Chapter 22

1.6K 93 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

  *ina tune daku, kawaye na GGUSS k/kosh*

fatima Aliyu Nasarawa
maryam Abubakar Bilbis
Amina muhammad B/gwari
shamsiya ishaq B/gwari
fareeda Abdullahi dan ibro
Aisha Ibrahim mai iyours
hajaru da Rukayya ishaq anka
Haleema Aliyu Adafka
        *taku~Halima ja'afar yakubu*

*wattpad@Maamee Ja'afar*

*page 21~22*

――――Safiyar sunday ne aka kin kintsa gidan, naja su Nuwairah da Abdul muka tafi ta backyard din gidanmu, wajan shakatawa, hira muke, ina cikin wani farin ciki da nishadi, a duk sanda na tuna haduwan mu da yaya majeed a jiya, har lokacin na kasa mantawa, yayin da nake jin wani irin sanyi sanyi da kwanciyan hankali, a ciki n garin zazzau,,,,

A site din mummy na samu aunty jidda da mummyn zaune, a falonta suna hira, na shiga da sallama tare da samun guri gefe daya bisa kujera ina zama, nai shiru ina kallon mummy data dada hada fuska, bayan shigowa na, aunty jidda ta kalleni da kulawa take fadin, yadai akayi meenal?na wani hadiye tsoro ina dan dada kallon mummy nace, dama zanma mummy godiyan earring din data sai mun ne, nagode, Allah kara budi, aunty jidda tace, Amin, ta kalli mummy dake wani basarwa, sannan mummy tace, hmm dama dai ba meenal ba, don zata iya careless da dankunnin nan, ni kuma gaskiya in hakan ta faru, mutum bazai ji da dadi ba, aunty jidda ta kalleni, tana fadin, haba kaman meenal, ki kula dasu kinji, kudine masu yawan gaske, nace, to in sha Allah, tace, good tashi kije Allah miki albarka, na mike tare da barin falon,,,,,,,

mummy ta kalla tana fadin, kai sa'adatu, ku rage ma yarinyan nan, wasu abun, ko magana direct, bata iya muku, duk kunbi kun raineta da tsoro, mummy tace, itace dai tasa ma kanta hakan, amman meye wanda ba m.....katseta aunty jidda tayi da fadin, akwaishi kuwa, banbacin da kuke nunawa tsakanin su da Amal, ki duba fa, yanda kuka kashe ma Amal kudi, ita ko yer henna design dinnan, ban ganshi a hannun taba, dole wani abun tai tunanin ko baku kuka haifeta ba, nikaina bacin kin shayar da ita gabana, Abdullah kuma ina wajan, sanda kika haifeshi, da sai ince ye'yen wasu aka kwaso aka kawo miki, mummy na bata rai tace, aunty kwata kwata abun ba haka yake ba, baki gane yarannan bane kullum haka suke, ka haifi dane, baka haifi halin shiba, ni kayan ma dakika kashe musu kudi, Allah da baki bata kudin kiba, suna da kayan su, har gwara ma Abdul, amm.....sake katseta tayi tana fadin, nidai yimun shiru, babu ruwanki da kudin dana kashe musu, komai da kuke yi, daga ke har senator a'i ina gani, ba yau na saba zuwa gidan ba, kun maida yarinya kaman wata bora, ina gudun muku rannan daza kuyi dana sani, da wannan hallayyar, rashin adalci tsakanin ye'ye, musiba ne, yana kawo kiyayya a tsakanin su, sannan ya sanya musu rashin hadin kai, mummy tace, aunty nifa bansan mai zan rika yinma yarannan bane, tace, ke kika sani a'i dama ni tsiyata dake, shegen kafiyan nan, tun ba yanxu ba, in kina son abu, to kefa shike nankina so, to wannan so ko wahala, in zaki banbanta tsakanin ye'yenki, amman ki tuna ko hadith din manzon Allah(SAW) yana cewa, muji tsoran allah, kuma muyi adalci a tsakanin ye'ye yenmu,(hattara iyay)

don haka ina baki shawara daku canza tsari, tai dan tsaki tana cigaba da fadin, maybe sai na fada ma umma ma, wannan halin naki, kota ita inta miki fada kyaji nata, mummy ta zaro ido tana fadin, umma kuma, don Allah karki hada ni da ita, akan ye'yennan, tsaki tayi, tana cigaba da yima mummyn fada, amman maimakon ta sauka, sai ta data hawa tana daura laifin gaba daya akan ni meenal.


*****
――Rayuwa kenan, na kasance cikin farin ciki, a ko da yaushe, ina ganin kaman zan iya mallarkan abin da nake so, amman na kasa gane abu daya, a duk lokacin da muka hadu da yaya majeed, dalilin da yasa yake bina da wani irin kallo, ko kuma ya tsareni da ido, kwarjininsa na kuma futowa, na nisa, ina tuno ranan event din daddy da farko ma tsorata nayi da irin kallon da yake mun, sanda ya dago fuskata, naji wani tsigan jikina na tashi, na runtse idanuna, ina jin wani feeling, kaman lokacin abin ke faruwa, nai dan tsaki, wata zuciyan na raya mun, shima yana jin yanda kike ji a kanshi, daya bangaren kuma na raya mun, umh uhm meenal maybe dresing din da kika yine, ya jashi, ba kiga yanda ya manta, ya share kowa ba, ke kadai idanunsa ke gani, na mike zaune daga kwacan da nake, ina bude wata side drower na, na ciro, pieceis na ankon su ummee har guda  hudu, na zuba musu ido ina murmushi, tare da raya, yaya majeed kana son kwalliyana, nima ina son burge ka, kayi mun a rayuwa, kuma kai nake so, promise, zan baka mamaki bikin su ummee, zan dage wajan ganin na samu sutura, irin wanda kake so, koda mummy zata kasheni da fada ne, zan tabbatar da ana mun koda rabin abin da ake yinma Amal, nai shiru ina kuma tunano hiran mu dasu sameera, wai ance cikin family zai zabi matar da zai aura, kuma an bashi lokacin bikin su ummee, yayi amfani da wannan daman, wani sashi na zuciyana na fadin, to inya kasance kene meenal, na wani saki murmushi jin dadi, ina jingina bayana da pillow, nasan yaya majeed bazai zabi wata can useless din yarinya ba, sai wanda ta jiku, ta amsa sunanta model baby, inko hakane to Amal na cikinsu, don nasan Amal ta iya kera dresing,,,,,,,,,

