🖋🖋🖋mata ta gari 🖋🖋🖋

361 26 0
                                    

📄📄📄story and
                  written
                      By
                         Khadeeja Muhammad
                            One love 📄📄📄📄
Dedicated to
   Fatima Hussein (bestie)...
005
Gidane na masu rufin asiri duk da bekai gidansu Fatima kyau ba amma duk da haka an kawatashi daidai karfin masu gidan...
Mata biyu ne aciki kasancewar mutuwar mijin Kanwar babansu Maryam din yasa ta dawo gidan da zama..
Ciki da parlour ne guda biyu Wanda suke manne da juna, Dayan na mama ne Dayan kuma na aunty fadila ne..... Haka suke kiranta...
Sai wata matakala Wacce bata wuce four steps ba a nan dakin maza yake....
Sai wajen tap da rijiya a gefe....
Fadin gidan babu laifi kuma malale yake da siminti tsaf tsaf an shareshi...
Da gudu suka shigo gidan ayayin da maryam kebin Fatima...
Dakin mama Fatima ta shiga direct maryam din ta rufa mata baya...
Mama dake zaune Tana kwaba Garin Dan wake ta dago da sauri ganin Ko suwaye yasa taja tsaki sannan ta daka musu tsawa...
Wannan wane Kalar haukane ku shigo gida da gudu....
Duk da hakan saida  Fatima ta tsallaketa sannan ta zauna...
Maryam Tsayawa tayi Tana Kallonta..
Numfashi take ajiye wa a hankali Kamar Wacce tayi gudun fanfalaki..
Kallon maryam tayi Wacce ta bata rai.
Dariya tayi ciki ciki sannan tace
Wlh na rigaki Don haka dole ki bani.
Mama dai Ko kallonsu batayi ba ta Cigaba da abinda take...
Aunty fadila Wanda lekowarta kenan domin ihunsu da gudun da sukayi yasata farkawa daga baccin datake tace
Wai meya faru ne??
Fatima na haki tace
Wai fa ina wannan bangles din da Didi ta kawo mata daga Saudia to shi tace zata bani Idan har na rigata kuma Gashi na rigatan...
Aunty fadila ta Kalli maryam tace
To sai ki bata tunda dama baki ke yanka Wuya...
Tsaki maryam taja sannan ta juya ta nufi dakin aunty fadilar kasancewar a can take kwana..
Fatima ganin hakan yasa ta Mike ta bita da sauri..
Tarar da ita tayi ta kwanta tayi ruf da ciki Tana Danna Wayar ta...
Haba one love ya zaki shareni bayan kinsan mun Saba hakan dake...
Banza tayi da ita.
Ganin taki kulata yasata kwace Wayar  ...kallon screen din tayi..
Hoton malam Abdul ne Wanda da alamu besan an dauke shi hoton ba..
Sanye da jallabiya me ruwan kasa hakan sai Ya kara fito da hasken fatarsa.
Kurawa hoton idanu tayi dan Ya matukar burgeta..
Ta bagaren maryam kuwa fatimar take kallo Tana nazarin yanayin fuskarta...
Tabe baki tayi sannan ta fuzge Wayar tace
Kin Wani kafa masa idanu Kamar yau kika taba ganin sa...
Ajiyar zuciya Fatima tayi sannan tace
A, a  one love kawai ina ganin dacewar ku ne.
Hmm haka kika ce Ko..?
Eh mana to Meye Dan na Gayi hakan..
Eh nasan mun dace nifa inasonshi sosai...
Maganar ta daki Fatima sosai amma ta daure tace
Nima shaidace one love.
Karar Wayar maryam din yasa suka Kalli Wayar.. Sugar crush ne rubuce ajiki.
Dauke fuska Fatima tayi sannan ta Mike tace
Ina wajen mama Idan kin Gama inform me pls..
Gyada Kai kawai tayi sannan ta dauka.
Cikeda shagwaba take amsa  Wayar Wanda hakan yasa Fatima kara saurin ficewa daga dakin.
Mama ta tarar bakin murhu Tana saka Dan waken, Da sauri ta amsa ta Cigaba da saka mata...
Duk da aiki take amma hankalin ta na kofar dakin duk bayan lokaci kadan take duba kofar dakin...
A haka har Ta Gama sakawa ta kwashe ta soya Mai duk bata fito ba.
Wani bangare na zuciyarta yana bata shawarar ta shiga dakin kawai Wani kuma yana hanata..
Mama ta dago ta dubi Fatima tace
Jeki kicewa maryam tazo Kuci abincin mana.
Da sauri Kamar me jira ta Afka dakin
Daidai lokacin da suke gayawa juna kalamai masu sanyaya ran masoya (😂 lol)
Batasan lokacin dataje ta fuzge Wayar ba ta kashe a fusace ta juyo ta kalleta.
Maryam kuwa idanu ta zuba mata Tana Kallonta..
Ganin irin kallon da maryam din take mata ya sa jikin ta yayi sanyi.
Ahankali tace
Mama tace kizo muci abinci..
Murmushi maryam tayi sannan tace
Muje to.
A tare suka jera har dakin mamar .
Dagowa tayi ta kalleta sannan tace
Sannu sarauniya kinacan a Kwance ni ina nan ina aiki Ko sai kawarki ce ta amsheni.
Cikin sauri Fatima ta katseta da cewa
Lah mama Waya take fa
Eh dama ai bakusan laifin juna.
Kallon juna sukayi sannan sukayi murmushi suka fara cin abinci.
Bayan sun Gama Fatima ta Kalli maryam tace
One love taso ki dauko mini na wuce gida .
Mikewa tayi taje ta dauko mata jakar ta bata
Kallonta tayi ta bata rai sannan tace
Bani bangles din.
Tsuke fuska tayi sannan ta dauko ta Mika mata.
Murmushi tayi sannan tace
Muje na rakaki...
Tafe suke a hanya suna fira sai yawancin lokuta Akan tsayar dasu samarin hanya su  nuna suna son maryam din kasancewar ita Fara ce ita kuma Fatima bakace(wanda a zamanin yanzu samari sun fison Marar mace)
Hakan ya zamar musu jiki indai suna tafiya sai an nuna anason maryam din Wanda hakan be taba damun Fatima ba.
Maryam ta Kalli Fatima tace
Wai one love hakan baya damunki
Cikin halin Ko in kula tace
Mefa
Ganin bakida saurayi har yanzu.
Murmushi tayi sannan tace ke hakan ya dameki ne
Daga kafadu maryam tayi sannan ta ce
A, a
Murmushi Fatima tayi sannan tace
To kin gani nima baya damuna har yanzu ban wuce teenagers ba fa .kuma ma duk me sonki ai ni yakeso tunda duk dayane.
Haka suka Cigaba da firar su har suka isa gidansu Fatiman.

Mata Tagari Where stories live. Discover now