Chapter 10

1.8K 113 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

*dedicated to my dearest friend and also a sister,,,Haalimatu y umar《maaameee》ummu seeyama*

*🌸pls ina kara fada,,don Allah a rika ije karatu lokutan ibada da school da kuma lokutan a'iki masu muhimmanci,,tnx🌸*


Vote me on wattpad
*Maamee Ja'afar*

*page 09~10*

――――Na samu kusan 2month ina gida bana futa ko ina duk da ban cika futa ba sai da naji na takura, ga mummy da tsatsauran ra'ayi, ina ji ina gani akai bikin sadiya amma ta hanani zuwa har kuka sai da nayi daga karshe na hakura na fawwala ma Allah komai.

―― kusan shekara daya kenan da kammala school dina, gashi zaune kawai nake a gida ba'a neman mu wata school ba, gashi niba sana'a garenba, na koma kaman wata marainiya, mummy nema kama zata naima mun ABU last year sai kuma maganan yasha ruwa,,,

don haka na shiga zullumin wannnan shekaran, duk da dai nayi jamb wannan year din, amma banda tabbas za'a nema mun school din, don last year haka result dina ya futo yai kyau amma duk a banxa.

Tun kafun ta shigo take kwala ma mummy kira,hannunta daya na janye da trolley bag karami sai kuma hand bag data makale a dayan hannun, doguwar rigan material ne a jikinta sai ta rolling dankwalin a kanta, ta shigo main falon mu inda nake zaune ina kallo, ta kara yin haske da kiba, ga wani bakin goggle dake idonta, da karfinta take fadin, mummy!mummy!,mummy ina kike,,,,,

Da sauri mummy ta futo daga site dinta, har suna kusan cin karo da juna, a rude mummy ke fadin, Amal meya faru ne?,Amal dake ije handbag dinta kan cushion tai murmushi tana fadin, mummy ina gifts dina ance jiya an kawo mun, mummy tace, waya fada miki?Amal ta zauna tana bata rai tace, mummy wanda jiya fa aka a'iko driver dashi ya kawo mun, mummy tace, amma ba don shi kika dawo ba ko?,tace, mummy don shine mana kinsan yanda kyautan nan yake so special to me kuwa? daga mummy fa muna waya nace, yace zai tafiya, shine nace yaimun tsaraba, i was just joking, yesterday kawai muna waya sai cewa yayi harya a'iko mun dashi gida, shine ko yau early in the  morning na kwaso, kayana nayo gida, ta karisa maganan cike da farin ciki, mummy tace, to gift nawa kika sha amsa, amma sai wannan duk kin wani rude, tai wata yer dariya tana fadin, hmm mum yhu won't understood, nidai muje kiba ni kyauta na, ta mike suka shige ciki,mummy na fadin, Allah yasa baki baro important lectures ba kika taho, na bisu da ido kawai ina mamakin wanda yayi kyautan, na dai san ba mubash bane, don yasha bata gift amma batai irin wannan murnan ba.

A daki ta zube kayan bisa gadonta, kaya ne sosai daga kan kayan make up zuwa su takalma ne da dai sauransu, nabi kayan da kallo tare da sister Amal wanda ke cikin farin ciki take fadin, this is the most fevorate gift i ever have in my life, ta rungume wani kawlin turare tana fadin, thank u so much my sweet bro.

can kuma naga ta daga waya tare da dailing number ta kara a kunni, ta saki murmushi sanda akai picking call din tana fadin, hello my bro. majeed, sai da gabana yayi wani irin faduwa, na runtse idona kaina na wani irin juyawa, ina ji tana cigaba da mishi godiya wai kayan sun mata kyau kuma kyauta ne da baza ta manta dashi ba forever, tana fadin, thank u my dear bro, da sauri na tashi na bar dakin don bazan iya jure jin wa'innan words dinba, can backyard din gidan mu na tafi na zauna, ina tunani yanda zan manta da majeed dinnan a rayuwata, na rasa inda zansa kaina, haka ranan na wuni ko daki naje naga kayan kan mirron Amal sai naji bakin ciki, na rasa dalilin hakan, don in mubash yayi mata kyauta bana jin irin hakan.



SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now