Chapter 12

1.7K 103 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

*Baxan manta daku ba*
Hauwa'u Amad Amir
zainab Aliyu sambo
zakiyya muhammad yola
salaha Abubakar yaro
zainab Abdullahi Danbaba.
Asma'u M Tukur
*kuna raina*

vote me on wattpad
*Maamee Ja'afar*

*page 11~12*

――――An daura auren su uncle idris, inda aka fara da nashi a matsayin babba kafun a wuce na uncle kabir, bayan an kammala daurin aure kuma aka wuce tamfatse tsen hall din da manyan yayyin suka kama don reception, gaba daya aka hada, don haka gun ya cika sosai, su uncle ibrahim da uncle lamido suna wuri na musamman inda suke amsan bakin su.

Yaya sagir ne da yaya baffajo suka shigo haraban wajen suna packing din mota dai dai sanda suka hangi yaya majeed yana packing din nasa motan don haka tare suka karisa shiga ciki, angwayen sun sha kyau sai kyalli suke, suka gama musu ba'a duk da uncles ne amman an taso tare kaman friends, sannan suka wuce inda iyayen nasu suke zaune na musamman.

sun gaisa da iyayan nasu a ciki harda mahaifin yaya majeed wato alh.Alkasim,uncle lamido yace su zauna yana fadin, ya kamata fa kuma kuxo kuyi wannan auren naga duk kun fini tsawo haka, aka sa dariya, uncle alkasim yana fadin, gaskiyan ka director nima tunanin dana keyi kenan ankama a'ikin yie meya rage?, yaya majeed yai saurin fadin, no dad da sauran mu,we are not yet ready, uncle lamido yace,come on kaji commishner da wani magana naso na hanafa wanda zai baka matsayi nan yaba kashi haka ba aure, dariya aka kuma yi yaya sagir na fadin, ah uncle lamido auran fa ba easy bane sai an shirya, yace, karku damu zamu aurad daku ne, uncle ibrahim dake gefe daya yana murmushi yace, ina a'i kowa sai yaji abin da ake ji kuma bude bakin aljihun ku, yaya baffajo yace, amma Abba ban dani ko?, yace, harda kai dama baka fara a'iki bane but tunda ka fara magana ta kare,,,,,

uncle alkasim ya gyara zama da kyau so serious yake fadin, to ku kunji da gaske ba wasa ba kowa ya shirya, don girma an gama yinshi ko?uncle lamido ya amshe da fadin, tabbas kwarai da gaske, aure kaman kunyi don yanxu ne right time dinku, don haka kowa ya fotu da mata,aure za kuyi, yaya baffajo ya amsa da fadin, nidai banda matsala, yaya sagir yace, to nidai ina dashi gaskiya don ban shirya ba,,,,

uncle lamido yace, kaji na rantse maka sai kayi,kama futo da mata, yau dinnan a kayi ma kanninku baiko sai ku manyanku daku kun girma kuna zaune mana a gida, yaya majeed ya zaro ido yana fadin, uncle rantsuwa fa kayi, uncle alkasim yace, of course son zamu zauna mu zuba muku idone, dama ina shirin yin maka maganan, kasa kawai yayi da kanshi yana murmushi, don shi abun ma dariya yake bashi yanda suka dage da gaske suke, uncle ibrahim yace,

bafa wasa muke ba musamman A/majeed kai da sagir kune manya ya kamata kuyi ma kanku fada saboda duk wani mutum mai kamala baya kammaluwa sai da aure, iyali sune cikon rayuwan da Adam, sunna ne babba kun sani, uncle lamido yace, wannan hakane gaskiya, don haka duk ku futo da matan da zaku aura, in kuma babu se in sani, ya karisa maganan yana kallonsu,,,

yaya baffajo yai saurin fadin, uncle nifa bani da matsala, uncle lamidon yayi dan dariya da fadin,yawwa aha nawan, a'i na sanka mutumin baka da sanya, ya kalli yaya sagir yace, sai kai custom sagir kai muke sauraro, yana dan bata rai yace, ah nima fa bani da matsala ta wannan side din kawai dai matsalan na en canjinne, yace, karka damu za'a samosu bakin border, ya koma kan yaya majeed yana fadin, commishner ina fatan dai ba matsala,,,,

yaya majeed ya dago kai tare dasa hannu yana dan gyara zaman hulan dake kanshi, kaman baxai magana ba, sai kuma yace, akwai matsala fa, uncle lamido yace, to kaima na encanjinne, yai dan ajiyar zuciya da fadin, a'a amaryan ne babu ita, dariya suka kuma yie uncle ibrahim na fadin, babu amarya akwai kuwa babban matsala, uncle lamido yace, to lallai ka duba gasu nan variety of color, ka bincika kai ko anan family baxa ka rasa mata ba, ga yeye nan, da sauri dad dinshi yace, ah yama bincika kawai cikin family din hankali na zaifi kwanciya, in er family ne basai an tsaya ana wasu bincikan halaye ba, don haka daga nan har Abuja ka duba matar aure, uncle lamido yace, zamu baka time don ka bincika amma baffajo da sagir tsanani five month ne mun kammala babban magana, yaya sagir na zare ido yace, da wuri haka?

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now