🖋🖋🖋mata ta gari 🖋🖋🖋

373 27 0
                                    

📄📄📄story and written
                        By
                           Deeja one love 📄📄📄
Dedicated to Fatima Hussein
Ina taya dukkan Al ummar kasarmu murnan hawan buhari a Karo na biyu. Allah yasa hakan shi yafi alkhairi samari ayi murna amma pls ayi me tsafta kada Garin murna kaje Ka halaka kanka Ko kajiwa  kanka rauni.allah ka k'ara zaunar da k'asarmu Lafiya.
023
Sallama tayi daga Cikin daki aka amsa mata.
Tabbas sai da ta shigo abubuwa da yawa suke dawo mata, Yar kwallar idanunta ta goge.
Dago labule akayi mama na fadin
Oyoyo 'Ya tagari,shigo daga ciki,
Ruwa me sanyi ta kawo mata ta sha, gaisawa sukayi Cikin mutunci
Sunkuyadda Kai Fatima tayi tace
Mama ya wajensu Maryam.
Hade rai tayi tace
Au  ita kikazo tambaya dama ba gaisheni kikazo yi ba.
Fatima ta ce
A'a. Mama nazo gaisheki ne sannan Idan da number ta Abani.
A sanyaye tace
Kawarki tunda ta bar nan  bata sake kiran Kowa ba.
Gashi ainihin gidan da aka kaitan munje Wai sun tashi
Cikin kuka Fatima tace
Kuma mama sai baku nemeta ba?
Wata ajiye da zai nemeta Fatima ai tasan inda Muke ina? Ko mun canza gida ne.
Girgiza Kai tayi Tana share hawaye.
Kinga zo ki tafi tunda Idan kin zauna Anan gidan bakida Abin da zakiyi sai kuka.
Share Hawaye tayi tace
Yi hakuri mama bazan kuma ba .
Sai wajen sha biyu sannan ta tafi gidansu,nan ma dai fira sukayi da Maman har Hindu suka dawo makaranta.
Fatima ta basu labarin Abin da mama ta gaya mata.
Tabe baki Hindu tayi tace Oho ita ta sani
Harara Fatima tayi mata tace
Bansan Rashin kunya.
Tashi tayi tace
Ai duk Wanda ya bi motor kwadayi zai sauka a tashar wulakanci.
Sai bayan isha sannan ya zo suka tafi.
Washegari haka ta tashi da zazzabi me zafi
Zuba mata idanu yayi yace
Bintu me ke damunki Hakane ina sane jiya fa baki barci ba kuka ki ka dinga yi.
Cikin jin zafin ciwo tace
One love my peach.
Tsaki yaja ya Mike yace
Dama tun farko sai da Nace kada kije gidan ai amma da muka kara wucewa ta kofar gidan kika sake nacewa da ace na hanaki kuka zaki saka mini gashin nan ai...
Maganar ce ta tsaya ganin Tana yunkurin amai.
Janyota jikinshi yayi hakan kuwa yasa ta sharo masa shi.
Kasancewar babu abinda taci yasa Aman tun yana fita har ya koma kakarine.
A hankali ya Fara Lafa mata kwantar da ita yayi Ya Fara shiga bayi ya wanke jikin shi sannan yazo Ya dauketa ya kaita bayin ya mata wanka.
Kaya ya sa mata ya Kai ta parlour kan three seater Ya kwantar da ita.
Bedroom din yaje ya gyara sannan ya dawo ya kamata ya suka fito.
Me okada Ya tsayar Ya shiga ita ma Ya shigar da ita.
Direct asibitin limi suka je.
Layine Gashinan na jiran likita .
Sai da ya yanki Kati sannan ya dawo ya zauna a Kusa da ita.
Tun safe sai wajen sha biyu sannan layin yazo kanta.
Daukan ta yayi Cak har office din likitan.
Sai da ta gaya masa abubuwan daya dameta sannan likitan yace suje a musu test.
