,enmata sai rawan kai suke kafun kuma wasu su koma taitayisu da zuwan,Basmatie wace bata da banbanci da jinin larabawa yer minister ce ,yarinyan abokin dad dinsu ,tun daga india taxo inda take karantan medicine,don taya friend din nata murna,ba'a maganan irin suturar dake jikinta don ya tona asirin ko ita wacece,daka ganta kaga kudi,kusa dashi ta tsaya,zuwanta kuma ya kara wani annurin afuskarsa,na rika kallon su cikin burgewa yayin da wasu enmatan suke cike da jin haushi,haka dai taro ya soma watsewa lokacin da aka fara hotuna, Amal da khairat sune en gaba ,,koda harda mummy maa naga sun dauka,zarah ma da ummi sunje nidai da sameera wanda ke waya da saurayi muna zaune inda muke,ina rike da Adil wanda yai bacci,haka aka rika watsi da kudi kaman ba'a so, kafun sameera ta kare waya ta mike tana fadin,nima bari naje ayi dani,ta kalleni tace,ke meenal kinanan a nan ko?,kai kurum na daga mata alamar eh,ta tafi ta barni zaune nan ina tunanin rayuwa.
Tsaye nake dai dai entrance din wajan goye da Adil ina jiran mummy mu tafi gida gashi an fara kiraye kirayen salla magrib,lokacinne suke ta rabon kayan surveneir,maryam tazo wucewa dashi a hannunta da wasu friends dinta suma dashi kaman zasu bigeni da sauri naja gefe na tsaya,can sai ga ummi dashi a hannun da sauri na karisa gunta ina fadin,ummi kinga su mummy da Amal,tace,a'a nima umman mu nake nema zan amshi key a wajanta insa ma mameen su samira wannan a mota,na mika hannu ina fadin mu gani,na amsa babban jaka da calendar wanda yake dauke da hotan yaya majeed a jiki tare da wasu sauran tarkace dai a ciki,na tsura ma hoton ido ina kallon yanda yai kyau cikin kayan en sanda,ummi tace,yauwa gama mameen can bari na amso key din kafun ki gama kallon,ta wuce ni kuma na cigaba da kallo harda wata yer murmushi na ba tare da nasan na tsaya akan hanya ba.
"excuse me"shine kalman dana jie a tsakar kaina wanda yai sanadiyar saukar mun da wani karfaffan faduwar gaba,na dago idanu wana nan ko mukai 4eyes dashi,wani rudewa dana yie bansan sanda na saki jakan dake hannu na ba,ya fadi kasa kayan dake ciki suka watse,sai kuma na duka da sauri ina kwashe kayan duk na rude,bansan na tsare mishi hanyar wucewa bane,yatsunsa ya zuba saman fuskansa tare da dan runtse ido ya budesu yana fadin,oh!!my god,u are geting on my way,kin tsare hanyar da zan wuce fa,da sauri na mike ina fadin, ohhh,tare da matsawa can gefe,ya wuce da sauri shida abokansa su biyu sai cikin securities din da suke take mai baya su biyu,ya juyo yana ma daya daga cikin su magana,myke pls help her pick up her things,daga haka suka wuce sai sauri yake,nikam na bishi da ido kaman ince yaya majeed dawo,sai da har security din ya gama kwashe mun kayan yana miko mun sannan na dawo hayyacina,na amsa tare da wucewa inda naga ummi tayi.
Ina tsaye gun motarmu su Amal suka kariso mummy na fadin sai mun jira faauntyn tace zata a'iko da wasu kaya, aunty salma ta amshi Adil, yayin da kausar ita da khairat suka kariso gun da kaya niki niki duk na surveneir ne,ta mika masu mummy,tare da ba Amal nata sai lokacin ta ganni tana fadin,ah meenal ashe kinzo,nai murmushi muna gaiswa,tace ,ehyah,bansan kinzi ba dana taho miki da naki surveneir ,but ba matsala bari naxo,mummy ne tai saurin fadin,a'a kausar da kin bashshi don yanzu zamu tafi,tana dan tafiya tace,pls aunty sa'adatu yanzu zan kawo ma...sai kuma ta kalli khairat dake rike da wasu tana fadin ,yauwa sis.ban wannan in bata,yamutsa fuska tayi tare da cewa,no wannan nasu billy ne,suma they are going now,tsaki kausar ta saki tare da juyawa cikin sauri take fadin,pls just two minute,itama ta juya tabi bayanta, wani wawan tsaki Amal ta saki tana bangajeni tace,dalla matsa banza zaki bata ma mutane lokaci,mummy ta kara da fadin,gashi dare yayiba,da sauri na koma ta dayan bangaren inda ke facing main gate din gidan mai hade da masallaci na tsaya tare da dukad da kaina,ina jin Amal na fadin,ko uban mai ya hanata shiga cikin mota oho,shiru kawai nayi ina kokarin dane hawaye tare da tunanin a ko ina nake dai sai an maishe nie bora ,wani faduwan gaba najie wanda nasan na daban ne a en kwanakin nan yasa nie dago kaina da sauri,tabbas kuwa shi na gani yana tafiya cikin sauri dag barayin da ake alola zai shiga cikin masallaci ,ya cire suite din rungume a dayan hannun sai faran na saman, yana tafe yana nade longslip din hannun rigan,har ya shige masallacinsalla, Allahu Akbar ,shine abin dana fada cikin zuciya don najie ya dada ban sha'awa sosai dama saurin da yake tayi kenan yaje yai salla ,Allah sarki yaya majeed ya dada burgeni sosai ,mummy ne ta kwalamun kira sanda naxo kausar ta bani nawa surveneir muka kama hanyar gida cikin mota wanda driver keja, ina gaba mummy da Amal suna baya,don aunty salma ta wuce itama gida daga nan.
