Chapter 70

2.4K 89 4
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W @H@L@H?~~3*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj*

*page 70*

――――A mota ya lura da irin mood din da nake, amma sai bece mun komai game da lamarin, yana jana da hira, tare da fada mun yanda zan ga garin makka, da dai sauransu, sai gashi lokaci kankani na manta dukkan damuwa, muna hira muna dariya,,,

haka muka isa haunwa, sunyi farin cikin ganin mu, lokacin da salima da Nabila suka zagayeni da murna, kowa ke fadamun abin da zan siyo musu, lokacin da aunty mariya ke musu tsiyan a'ikena zasuyi kenan, haka sister kausar da maryam suka xo sukai joining dinmu, salim ma ya shigo yana faman fadin,,,

aunty meenal wata arebain jallabiya yana nan, karki manta plss, dariya akeyi ana hira, kowa na farin ciki, banda sister maryam data hada giran sama dana kasa, tare da dabi'ar na daura kafa daya kan daya, tana girgixawa, tunda ta gaishe da brothern su, ya amsa yana futa zuwa site din daddynsu, ko inda nake bata kalla ba, tana dai bina da harara ta kasan ido, sister kausar na fadin,,,

momma me za'a siyo miki ke?sai data wani yastina fuska kafun tace,,,

no basai ta wahalar da kanta ba, indai maryam ne, bana so, zaro idanu sukayi, dama mummynsu ta tashi ta futa a falon, salima tasa dariya tare da zuba yatsu wajen kunnuwa tana kallonta da sakar mata gwalo, take fadin,,,

yeee mudai muna so, a harzike ta dago tana fadin,,,

salima zanxo nan, in faffalla miki mari, kin rainani ko, sister kausar ma ta tsaida ita da saurin tana fadin,,,

no no no, karki sake ki taba ta, kinyi ma wasu ne, shi yasa itama ta miki, cikin jin haushi ta koma ta zauna, tana dan gyara skirt din daya digile saboda zaman da tayi na daura kafa daya kan daya, tare da cigaba da danna wayanta, bata kuma cewa komai ba, muna hiran mu da sister kausar,,,

a haka ya shigo yana fadin, inxo mu tafi, aunty mariya ta futo musamman ta yafo gyale, rike da hannuna, duk yaran gidan suka rankaya rakomu wajen mota, nan muka same dad dinsu, ta kaini wai ya samun albarka suna magana suna yer dariya, ba abin daya shafesu yaransu na wajen,,,

nan kuwa yayi mun nasiha, ayi ibada da kyau, tare da shi mana albarka, sai gashi kaman zanyi kukan dadi, wato wata lokacin baka bukatar mahaifin daya haifeka yasa kayi feeling shi ubane a gareka, wasu iyayan da basu haifeka ba, mutanan arzirki, zasu saka kaji kaman sune iyayanka na a'inihi, haka dai kowa namun fatan alkhairie, harda sister kausar data rungumeni tana fadin,,,

ohh really gonna miss yhu, ta dan sakeni tana cigaba da fadin,,,

karfa ki manta, kie dawo da wuri, saboda duk wani preparation na bikina da ke zanyi, dariya mukayi ina fadin,,,

karki samu damuwa sister, daga haka mukai sallama muka tafi, su kuma suka koma ciki.

a falo ta tarad da sister maryam, zaune ita daya tana faman kumbura, kaman an mata wani babban alamari, sister kausar ta zauna da kallonta take fadin,,,

wai momma meye matsalanki da meenal, naga yarinyan tana da saukin kai, me yasa kwata kwata baki son kulla alkhairie da it....... da sauri ta katseta cikin fushi take fadin,,,

never, never ever in this life, me take dashi, na rasa gane abin da take dashi kuke rawan kai idan taxo, harda shi brother, zai wani siya ma mota, sannan ya kaita hajji, daga ta auri yayanmu, ita ba kowan kowa ba, amman taxo ta fimun, bamu da mota ya siya mata, sannan yanxu ya kaita saudiya, na rasa meye take dashi da brother ke rawan jiki a kanta, tswssssssss! taja wani tsaki tana girgixa jiki, alaman abin ya zafeta, sister kausar kawai idanu ta zuba ma maryam din, duk inda take tunanin yarinyan ta wuce haka, mamaki da dariya duk suka kamata, tana tafa hannu da fadin,,,

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now