🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕
*Dedicated to fans so ko wahala*
*matukaaa ina godiya da irin comment dinku, tnx so much, luv u all💕*
*wattpad@Maamee Ja'afar*
*page 20~21*
――――mummy ta bata rai, tana dan tsaki, tace, niban san abun da meenal ta tsaya yiba, sai kace ba nan cikin GRA ba, ta kuma yin wani tsakin tana kallon kofa,,,,,,
Dai dai sanda na shigo gurin rungume da ipad posse dina, sai kuma dayan hannun dana dan kama doguwar rigan dake dan ja da kasa, ana hangen takalmin dake kafana kadan kadan, idanu gaba daya ya dawo kaina yayin da mc ke gabatar dani amatsayin, second daughter na senator sulaiman gidado Abba, hutuna ta ko ina kakeji, yayin da masu daukan labaru suke ta a'ikin haskani,(karku manta diyan senator ne😉) tafiya nake dai dai dai, yayin dana ji kafana namun nauyi, saboda idon da sukai mun yawa, dai dai nan kuma naga ana mun alama da in tsaya in daina tafiya, na dakata ina dan ja na tsaya,,,,,,,
Abdul na hango yana tasowa daga inda yake zaune, tare da hayowa wasu yen steps, yana karisowa inda nake tsaye, ya kalleni naga ya wani saki murmushi, nima na kallesa ina murmushin, sannan muka karisa inda su mummy ke tsaye jere da juna, a matsayin real brother and sister, kowa na sha'awan yanda muka jero, shi kanshi daddy kallon mu yake da murmushi a fuskan sa, banda mummy da Amal da suke wani basarwa, naje ta gefen mummy na tsaya, yayin da Abdul ya tsaya ta gefen daddy, mc na fadin, plss put your hands together for this wonderful family, aka rika tafawa, karo na farko dana jini a matsayin ye' a family sulaiman gidado Abba, haka ma ta bangaren Abdul,,,,,,
Daddy ya yanka cake din, mummy ya fara ba, sannan Amal, muma munci azzikin idon baki, mummy ma ta bashi, tana nuna kulawanta a kanshi sosai, aka rika basu hannu, muka sakko daga wajen, bayan kammala yanka cake din, ana cigaba da gabatar da program, da sauri naje ina rungume aunty jidda, na dago cike da farin ciki nake fadin, aunty jidda nagode, thank u so much, itama tana fara'a tace, Allah sarki daughter meenal, karki damu, ta shafa kunnina, tana cigaba da fadin, ki kula da wannan earring din suna da tsada sosai, musamman mummy ki ta a'iko da kudi a siya miki su, na dan zaro ido da mamaki ina fadin, mummy, tace, of course, mummyn kufa, don haka kije ki mata godiya, na dan saci gefen inda take zaune suna gaisawa da wasu bakin ta, hada ido mukayi da ita, tai saurin wani basarwa tana juyawa, tare da cigaba da magana da friends dinta, aunty jidda ta rike hannuna tana fadin, muje ku gaisa da wasu friends din mummyn naku, don yawanci basu sanki ba, sai wannan yer lelen,,,,,,,,
sosai wasu abokan daddy suke ta mamaki wai yana da wasu ye'yen bayan Amal, yayin da wasu friends din mummy suka rika surutu, wai ni carbon copy dinta ne sak, tana fadin, ita kar a hada ta dani, don na fiye muni, aunty jidda na fadin, ta dai fi wancan sangartaciyan first born din naki, barayin Amal ma seat dinta ta koma ta zauna, gaba daya ruwan kanta ya kare, tana jin kaman ta koma gida ta sanja dresing, yayin da sister kausar ke faman fadin, meenal tayi kyau, so cute, kai Amal, gaskiya sister meenal tafiki kyau sai yau na lura, yayin da ita kuma sister maryam ke fadin, kai sister kausar dresing ne kawai ya canxata, amman sister Amal ta fita kyau, ta kalli Amal din tana cigaba da fadin, sister Amal me yasa ba kiyi irin nata dresing dinba,yafi kyau, da dacewa da event din sosai, shiru ne kawai amsan da Amal take iya badawa a wannan lokacin, don tunani sun hadu sun mata yawa, ga mubash dake ta damunta sai taje inda yake,,,,,,,,,,
Gaba daya komai ya tsaya mishi, mutuwar zaune kawai yayi, tun lokacin data shigo wajen har sanda ta isa gaban cake din kallonta yake, ya kasa dauke idanunsa a kanta, karo na farko daya ji wani irin zafi a zuciyansa lokacin daya sata kallon wasu guys din a wajan, irin mutuwar zaunan da yayi suma shi sukayi, da dama yarinyan ta burgesu, yayin daya ji su uncle idris na musun ba ita bane, shi kuma yaya baffajo na fadin, majeed kaga mutumiyar naka kuwa, yai shiru yana tunanin, a sanin shi in yaga yarinya tai kwalliya tana burgeshi,kuma baya taba jin haushi don wasu maxan sun kalleta ko sun yaba kwalliyan, amman me yasa yake jin zafin, shigan da meenal tayi a yau, yasan haka nema, da baice ta dawo ba, babban burinsa yaga ta bar hall din, don haka lokacin da aka fara ciye ciye, wasu na tashi, ya mike ya bar hall din yana kiran numbern kausar,,,,,,,,