🖋🖋🖋mata tagari 🖋🖋🖋

406 33 0
                                    

     📄📄📄story and written
                               By
                                 Deeja one love 📄📄📄
Dedicated to 
           Fatima Hussein (bestie)
003
Tunda Fatima ta kwanta duniyar tunani ta fada.
Tabbas ta tabbatar Tana son mal Abdul.... To amma ya zatayi da kawarta aminiyar ta Maryam
Wannan Ai Abin kunya ne ace  tarasa Wanda zataso sai saurayin da kawarta takeso.
Kuka ta fashe dashi.
Cikin sheshsheka tace
Amma so bai mini adalci ba yarasa Wanda zai so sai Wanda aminiya ta keso.
Har Karfe biyu barcin yaki zuwa.
Ganin hakan bazai fishsheta ba yasa ta Mike ta dauro alwala Ta Tada sallah domin neman zabin ubangijinta (wannan shi akeso musulmi mumini kayi bawai yanke  hunkunci direct ba)
🍬🍬🍬🍬
A dai dai wannan lokacin kuma a bagaren aminiyar Tata .
Kwance take Tana Waya da rabin ran Nata.
Lumshe ido tayi tace
Habibi da'eeman me Kake yanzu ne.
A hankali Kamar me rada yace
Karatu nake mana kefa?
Barci nake kiranka ne ma Ya farkar Dani.
Hmm tunda har na tashe ki to Ki tashi  ki gaida ubangijinki kinji.
To angama sahibul kamala.
Yar dariya yayi yace
Habibaty Wlh inasonki da gaske.
Ni shaidace habibi.. Yauwa shine dazu   ka yaba karatun one love Ko?
Murmushi yayi yace
Kada ki ce mini itama kishi kike da ita   
Of course yes. Itama ai macece
Haba habibaty be kamata kina fadin hakan wannan be dace ba.
To Ya isa haka kada muja da yawa Nidai Abin da na sani kawai ina sonka kuma ina kishinka..
Lumshe idanu yayi yace
To shikenan yanzu tashi kiyi mana addu'a.
Zunboro baki tayi tace
To
Kashe wayar yayi kawai..
Tsaki taja kawai a Ciki tace
Gaskiya barci nakeji ...
Ajiye wayar tayi ta juya sai barci...
Ta bagaren mal Abdul kuwa
Murmushi yayi yacigaba da karatunshi.
Sai Karfe uku na dare sannan ya tashi ya Fara sallah.
Zuwa Hudu da Rabi ya yi raka atanil fajr sannan ya wuce masallaci.
A bagaren Fatima ma haka ta kasance
Tana idar da sallah ta Cigaba da yin zikiri har gari yayi haske sannan
Tayi raka a biyu (wannan Manzon Allah yace duk Wanda yayi hakan to ladansa Kamar Wanda yayi aikin hajji da umura wallahu a, alam.)
Parlour ta fito ta Fara aikin hada break fast Don tasan ummi da abban sun tafi makaranta can magumi.
Sai wajen goma ta Gama Wanda hakan yayi daidai da su ummi suka dawo.. Dama olredy kannenta sun rigada sun tafi makarantar Boko.
Ita kuma kasancewar ta Gama secondary school yasa take zaman gidan.
Gaidasu tayi sannan suka shiga sukayi wanka sannan suka fito..
Tana zaune Tana jiran fitowarsu.
Suna fitowa suka nufi dinning area..
Serving din ummi tayi ita kuma ummin tayi serving din abban..
Murmushi tayi domin hakan yana burgeta duk tsanani ummin bata yarda yaranta suyi serving mahaifinsu.
Kayan dasu ga gama break fast din ta dauraye sannan ta kunna kallo Tashar manara TV.
Ummi kuwa barci ta kwanta hakan yasa gidan Ya koma ita daya..
Wayar Tane yayi ringing.
Ganin me kiran ya sata yin murmushi sannan ta dauka..

Hello one love..
Daga dayan bagaren ta amsa..
Aslm one love kina jina..
Eh ya akayi..
Dama na kirane na gaya miki na siya mana wannan Jakar...
Yes Kai one love Allah Ya barmini ke.
Cikin zakuwa Maryam tace
Kinsan me dazu yah sadik yake ce mini gobe uncle Ibrahim zai dawo.
Fati tace
To Idan ya dawo me zai miki?
Ki jiki one love ba shi yah sadik zai kaiwa maganata da mal Abdul ba..
Jiki a sanyaye Fatima tace
Oh Hakane..
Yanaji Kinyi low ne kalau kuwa?
Yeah am fine kawai tunani nake in Kinyi aure zanyi missing.
Fatima ta gaya
Cikin jin dadi Maryam tace
Ayya kada ki damu  AI zai barni na Cigaba da zuwa..
Fatima ta numfasa tace
One love take care of yourself bye bye
OK bye love you
Hmm OK...
Shiru Fatima tayi Tana Ajiyar Zuciya lallai Idan tayi sake zuciyarta zata sa ta jin kunya... (Nidai Nace aikin Gama ya Gama Fatima)
Pls vote for me and follow me on my wattpad 13 deeja

Mata Tagari Where stories live. Discover now