🖋🖋🖋mata ta gari 🖋🖋🖋

310 20 0
                                    

📄📄📄story and
                              Written by
                     Deeja one love📄📄📄
Dedicated to Fatima Hussein (bestie)

012
Hannunta maryam ta rike sannan tace
One love Ki Dena tuhumata Akan abinda inada damar da zanyi amfani da ita.
Girgiza Kai Fatima tayi sannan tace
Wlh one love ina Jiye miki shiga matsala an fa sa miki rana?
Na sani one love kada ki damu.
Ranar yini Fatima tayi Tana mamakin maryam din Idan bata manta ba akwai saurayin da Ya taba tare ta tayi mishi wulakanci just bcoz of mal Abdul.
Har sati Ya zagayo Abin yana damunta.
Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya.
Ayau dai bikin maryam da mal Abdul Saura sati daya.
Tabbas Fatima taga canje 2 daga kawarta ta.
Fatima ce keta sauri domin tanaso taje ta sami maryam din Don su shirya abubuwan da zasuyi.
Sallama tayi ta shiga gidan.
Maryam dince ke wanke wanke.
Cikeda fara'a suka Tarbi juna .wanke wanken ta Cigaba da tayata.
Dagowa tayi ta Kalli maryam tace
Wai one love har yanzu banji kince komai game da rabon Kati ba.
Daure fuska maryam tayi tace ke ki kyaleni kawai Dan Wlh ni kadai nasan me nakeji.
A sanyaye tace
To Allah ya yaye miki.
Ba Wanda ya kuma magana har suka Gama wanke wanken .
Wajen mama taje ta gaisheta sannan ta mata sallama.
Dakin aunty fadila ta leka,maryam Kwance kan katifa Tana Waya yayinda aunty fadila ke goge kaya.
One love zan tafi.
Daga mata yatsu biyu tayi.

Alamar see you later.
Haba one love Ki taso ki rakani mana bafa mu taba Haka dake ba
Fatima ta gaya idanunta na kawo ruwa Kamar zatayi kuka.
Dan murmushi maryam tayi kafin tace
Sugar crush Bari nayi escorting one love .shiru tayi alamun akwai abinda Ya ke gaya mata.
Dariya tayi kafin tace
Kasan Bana son kukanta kuma da alamu kukan zatayi.
Shiru ta kuma yi kafin tace
Haba crush ka cika matsala Wlh son danake mata daban kaima naka daban kasan ina sonka...
OK me too bye.
Fatima ta juyar dakai gefe Cikin dacin rai ta Fara tafiya.
Barin gidan tayi Cikin sauri Tana Hawayen takaici.
Maryam ta biyo ta da sauri Tana kiranta .
Sai da ta hada da gudu sannan ta cimma ta .
Haba one love Meye Hakane Wai. Ta fada Tana haki.
Juyowa Fatima tayi tace
One love yanzu kin Dena ji Dani ko?
Ba haka bane fa  yanzu bagashi na rakoki ba.
Dariya suka yi sannan suka juya suka Cigaba da tafiya.
Har bakin titi ta rakata kafin ta juyo.
Yau ya rage Saura kwana uku
Wanda tun Ranar da Fatima taje gidansu maryam bata koma ba haka itama maryam din bata zo ba.
Itakam Fatima ta kasa gane inda maryam ta dosa.
Gashi yan makarantarsu sai damunta suke.
Wayar Tane dake gefe yayi kara kallon screen din tayi amma bata gane waye ba.
Dagawa tayi.
Sai dai tanajin muryarsa tayi saurin mikewa.
Jikinta har rawa yakeyi.
Cikin daburcewa ta amsa masa da to
Hijab dinta ta zura ta fita.
A gefen wata plantain tree ta ganshi tsaye ya juya baya da alamu Waya ma  yake yi.
Cikin nutsuwar data tattaro ta nufeshi.
Jin taku Ya sashi waigowa tsaf Ya kafeta da Idanu har Tana hardewa Kamar ta fadi.
Sallama ta masa Ya amsa.
Sai da suka gaisa sannan ya ce mata
Nazo ne Naji me kuka tsara na game da bikin?
Zufa ta goge tace
Wlh naje ranarnan amma batace komai ba sai dai ina ganin kawai walimar ayita bayan biki .
Eh hakan yafi dama shine dacewa da sunna.
Yanzu gashi.
Ya miko mata ledar dake hannunsa.
Amsa tayi. Ya Cigaba da cewa
Kati ne a ciki nasan zaku rarraba sai kuma ku fadi sauran abubuwan da kuke so.
To zanje wajenta Naji.
OK sannan Dan Allah kice Idan na kira ta daga Wayar Dan kusan five days kenan data Dena picking call dina.
Da sauri ta kalleshi gabanta na faduwa.
Kada dai abinda take gudu ya afku.
Cikin dakiya tace
Insha Allah zanje na mata magana.
Na gode ya juya ya hau mashin Dinsa ya tafi.
Ta dade tsaye a wajen kafin ta ajiye Ajiyar zuciya ta shige Cikin gida.

Mata Tagari Where stories live. Discover now