🖋🖋🖋mata ta gari 🖋🖋🖋

332 26 0
                                    

📄📄📄story and
                    Written by
                           Deeja one love 📄📄📄

Dedicated to Fatima Hussein (bestie)

009
Ummi suka Tarar azaune Tana Karatu, da sauri ta Mike Tana tambayar Lpy kuwa?
Maryam ce ta bata amsa da
Wai kanta ke ciwo.
Ummi Tabe baki tayi tace
Hmm Allah Ya shiryaki Wlh rakinki yayi yawa Fatima..
Murmushi maryam tayi tace
Ummi ai hakan nan bazata dinga kuka ba, to Naji ai dama dayanku baya laifi.. Jeki ki koma makarantar ki..
Ke kuma ta nuna Fatima
Je kisha sudrex ki kwanta Allah Ya sauwake.. Ya mutsa fuska tayi sannan tace, to ummi...
Juyawa tayi ta Kalli maryam tace
Tnxs one love bye
U wlcm...wish you quickly recovery..
Wucewa tayi ta cire hijab din ta da kayanta...
Bathroom ta fada tayi wanka sannan ta zo ta kwanta.
Duniyar tunani ta fada Tabbas ita tata kaddarar kenan fashewa ta kuma yi da kuka... Tabbas so masifa ne ita dake kokarin cirewa amma kara mannewa yake a zuciyarta
Ya ilahi..
Tunowa tayi Da murmushin daya mata.
A take ta Fara murmushin itama (Nidai Nace to Hindu ta Gayi gaskiya masoya mahaukata suke koma waye☺☺☺)
Acan makaranta kuwa mutum hudu ne a zaune
Khadeeja ta Kalli nafisa tace
Haba nafisa be kamata ace makiya najin kanmu ba...
Dariya Aisha tayi tace
Aifa Wai makiya ke nifa na Fara kishi..
Ke dawa maryam ta gaya Tana Danna wayarta .
To Kowa Ya tashi sai Ya wareni gefe..
Kinata magana a baibai.. Khadeeja ta gaya tana kunshe dariya.
Harara ta aika mata sannan tace
Wlh ina daf da ja miki Jan Biro...
Kwashewa da dariya sukayi sannan nafisa tace Wai maryam ni na kasa gane inda kuka saka gaba..
Kamarya fa. Maryam ta tambayeta
Na keda mal Abdul mana
Dariya sukayi gaba daya sannan maryam tace
Amegbo nafisa zama da Wai'nnan yasa kin Fara kaitan sa ido Ko
A, a gyara maganarki young lady
Suka fadi Atare
Cikin murmushi tace
Dazu ma da safe baba yahya yace Nace mishi ya turo..
Atare suka ce
Da gaske suka juya suka Kalli juna suka kuma kwashe da dariya..
Maryam tace
Allah Ya nuna mini Ranar da zaku Dena wannan iskancin  ...
Dai dai lokacin da tasa Wayar a kunnenta
Still har ta Gama ringing ba'afara daga ba.
Hmm tab Wai wa kiketa kirane since.
Dan karamin tsaki taja kafin tace
One love mana inaso Naji Ya jikin Nata
Sake Kira tayi, Cikin sa'annin kuwa Ta daga
Hello one love Haba inata kiranki shiru baki daga ba?
Kokarin daidai ta maganarta tayi sannan tace
One love ina barci ne..
A sanyaye maryam tace
Kuka kika Cigaba ko
Hawayen dake fuskarta ta share sannan
Tace
A, a barci ne kawai danayi
Karyane one love kuka kikeyi ko nazo ne.
Nope ki zauna  kawai ba  Wani abun
OK Idan an tashi zanzo and promise me bazaki kuma kuka ba..
Fatima ta kuma share hawayen fuskarta sannan tace
I promise you that...
OK glad to hear that bye.
Kallonta sukayi suka ce
Meya sameta?
Kanta ke ciwo shine take kuka
Dariya sukayi sannan
Nafisa tace
Allah Ya kyauta tab
Aisha tace
Ameen wannan qauna haka.
Dundu ta Kai mata Khadeeja tayi saurin tarewa tace
A, a Ya da haka .
Hakadai suka Cigaba da surutunsu har aka koma aji.
Karfe hudu da Rabi yau aka tashi Maryam duk ta kosa a tashi ta je taga jikin one love dinta...
Su shida haka suka tafi gidan su fatiman har da masu zuwa gulma dai ...
A bakin titin dazai shigar dasu GRA suka sauka daidai Wani kiosk suka tsaya maryam ta sayi credit.
A bakin gate suka tsaya sun Dan jima kan azo a bude musu kofa su shiga..
Hindu tayi musu jagora har dakin nasu kasancewar ummi bata nan hakan ya basu damar yin shiriritarsu a gidan..
Sun jima sannan maryam ta miko mata katin tace
Gashinan ki saka a wayarki kuma anjima zan kiraki and don't forget u have promised me that bazaki kuma kukaba.
Juyawa tayi ta kallesu tace
Ku kuma Idan kun Gama iskancin naku ku taso Mu tafi.
Dariya Aisha tayi tace
Mufa Bamu muka dorawa one love din taki ciwo ba da zaki damemu... Juyawa tayi ta Kalli Fatima tace
Allah Ya sauwake yasa a Dena yiwa headache kuka ..
Dariya Naja tayi tace
Kinsan komai samun wjene.
Ba Wanda ya tanka mata
Mikewa gaba daya sukayi zasu tafi
Har sun Kai bakin kofa maryam ta juyo tayi mata blowing kiss 😘
Khadeeja ce ta dawo bayan duk sun fita.
Zama tayi ta kamo hannun Fatima tace
Fatima komai da kike gani a rayuwa hakuri ake ba kodayaushe Idan kana son Abu Kake samu ba nasan Meye Matsalar ki amma kada ki manta Allah baya barci sannan ina so duk Wuya duk runtsi kada ki sake ki Bari makiya su samu damar yi muku dariya.
Cikin kokarin waske zancen
Fatima tace
Haba khadija nifa Wlh kawai haka Allah Ya halicceni da yiwa headache kuka.
Dariya Khadeeja tayi tace
Haba Fatima am Mature enough da zan gane ba ciwon Kai kikewa kuka ba soyayyar mal Abdul ce ke saki kuka.
Cikin sauri Fatima ta tashe bakin Khadeejar idanunta ya kawo ruwa tace
Na shiga uku Khadeeja Kowa a aji Ya gama sanin inason mal Abdul...

Mata Tagari Where stories live. Discover now