wata bakar zuciya ne, ta shiga raya mun, kema fa meenal sai kin tashi tsaye ya kamata kiyi amfani da lokacin bikin su sameera, ki saka kaya masu kyau da tsada, tare da yin duka ankon nasu, inkin fita wannan, kisa wannan, tabbas ko da yaushe idanunsa, zasu kasance akanki, yayin da wata zuciyar ke faman raya mun, to ina zaki samu duk wadannan kudin da kuma kayan, tambaya mai kyau,,,,,,,,,

Nadan rankwafar da kai, cike da tausayin kaina, ina fadin sai in dage da rokon mummy in sam...., ban karisa tunanin da nake yiba, sai jie nayi mummy ta turo kofa tare da mai dawa ta rufe, tana huci ta zaune gefen gadon Amal tana kallona, wani irin faduwar gaba ya saukan mun a lokaci daya, don kwata kwata babu sauki a tare da fuskanta,,,,,,,,

kaman daga sama naji tana magana cikin zafin murya take fadin, ke meye tsakanin da A/majeed?, nai kuri ina kallonta, yayin da cikina ke wani kullewa,murya na rawa nace, mummy bakomai, tace, ke karki kawo mun gulma da munafunci, bayan an fada mun kuna tare wajen event din dad dinku, har yana miki hotuna, na dafe kirji ina zaro ido, zanyi magana, ta daga mun hannu da fadin, ke dakata mun don Allah, taimun wani serious look tana cigaba da fadin, this should be the first and the last time, daxa ace mun angan ki dashi, ina miki good warning, ki futa hanyar sa, mutumin daya fara ganin yer uwanki yace, yana so, to mene kuma na shishshige masa, Amal ya gani, kuma itace sa'a auranshi, ba keba, don haka ki koma cikin hankalinki,,,,,,

tuni wasu hawaye suka wanke mun fuska ina fadin, mummy bafa ha......ta galla mun harara da fadin, madam bana ce kimun shiru bane, ban karisa maganan dana ke yiba, don haka, ki saurara mun, kinsha kai karata maybe gurin yer uwata ban saniba, to burinki ya cika, don tace, zata hadani da mahaifiyata,banji ba, ban ganiba, abun da nafi tsana a rayuwa na, bana muku sutura, bana kula da ku, to yanxu aka fara, indan kayanki zasu kaca kaca, ni sa'adat bazan asaran kudi na insai miki ba, koda kuwa suna zuban mun ne, na gama, tunda iya kokarin da nakeyi, ba'a gani kinsa daddy ku ba yin.......sai kuma ta katse maganan da fadin, kee basai na tsaya miki, bayaniba bazan yi bane, zaki fara gani tun daga bikin su zarah, sai dai ki tafi tsirara, duk da wahalar da nake na school dinki, ba'a gani ba, to shi kenan, fine, ni a saukina, na rantse ko zan miki sutura sai anjima da yawa, ki bita can egypt din ki fada mata, daga haka taja wani tsaki tana barin dakin, dai dai sanda Amal ta shigo tana murmushin mugunta,,,,,,,,

ta zauna inda mummy ta tashi, tare da kuma gintse fuska, tana hararana tace, is better mutum yayi hanzarin futa daga hanyata, a bar mun abin dake shirin zama mallakin nawa, don ko kina wanka da perfume, kina tashi da powder, ni dinnan nayi gaba, sai labari, kuma bro.majeed nawa ne, ni daya, ba kari, nidai dinnan Amal s gidado, taja tsaki tana hayewa gadonta, ta kishingida, sanda na saki wani irin marayan kuka, ina kallon rashin adalci, da mamaki, ta kara jifana, da wani hararan tana fadin, sai kuma kiyie, ta jawo wayanta tana saka earpiece a kunni take fadin, soyayya ciki nai dace a gaskiya, na samu zabin Allah bana shan wuya.

******
――Tun ana boye mata lamarin, har dai aka gaji aka fada mata,ranan haj. tayi fada kaman me, ta kuma zaga bayi ba adadi, itama zarah ranan taji komai dake wakana, dama kwananshi uku yau bexoba, kuma baya pickn call dinta tayi kuka sosai ,koba komai an bar mata tarihi arayuwanta, asa maka ranan aure ace kuma anfasa, amma ta brama allah kome, tausayi kam taba ma kowa, harda kakanta wanda taci fada kaman ta ari baki.

sati daya da faruwan lamarin ya diro garin, ya samu hutu ne, bayan yen watannin da yayi a gurin ai'ki, da zancan fasa auran zarah ya fara cin karo, don haka sauri sauri ya isa dakin haj. don jin cikakken bayani.

so ko wahalah?
*2018*
comment&share

meemartjj💕......✍🏻

thanks💕

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now