Chapter 77

2.3K 53 0
                                    


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?~~~3*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj*

*page 77*

――――Sallama yayie na dago kai muna hada ido tare da amsawa, zaune muke a falon tare dasu salima, raina duk a bace, tun sanda naga gwiwan nata, da dan damuwa yake zama kusa dani tare da fadin,,,

  soyayya nah, yadai me yake faru ne, ko babyna ne ke damunki?na dan yamutsa fuska da fadin,,,

  yaya majeed, gaskiya abin da ake a makarantan su momma ba kyautuwa, bai kamata su rika dukan yara ba, kaga yanda wani malami ya maida ma momma da kneels dinta, ya dan zaro ido fadin,,,

  tooh, kodai wani laifin ta mishi, hakanan a'i baxai hukunta taba, na kuma bata rai da fadin,,,

  ba wani nan, dama can yanda take yawan complain din teachern, ya fiye takura ma rayuwanta, na karisa maganan kama zan kuka, gaba daya idanu ya zuba mun kafun ya saki wani murmushi yana fadin,,,

 
  soyayya nah, kie daina damuwa haka, kika sani hakan ya zame musu alkhairi, zaro ido nayi, ina dan hararansa da fadin,,,

  yaya majeed donfa baka ga gwiwan nata bane, yasa kake mai dashi wasa, momma ta wuce wannan hukuncin, ina laifin ya bata wani purnishiment din, karfa ka manta elder sister nane, ya dan nisa, sanda yake fadin,,,

yanxu ina momman take, nace,,,

  tana dakinsu, tunda ta dawo take faman kuka, da alama abin yayi mata zafi, salima yasa ta kirata, ta futo rai bace, ido yai jaxur, dai dai nan mummynsu ta futo itama tana zama, sanda momman ke dada maimaita abin daya faru, yaya majeed na fadin,,,

  a'iko m.Nawwas din nan, yasan mutunci, yana da kirki a'i, iyayan sama mutana azziki ne, mummyn su tace,,,

  kajie ko, shie yasa nace, hakuri zatayi, ta kuma fashewa da kuka tana fadin,,,

  mummy nie ban yarda ba, bashi da wani kirki, a gabana yace ma wata yarinya ta wuce, be mata komai ba, kuma kawai don yana sonta ne, duk aka zuba mata idanu, sanda mummyn ta rike haba da mamaki, kafun ta fara mata fada, shie ko sai  kallona yayi da daga mun gira yake nunata, alaman dama na fada miki, zaro ido nayi ina kallonsa, yana wani kirne fuska da kallonta yake fadin,,,

  karya nayi kenen, da sauri take fadin,,,

  nifa ba haka nake nufi ba, na dan girgixa kai, kafun ince,,,

  kaga, yaya majeed plss zaifi kawai yanxun ka kaita clinic su duba mata ciwon, raunin yayi yawa, yadan mike sanda yake fadin,,,

   daddys princess, kiyi hakuri, wata ran sai labari, tashi muje kie amso magani, mikewa tayi rai bace, sai gata sanye da hijjab, yanxu ba ko yaushe take son saka gyale ba, duk ta sanja, Nabila tasa atishawa mai karfi, kowa ya kalleta, yasan neman excuse din da zata bisu kawai takeyi, bata gajiya da yawo, da hannu ya yafito ta alamar, zo muje, ta daka tsalle tana dira daga kujeran da fadin,,,

  yesss, mummynsu tai murmushi da kallonta take fadin,,,

  Allah ya shirya mana, daga haka suka fice daga falon, ina tausaya ma momma dake tafe da dingishi.

Daren ranan kwace take a gadon, sanye cikin classy night wear dinta, hannunta rike da cute heart pillow din, tana shafa gashin jiki, tare da kallon waje daya, mamakin kanta takeyi, ita maryam yer gayu, yer masu kudi, shine ta fada son talaka, talakan ma wanda ko a'iki bai fara ba, lallai bata da burin daya wuce ta aure wani dan professor ko governor, shine zata kai kanta irin wannan down level din, sai dai kuma wadannan basu suka fi damunta ba, kaman yanda take mugun jin tsoro, kar yanxo m.Nawwas din shi baya jin abin da take jie game dashi, musamman idan ta tuna da abin da yayi mata a yaudin, ta kuma saka sabon kuka tana nitsar da kanta cikin tattausar pillow din, data tada kanta dashi, da raya,,,

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now