🖋🖋🖋mata ta gari 🖋🖋🖋

289 24 0
                                    

📄📄📄story and written
                            By
               Deeja one love. 
💄💄💄                         💄💄💄💄💄
            💄                     💄                    💄
             💄                   💄                        💄
                💄💄💄💄💄  dedicated to
                  Fatima Hussein (bestie)

Na sadaukar da wannan page din ga one love dita wato maryam khamis
Dake goruba 3 sabon gari Zaria,
Miss you so much 😘😘😘.

010
Khadeeja ta girgiza Kai tace
Matsalar shine Fatima baki iya boye soyayyar da kike masa.
Kura mata idanu tayi Tabbas gaskiya ne to amma babu yadda ta iya.
Khadeeja zatayi magana Aisha ta Leko tace
Wai Khadeeja wace gulmar ake ne.
Murmushi Khadeeja ta mata sannan ta Mike kallon Aisha tayi ta galla mata Harara tace
To Muje mana.
Bayan  tafiyarsu shiru tayi Tana nazarin Maganar Khadeejar wato Kallonta sukeyi kawai tana Haukar ta gaban daya jikin ta yayi sanyi.
Wayar ta ta janyo
Gallery ta shiga pic dinshi Wanda ta tarar maryam na kallo Ranar nan shi ta Nemo ta zuba wa idanu.
Ita ta rasa me yasa take son wannan mutumin.
****            ****           ****            ****
Washegari Ranar lahadi haka ta shirya ta tafi makarantar duk da ba  yadda batayi Akan ummi ta Barta ba taki .
Cikin material ne lemon green da touch pink Tabbas kayan Ya mata kyau sosai komai to match ne sai dai hijab da yake uniform ne lemon purple.
A nutse suka tafi yau Dan da wuri suka fita.
Ta tarar da yan ajin yau sunyiwa Kansu fada sunzo da wuri.
Shi kanshi yau mal Abdul din Cikin farin ciki yake.
Tabe baki tayi watakila hakan baya rasa nasaba da albishir din jiya.
Maryam ta tabota tace
Ki Kalli littafin ki malama .
Saukar da Kai kasa tayi Kamar me saurare amma ina ta tafi duniya tunani...
Gaba daya hankalin ta yayi Wani wajen. Maryam ce ta kuma tabota tace
Ke mal na magana.
Kallonshi Fatima tayi tace
Na'am.
Cewa nayi karanta.
Ya bata amsa. Daburcewa tayi tace
Me zan karanta.
Oh Abin da nake bashi kike sauraro ba ko make damunki?
Ya tambaya.
Kasa magana tayi sai dai idanunta daya kawo ruwa
Girgiza Kai yayi sannan yace
Maryam khamis me yasa mi  kawarki ne?
Cikin sanyin jiki tace
Bansaniba Wlh kawai haka take ne
Kallon Fatima yayi yace
Mike tsaye.
Umarninsa tabi.
Tana daga tsayen akayi karatun aka Gama... Kuma a hakan sai da ta karanto.
Bayan sun fita sallah ne nafisa ta daga kyallen atamfa dana material tace
Ga ankon Aisha an fitar dariya sukayi sannan suka ce
Sai yau
Khadeeja tace.
Nidai gaskiya banda kudin yi
Naja tace Haba Yama za'ayi ace biki Saura ten days a  fito da anko .
Nafisa ta kalleta tace
Aike kam Ibrahim Ya tsaya miki Naja.
Maryam  ta Kalli Fatima tace
One love ya za'ayi kinsan dai mal bazai mini anko badai Ko?
Fatima tace
Nima babana bazai mini ba kinsani.
To yanzu ya za'ayi?
Maryam ta tambayeta
Abinda za'ayi kawai shine zan kira kawu ja'afar nasan zai mini.
Fatima ta gaya.
Maryam tace
To nima dai zan San yadda zanyi nayi mana atamfa Idan yaso ke kiyi mana material din.
OK Fatima ta bata amsa.
A haka har aka tashi Kowa Ya kama hanyar gidansu.
Ranar talata Fatima ta Kira maryam a Waya ta gaya mata ta sami kudin ankon duka biyun.
Cikin farin ciki maryam din tace
OK gobe zamuje mu siyo.
Washegari kuwa hakan akayi. Sukaje suka siyo daganan suka biya suka kaiwa tailor dinsu.
Yau ta Kama Ranar jum 'a Ranar daurin auren Aisha..
Taro sukayi gwanin ban sha'awa... Duk da maryam taso Adan cashe amma dangin amarya sukayi mata cikas. Khadeeja ta kalleta tace
Wlh maryam baki dace da malamummu ba.
Da sauri Fatima ta dubeta tace
Ya zakice haka ?Haba khadija ,
Dariya Aisha tayi tace
Tab Allah Ya kyuta kina Matar malam kinason Casu.
Duk da daure fuskar da tayi hakan be hanata dariya ba sannan tace
To ai ni social ce shi kuma ustaz.
Dariya sukayi gaba daya kafin nafisa
Tace Maganar khadija dai itace gaskiya.
Walida tace
To Aini zanso na kalla wannan zaman auren Tsakanin social da ustaz.
Duka Fatima ta Kai mata tace
Bazaku kyale mini one love dita bako.
Cikin nishadi suka Cigaba da firarsu Kamar yadda suka Saba Tsakanin kawaye dai....
Dare yayi dai dasu aka Kai amarya bayan an Gama Abin da aka Saba na aure Kowa Ya fito domin komawa gida...
Fatima ta Kalli maryam tace
One love akwai kudi da yawa awajenki kuwa.
Girgiza Kai tayi tace
A'a kinsan na sayi pad.
Dazu. Dan karamin tsaki Fatima taja kafin tace
To yanzu ya zamuyi.
Shiru maryam tayi zuwa can tace
Yes na tuno Bari na kira azo a daukemu.
Cikin maamaki Fatima tace
Wa zaki Kira?
Maryam tace
Take it easy mana zaki gani ai.
Sakin baki tayi har maryam tayi kiran ta Gama.
Jiran kusan 15mins sukayi kafin ya Iso .da sauri maryam ta Matsa jikin glass din tace my crush har Ka Iso.?
Fatima ai Sakin baki tayi Tana kallon abinda yafi karfinta....
Vote for me on my wattpad @13deeja

Mata Tagari Where stories live. Discover now