🖋🖋🖋mata ta gari 🖋🖋🖋

336 24 0
                                    

📄📄📄story and written
                            By deeja one love 📄📄📄
Dedicated to Fatima Hussein(bestie)

Allah yasa ayi zabe Lafiya Allah kuma ya bamu shugaba nagari.
Muna nan muna addu'a Allah Ya zaba mana Wanda yafi alkhairi.
And pls sisters da kinyi zabe ki tafi gida Dan Allah ba ruwanki da akasa atsare dinnan ki Bar maza kawai duk Wanda ya Nemi da ayi Tashin hankali kada ku  biye masa please Allah Ya kara hade kanmu ya zaunar da kasarmu Lafiya Ameen
016
Fatima tace
Ni bazan miki gori ba amma ki sani abinda kikayi yaudara ne.
Yaudara yaudara fa kikace ke kuma da kikeson abinda aminiyarki takeso akiraki Dame ko angaya miki bansan kina son mal Abdul bane.
Fatima ta bude baki zatayi magana Mama ta shigo dakin.
Harara ta ballawa maryam sannan ta Kama hannun Fatima suka fice a dakin .
Mama ta kalleta tace
Allah Ya miki albarka Fatima ubangiji ya baku zaman Lafiya kada ki yiwa iyayenki abinda kawarki tayi mini.
Fatima tace
Mama ban fahimta ba me kike nufi.?
Mama ta Kalli Khadeeja tace
Kamata mamana ki Kaita gida kinji daganan kiyi gida Dan biki ya tashi kuma.
Khadija tace
To mama sai anjima.
Jungum sukayi a hanya babu Wanda yayi magana cikinsu har suka isa gida .
Suna shiga suka tarar da ummi da kawarta mama Rabi ,
Mama Rabi ce ta Mike ta taresu.
Kallonta Khadeeja tayi tace
Sai anjima.
Daga Kai kawai Fatima tayi  har takai kofar fita ummi ta tsayar da ita. Tace
Haba khadija ki tsaya mana  Don yanzu Tana  bukatar ki a Kusa.
Kama hannun ta ku shiga.
Suna shiga bedroom dinsu gado ta fada ta  kwanta.
Cikin sanyin jiki khadija ta fita bata dadeba ta dawo tareda Hindu.
Baki suka dinga  bata har suka samu tayi shiru.
Magani Hindu ta amso aka bata Tasha saboda ciwon da Kan ta yakeyi  ,barci ne ya dauketa.
Hindu ta Kalli Khadeeja tace
Wlh ukhty ta godewa Allah Ta sami miji nagari.
Ajiyar zuciya tayi tace
Eh sai dai banso rabuwarsu tazo ta haka ba.
Tabe baki Hindu tayi tace
Oho be dameni ba Nidai kawai Yar uwata tayi sa'ar miji.
Duka Khadeeja ta Kai mata, "haka dai suka dinga fira kan ta Farka.
Sai wajen Karfe biyar da Rabi sannan ta farka.
Mamaki Ya kamata ganin dakin cike da kaya.
Alwala ta daura ta tada sallar la'asar.
Tana idarwa mama Rabi ta shigo.
Bathroom ta shiga  ta hada mata ruwan wanka.
Hannunta tazo takama sai da ta Kaita toilet sannan ta kalleta tace
Kiyi wanka ina zuwa.
Tana fitowa ta Tarar da Khadeeja da Hindu  .
Khadija ta jata ta zaunar da ita Akan dressing  chair kwalliya ta mata ta gani ta fada.
Ita kanta data Kalli kanta a madubi tasan tayi kyau.
Mama Rabi ta shigo ta kalleta tace Masha Allah gaskiya khadija dole  na biyaki.
Dariya Khadeeja tayi tace
A'a  mama kada hindu taji haushi.
Dariya sukayi,itadai Fatima murmushi kawai tayi.
Hannunta Hindu ta rike yayinda khadija ta koma ta gefe jerawa sukayi har parlourn abbanta.
Baba  ne azaune sai ummi daga kasa kuma mal Abdul ne zaune ya sunkuyadda Kai.
Su Hindu dai suna zaunar da ita suka juya suka fice.
Tsayin minti uku kafin baba yayi gyaran murya khudubatil hajah yayi kafin ya Dora da cewa
Alhamdulillah yau Allah Ya nuna mini Ranar dana sauke hakkinki akaina Fatima, yanzu abinda Ya rage shine ki mini biyayya kibi mijinki shima kuma ki masa biyayya.,Kisa a  ranki bauta kika je bautar kuma ta Wanda ya halicceki bawai aure just for fashion ba a'alam bautace kuma sai an dage.
Kada ki Bari naji Wani Abu daya Saba tarbiyar dana baki.
AI tuni fuskarta ta Jike da hawaye tab babbar magana.
Aure without any sign ba shiri ya ilahi, Dagowa tayi a hankali ta Kalli mal Abdul Wanda kanshi ke kasa... Gabanta ya Cigaba da dukan Tara tara.
Abba Ya Cigaba da cewa Idan Kinyi hakan Kin Kare martabata kin Kare martabar gidan nan.
Kinji Allah Ya miki albarka.
Sannan Kai kuma kayi hakuri da ita kaine gaba da ita ka fita  hankali kafita hangen nesa. Duk abinda tayi ba daidai ba  ka tsawatar mata.
Ka kuma yi hakuri na maka katsalandan a cikin rayuwar ka sai dai ka sani komai kaddarar ubangiji ne ga amanar Fatima nan na baka.
Kara sunkuyadda Kai yayi yace
Na amsa na kuma gode Allah Ya kara arziki banida bakin da zan gode maka .
Murmushi abba yayi Ya Kalli ummi yace
Ya Matata ko kinada Wani Abin da zaki kara akai.
Itama dai sai da tayi khudubatil haja sannan tace
Duk Wani Abu da zan gaya babanki ya Riga da Ya gama magana.
Sai dai ki sani aure kikaje ba zama ba ba'a samun aljanna da zama.
Sannan nima na kara baka amanarta.
Tashi kuje abba Ya umurta.
A hankali ta Mike haka suma.....
Hindu da Khadeeja da mama Rabi suka tarar a kofar parlour din.
Har bakin get suka rakata.
Kankame ummi tayi Tana hawaye itama kanta ummi kasa daurewa tayi sai da ta zubar da hawaye Hindu ta rungumesu duka itama Tana Nata Hawayen.
Dakar abba Ya banbaresu rikeshi tayi Tana zubar da hawaye.
Hannun khadija ta rike Cikin matsanancin kuka tace
Na gode khadija Kinga yadda za'a raba ni da gida ba tareda na shirya ba?
Kuka khadija tasa ta rungumeta tace
Fatima kada ki damu wannan shine yakin matan da ake cewa kije na miki alkwrin tayaki da Addu'a. Abba Ya rike hannunta Ya riko na mal Abdul Ya hada yace Allah Ya kaiku Lafiya Ya Baku zaman Lafiya da yaya na gari.
Girgiza Kai kawai take Dan  ta Kasa cewa komai.
Mashin dinshi Ya hau ya tada ita kuma ta hau baya.
Suna tsaye suna daga mata hannu har suka Dena  ganinsu.
Comments pls and vote me wattpad@13deeja

Mata Tagari Where stories live. Discover now