🖋🖋mata tagari🖋🖋

1.6K 58 1
                                    

📄📄📄   Written by deeja one love 📄📄
Dedicated to Fatima Hussein (bestie)

Bismillahir rahmanirrahim
001
            
Cikin sauri take shirinta domin tasan olredy tayi late kuma yau sai an dake ta.
Wani yaro ne da bazai wuce six years ba yashigo dakin.
Hannunsa rike da sweet yana sha.
Kallonta yayi yace "
Aunty ummi tace kiyi sauri munyi latti.
Jaka ta dauka tareda nikab tace "
Muje to.
Falo ta fito inda ta sami ummi a zaune da sauran yan uwanta.
Kallonta tayi tace "
Ummi mun tafi.
Cikin fara'a tace "
To Allah ya Baku Abin da kuke nema.
Amin ummita..
Cikin sauri suka bar gidan.
Tsakanin makarantar da gidansu da Nisa hakan yasa suketa sauri.
Makarantace dake Cikin unguwannin talakawa dai dai bakin classes din ta tsaya.
Dalibaine a tsaye da alamu WA,'inda sukayi lattine suma.
Ajiyar zuciya ta ajiye sannan ta karasa wajen.
Wacce bazasu wuce sa'annin juna bane ta dago tace "
Fati yau kinyi latti.
Wacce aka Kira da Fati tace
Hmm kedai Bari wlh bansan yadda akayi ba na makara .
Nafisa tace "
Tab bulalar mal Abdul na nan na jira.
Cikin tsoro tace meh.
Nafisa ta guntse dariya tace
Wlh Dan yazo tun dazu.
One love tazo kuwa?
Cewar Fatima .
I think so kinsan bata cika latti ba.
Wani Farin saurayi ne ya fito daga daya daga Cikin ajujuwan dake jere
Ya kallesu yace
Yanzu ake zuwa makaranta ko?
Kowa ya Fara kokarin Kare kanshi da uzururruka.
Dakatar dasu yayi yace
Ya isa haka ku shiga ajin mal Faisal Ya Zane ku.
Shiga suka Fara Yi daya Bayan daya ana zanesu.
Cikin jin zafin bulalar da akayi Fatima ta shigo ajin.
Kusa da wata ta je ta zauna a hankali tace
Hi baby
Dagowa tayi fuska a daure tace
Ya akayi
Dan karamin tsaki Fatima taja kafin tace
Waccen mutumin mana shi bayawa mutane uxuri a rayuwa.
Mal Abdul Ya dago daga karatun daya ke yace
Haba na gaya muku ku Dena Yin surutu Idan ana karatun Al qur ani
Allah Ya hana.
Kowacce ta ja baki tayi shiru Karatu yake amsa har yazo kan Fatima.
Cikeda nutsuwa ta bayar da haddarta.
Mal Abdul yace
A gaskiya wajen hadda ina yaba miki kin fi duk matan nan kokari.
Fatima tayi shiru kasancewar yadda taji matan suna kananan maganganu.
Murmushi tayi sannan ta Mike ta amso qur'nin ta ta koma ta zauna.
Ganin yadda kawarta ta ta daure fuska yasata yin shiru itama.
Karfe sha biyu da Rabi Kowa Ya fito domin sallah.
Dalibaine sunfi Dari kowana kokarin yin alwala.
Can na hango Fatima ta nufi wajen yan ajinsu.
Naja ta Kalli Nana tace
Anya Kuwa Fati bason mal Abdul take ba?
Tabe baki walida tayi tace
Oho musu Idan sonshi take Ai shima alamu Ya nuna
Nana tace
Kai walida waye besan malam maryaam yakeso ba kawarta salon taji kuma Abu yazo Ya cabe musu.
Naja tace
Aini haka nakeso wlh naga karyar shakuwa da anyi magana one love one love.
Dariya suka kwashe dashi.
Nafisa dake gefe tanajinsu bata sa baki ba tace
To waiku ina ruwanku ne dasu mtsew gulma kawai .
Fatima ce ta karaso tayi musu sallama suka amsa sannan tace
Nafisa baki gane mini one love Dina ba.
Cikin rashin kunya Naja tace
Gata a bayana.
Fati tace
Kinga Naja am not ur mate plz respect ur self.
Au daga magana
Cikin sauri nafisa tace
Waike dake tayi magana ne.
Ko tace najane?
Kinga Fati na ganta tabi wancan lungun.
Da sauri ta juya tabi hanyar......
Tundaga nesa ta hango shi yana ta faman murmushi yayinda kawarta ta juya baya.
Jingina tayi a jikin bango ta kafeshi da idanu itadai bata gajiya da kallon wannan bawan komai nashi burgeta yake Yi.
Dafa kafadarta taji anyi
Cikin sauri ta juyo.
Tace
Khadeeja kece?
Eh nice yanzu nake tambayar nafisa tace kina nan .
A hankali Fati tace
Maryam nazo Nema sai na sameta da mal Abdul suna fira.
Murmushi Khadeeja tayi sannan tace
Sun bar mutane na alwala sunzo suna bawa flower ruwa .
Yake Fati tayi tace
Zo mu tafi.
A hankali ta waiga ta kallesu daidai lokacin da Ya  idanunsa sai a Cikin Nata

Mata Tagari Where stories live. Discover now