Chapter 31

1.9K 103 3
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

*Dedicated to mum and dad* 

*wattpad@Maamee Ja'afar*

*page 30~31*

――――zaune yake a babban falon gidan, tun sanda ya iso ta kasa tsaye, ta kasa zaune, ta cika mishi gabanshi da kayan ciye ciye, dana sha, tun yana mata sannu da kokari, harya gaji ya koma yana dan binta da kallo, tare ciro wayanshi yana dannawa, har lokacin da mummy ta shigo falon, cikin tafiyan kasaita ta manyan mata, sosai suke gaisuwan mutunci, tana dan jin kunyan wai shi sirikinta, shiko ko a jikinshi, don tun ba yauba, tasan uwa take a gareshi, ko sisters din mum dinsu bai saba dasu ba, kaman yanda ya saba da mummy sa'adatu, Amal ta koma kujeran dake kusa da nashi, tana zama, tare da kallon mummyn tana fadin, mummy kinga bro. majeed  na shirya masa table tun dazu, amman ko drink yaki yasha, ta karisa maganan cike da shagwaba, na sangarci, mummy nadan murmushi tace, a'a Amal ba yanxu kika kammala shirya maiba, ki tsaya kiga inya tafi bai ciba tukuna, ta sa hannu tana daukan babban kwalin exotic, tare da glass cup ta bude tana zubawa, sannan ta mika mishi, da wani irin kallo, ya amsa yana wani murmushi, cike da dan yake, tare da rikewa kawai a hannu, yana kallon mummy yace, mummy kuyi hakuri, ina taso naxo na duba jikin baby, a'yyuka ne sun mun yawa, ban samun time, hope ta samu sauki, karaf Amal ke fadin, baby kuma, wace bandani? ita kanta mummy sai da tayi dan jim, tana ganin lokaci yayi da A/majeed zai daina kiran meenal da wannan sunan, ta kalli Amal dake jiran amsa, gogan ya wani shareta, tace, Amal kibarshi pls ya gama maganan mana, mummy ta cigaba da fadin, a'iko A/majeed da kabarshi ma, taji sauki, don har ta koma school, ya dan nisa lokacin da yaji ta sako maganan makaranta, yana fadin, ok ta koma can hostel ne?mummy tace, a'a,  ina ganin ta kara barine taji sauki, kafun ta koma, ya dan dukad da kai yana fadin, ok, ya kalli Amal da fadin, big baby pls kije, bari inyi magana da mummy, ta bude baki zatai magana, mummy tayi saurin yin mata sign alaman karatai magana, tana tsoron Amal din ta kara kwabsa magana,
ta mike tana fadin, ok, if u finishe, pls let me know, ta futa yana dan binta da ido, tare da kuma raya, ta cika rawan kai da yawa,,,,,,,,,

ya nisa lokacin da yake dawo da hankalinshi gun mummy, yana fadin, mummy don Allah dama ina son rokan wani alfarma ne, tace, ina jinka,meya faru A/majeed, yace, ina son meenal ta bar zaman hostel, ta dawo gida, tunda naga daganan zuwa school din nasu, ba wani nisa banedashi, tabarshi kawai ta rika zuwa dagaa gida, mummy tayi shiru, sannan tace, anya A/majeed ba wani abun tayiba, sai da gabanshi ya fadi, ya dake yana fadin, no mummy ba haka bane,ko daya, just dai, ana yawan kawo mana irin cases din nanne, indan aka samu wasu ye'yen da basu da tarbiya, suna lalata tarbiyan wasu, both mata da maza, kuma naga ita bata da wani nisa da school din, jikinta yayi sanyi, da kalolin wasu yen tunani, take fadin, a'iko nagode A/majeed, sai yanxu nima nake dana sanin barinta a hostel, meenal da take wata sakarya, ba wuya a juya mun tarbiyanta, kwata kwata bata da wayau, zansa driver kawai ya kwaso mun kayanta, yai dan shiru kafun yace, babyn ta futa ne?mummy na dan bata fuska tace, eh bata jima da tafiya school dinba, sai kuma 6pm nake tunanin zata dawo, tayi dan jim, tana kuma fadin, ni sai ina ganin kaman akwai abun da meenal tayi, kodai kana boyewa ne?yai wani murmushin yake yana fadin, mummy karki damu, ba abun daya faru, ban cika son zamansu a hostel bane, momma ma daga gida, take zuwa nan samaru, kausar kuma tana xaune gidan uncle usman abuja, mummy tace, hakane, bayi da wani amfani indai, ba can nesaba, babynmu ma, bansa yanda za tayi da karatun ba, dadina ma auran nan da zatayi, sai lokacin ya danyi kasa da kai, yana tunawa da wani auranshi wai da Amal, ya nisa da fadin, ba damuwa mummy, ina da gida a can kano, sai ta zauna, cike da farin ciki take fadin, Alhamdulillah, hakan yayi, Allah sanya albarka, ya mike yana fadin, mummy ni bari in wuce, tare da ije cup din da Amal ta mika mishi, tunda yai sip biyu, bai kara shaba, mummy ta mike tana fadin, bari na kira maka Amal din, da sauri yake fadin, a'a da kin barta, sauri nake, zamu hadu next time, daga haka sukai sallama da mummy, bayan ya cika su da kudi, ya samu ya shiga motarsa yana bari gidan, Ama na futowa farfajiyan gidan, take tsaki, sanda ta hangi motarshi na barin wajen gate, ta koma cikin gida cike da kunkunai.

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now