Yau ya rage saura kwana uku muyi resuming school ,ina ta shiri tare da harhada kayana,na nufi can garden side ina tsefe kitson dake kaina,,zaune nake kan swing chair mai guda uku na kammala tsifan tare da oiling gashin ina tajewa,motsi na fara ji ta bayan inda nake zaune barayin da wasu manya manya cage room suke,sanina dai babu komai a ciki don haka na mike a tsorace ina lekawa har gurin door din,ga mamaki na bavu kowa amma sai kaji a ciki,da barayin turkey daban, ansa musu abinci ga ruwa sai sha suke,ina cikin mamakin na wanene don na san mummy bata kiwo,Amal kuma bata garinma,basu da yawa sosai bare nace na dad ne,,,sai jin wani razanan nan kara naji a bayana,a tsorace na jiyo,ya kwashe mun da dariya,yana nunani 👈,wani takaici yasa ni daukan wani sanda dake gun don na tsorata sosai tare da kaimai duka, ya kauce ya zuba da gudu,nima nace muje yie,haka mukai ta zagaye field din garden kafun na gaji na zauna ina mishi tsiya shima dayan kujeran dake facing dina ya zauna yana fadin,sorry sweet sis.dina na tuba bazan karaba,murmushi nayi ina fadin,kama kara zan hada ka da dad ne,tuni ya sanja fuska tare da daurewa yace,ance motar Amal gobe zaizo,nace,waya fada ma?,yai dariya yana fadin meenal kennan waya ce miki abun duniya na boyuwa,kinsan abin da dad yake baya kyautawa,motar7million yasai ma Amal ,amma nie just a common bike nai mai magana yace ba yanzu ba da saura na,ita Amal aure tayi da aka sai mata motan,nai murmushi ina fadin,Abdul kasan yanzu bata lokacine mutum ya rika hada kanshi da Amal,cos ita special ne a gun dad,tsaki yayi yana fadin,ba wani nan dame Amal din ta fimu kisan in kyaune mun shafeta naisa ba kusa ba in kuma tarbiyan。。。da sauri na katseshi da fadin,tom ya isa haka kai dai kayi kokarin naiman na kanka,in kana dashi ka huta takaici,na numfasa ina cigaba da fadin,dama inka kammala secondary school dinka ka wuce police academy kaman yaya majeed, kaga matsayin ya dace dashi,yace,cabdi wa kike tunanin zai kashe mun kudin da aka kashe ma yaya majeed,ance miki wasane,nace ,amma kasan dad yana biyan mana school fees koh?,yace,eh nasan wannan, but meenal ki duba wasu abin duk mummy keyi banda school fees me yake mana,na katse hiran da fadin,Abdul yanzu baza kayi police academy dinba ,ko kai yaya majeed bai burge kaba,yai murmushi yana fadin, lallai meena na lura yaya majeed ya yankeki da matsayin nan,nikam police baya ra'ayina ,ya mike yana fadin,kinga ma nie yanzu poultry nasa ma gaba,na zaro ido ina fadin,lah Abdul naka ne dama chickens da turkeys din dana gani ?, yace,eh last week ma na sasu dana kwashe wasu,nace ,lallai bro. kayi kokari fa,amma ina kasa mu kudin da kake business din dashi,yana dariya ya wuce yana fadin,Allah ya bani,na bishi da kallo ina ganin yanda Abdul yake kokarin yin sana'a don ya dogara da kanshi,nima na soma tunanin sana'an da zanyi in huta da shan zagi da hantara a duk lokacin dana tambaya wani abun.
shagargarin ranan aka kawo motar Amal murna kaman ya kasheta,ranan dad ya dawo,motar kirar pasad mai kyau da tsada,mummy ta dakko tab dinta dad ya rika musu hotuna a jikin motar,nidai ina daga bakin window ina kallosu.ta shigo daki tana kada key din mota tare da fadawa gado,wayarta ta jawo tana sanar ma friensds dinta tare da shaida musu dashi zata dawo school,ta kammala wayan,na kalleta ina fadin,ya Amal congrat,Allah nuna mana namu haka,murmushi tayi kafun tace,tnx ,amma kafun nakun yazo tym din kun fara a'iki, ta mike ta barmun dakin ina mamakin kalamanta.
Sosai akayi case da Abdul akan motar dan masifa kawai yake har da kukanshi ,nidai sai tsoro nake dad yai mishi wani abun ashe ma bayanan sun futa tare da Amal,mummy ne tai mishi zaga zaga kaman ta dukeshi sannan ta hadamu duka ta zage tana mana fada da in mun isa mu canza Amal daga yanda Allah ya nufa zata jie dadi,wato daddys favourite,kuma ta riga da ta mana zarrah in zamu daina hada kanmu da ita mu daina wahalar da kanmu,tai zafi sosai don haka munsha fada,Abdul ma yasha kuka don yana ganin anki sai mashi common bike ita an sai mata mota ,nidai sai rarrashin sa nake tare da bashi baki.
Haka rayuwa dama yake, ko a cikin gidanku kake sai kayi hakuri,Abdul yasa ma kanshi burin cika burinsa na siyan mashin,nayi rarrashin amma ya kafe,dole na kyaleshi na tatara yen kayana na koma makaranta ko dan pocket money din ban ansa ba ,don banga fuska ba ,mummy cike take damu ,na tattara na koma school, gashi this time za muyi zaman extension.



so ko wahalah?
*2018*
comment&share

✍🏻by meemartjj💕

thanks💕

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now