Result din ya amso Ya kawowa likitan.
Kallonshi likitan yayi yace
Congratulations my friend ur wife is two months pregnant.
Alhmdllh dagata sama yayi yana murna shi kanshi likitan dariya yakeyi.
Direct gidansu Ya wuce da ita.
Gaisawa sukayi da mama sannan ta kwanta.
Har wajen la'asar Tana barci.
Rahina ce tazo ta tasheta.
Sai da tayi sallah sannan aka kawo mata abinci.
Alale ne na gwangwani hakan kuwa Ya mata dadi ta kuma ci shi sosai.
Ganin hakan yasa mama ta ajiye mata Wani da dare shi ta kuma ci.
Da suka zo  tafiya mama tace
Kada ka takurata taci abinda bataso duk abinda take so ka kirani ka gaya mini ni zan dafa mata.
Ai ji tayi Kamar kasa ta tsage ta shige saboda kunya.
A hanya ta kalleshi tace
Shine ka gayawa mama Ko
Dariya yayi yace
Bazan iya boyewa bane.
Zaro idanu tayi tace
Badai Ko ina kagaya ba ko.
Babu Wanda na sani Wanda ban gayawa ba
Har da abba?
Eh mana
Turo baki tayi ta Fara matsar hawaye, dariya yayi yace
Bintu kenan Rigima ke yanzu Idan aka ce miki na gayawa abba sai ki yarda ai da kunya.
Hakadai Ya Cigaba da tsokanarta har suka karasa gida
Yanzu dai ciki ya fito sosai haihuwa Ko yau Ko gobe..wanda ma be saniba ya sani ga Karatu Dan suna last semester a 200level inda Allah Ya taimaketa an tafi strike.
Lemo ne a gabanta tun safe shi take sha.
Sallama yayi Ya shigo
Zama yayi Kusa da ita yace
Maman biyu hutawa akayi.
Dariya tayi tace
Wlh peach kada kayi mini baki.
Oya albishirinki
Goro
Kwalin Waya ya miko mata.
Duba Wayar tayi infinix knot 5
Dariya tayi ta Kankame shi Tana murna
Kwasarta yayi sai daki daganan dai suka farantawa juna rai.
Yau tun safe take jinta Wani iri daurewa kawai takeyi Waya suke da khadija.
A daddafe tace mata
Sai anjima.
Fitsari taji tanaji hakan yasa ta shiga bayi Aifa Fitsari Ya fito Abu ya gagara ciwo sai karuwa yake
Gashi mal Abdul Ya tafi shago ya duba yanayin yadda yaran suke tafiyar da shagunayen dan yanzu likafa ta Cigaba.
A daddafe ta fito ta dauko wayarta ta kirashi Tana kuka Tana fadin
Kazo zan mutu
A rude yayo gida ya dauketa sai asibiti   kiran su ummi yayi Ya fada musu Hakama mama.
Awajen tare suka iso.
Har wajen hudu shiru iya rudewa ya rude nurses ne kawai ke shige da fice
Sai wajen biyar sannan likitan ya fito
Da sauri mal Abdul Ya tareshi yana tambayarshi Ya  ta haihun?
Kafin ya bashi amsa nurses guda biyu suka fito da yara Kowacce a hannunta da sauri suka karasa har rige rigen daukarsu sukeyi sai da mama ta harareshi sannan ya Janye hannunsa yana Sosa keya.
Aka sakawa ummi a hannu farinciki ba a magana.
Nurse ta kallesu tace
Na hannunki ta nuna
Ummi tace
Shine Hassan Waccen kuma Hussein na hannun mama.
Readers ga  Fatima ta haifi twins maza (ya Allah ka bani su Ameen )
Idan da Wanda zai rakani Muje suna to Ya daga hannu Nidai zanje koda a gayyar karerene. Aha to.....

Mata Tagari Where stories live. Discover now