🖋🖋🖋mata ta gari 🖋🖋🖋

321 25 0
                                    

📄📄📄story and written by
                                      Khadeeja.             Muhammad (one love) 📄📄📄

Dedicated to
       
       .        Fatima Hussein (bestie )

Yan bauchi na gaisheku kunayina ina yinku nima.... Wannan page din na sadaukar dashi ga  duk Wanda yake a bauchi thanks for your love.... Najida dadi sosai Allah Ya barmini ku Ameen 😘😘😘😘
Allah yasa daga zaben shi yafi alkhairi Ameen.

Hafsat Hausa novel(facebook) ina jin dadi comments dinku Allah Ya saka da alkhairi ....
Comments dinku na kara mini karfin guiwa......
007
Dif wajen yayi tsabar mamakin data basu... Duk da amfara yayyafi hakan be Hana ta Tsayawa,kallonshi tayi a dage sannan ta nuna shi da yatsa tace
Kai karamin Mara mutunci ne Dan rainin wayo tsabar cin mutunci a Gabana Kake yafi tata Kake zundena Dan Kai ga  Dan  Tasha Ko to Bari Kaji Idan ma Madigon da Kake tunani ne ai da uwarrrr..... 🙊🙊🙊 muka Fara wawa Wanda besan me yake ba tsabar Rashin gani a kyale..
Ai me okada da su jabir idanu kawai suka zuba mata...
Da kyar me okada Ya tattaro ragowar karfinsa yace
Ke ni zaki Mara?
Anmarekan ko zaka Rama ne?
Daga hannu yayi zai mareta daidai karsowarsa Wanda tun dazu yake kallon drama dinsu..
Duk da besan me ya hadasu ba. Da sauri Ya rike hannun sannan ya juya Ya kalleta yace
Jeki gida  baby...
Duk da haka sai da ta wulla masa Harara sannan ta juya ta tafi ..
Kan ta karasa gidan har Ta Fara jikewa Dan haka Tana shiga ta cire hijab din ta Shanya...
A bagaren Fatima kuwa koda ta koma gida hijab kawai ta cire ta nufi kitchen wannan yana daya daga Cikin Abin da yake aikin ta wato hada dinner ita kuma Hindu tayi lunch ummi keyin break fast sometimes kuma Wani daga cikinsu especially Fatimar kasancewar tafi Hindu zaman gida.
Har akayi kiran sallar magrib sannan ta fito..
Kallon su ameer da umar tayi sannan ta ce
Oya go and pray..
Da sauri suka wuce .
Daki ta shiga tayi alwala tayi sallah Anan ta zauna har akayi kiran ishai sai dai Yau azkar din gagararta yayi duniyar tunani ta fada...
Tabbas Ta kosa gobe tayi taje ta ga mal Abdul...
Ya ilahi wannan wane Kalar masifa ne...
Firarsu da maryam ne ta dinga dawo mata a hankali ta sulale kasa ta fashe da kuka... So na neman sata jin kunya lallai da alamu duk Ranar da maryam ta gane Tana son mal Abdul to amintarsu tazo karshe.
Lpy kike Fatima?
Ummi data shigo dakin ta Fada a hankali ta dago ta  ..
Fadawa jikin ta tayi ta Cigaba da kukanta..
Ummi kuwa bubbuga bayanta ta Fara yi a haka har ta Fara Ajiyar zuciya....
Sakin ta ummi tayi sannan tace
Kinyi sallah ne?
Girgiza mata Kai tayi alamar a, a
To tashi kiyi.
Mikewa kawai tayi ta tada kabbara... Itakuma ummin ta fita,tana idar da sallar Hindu ta shigo.. Kallon kallo suka Fara kafin Hindu ta Matso ta Kama hannunta tace
Mal Abdul ko...
Ji tayi gaba daya komai Nata ya Dena functioning...
Kafe ta da idanu tayi ..hindu ganin bazata Dena kallon Nata bane yasata cewa..
Haba ukhty addu'a Ya kamata ki yawaita.keda kike bani shawara yau kuma hakan ya gagareki?
Ki taso Muje muci abinci ummi na jiran mu..
Fitowarsu yasa ummi Dena cin abincin su ta zubawa idanu har suka karaso.. Hindu ta ja mata kujera ta zauna sannan ta Fara serving dinta..ganin bazasu ce komai ba ya sa ummi ta Kalli Hindu tace
Mamana meya sameta..
Gabanta ne ya fadi addu'a take Allah yasa kada hindun ta tonata,hindu ta kalleta tace
Ummi Wai dama fada sukayi da aunty maryam.. Ajiyar zuciya suka sauke a tare. Da sauri ummi ta kalleta saukar da kanta kasa tayi ummi cikeda zargi tace
Meya hadaku?
Amm dama dama Akan Wani zobe ne dana bata...
To kunfi Kusa dai...
Basu kara cewa komai ba har suka Gama cin abincin....
🍬🍬🍬🍬🍬           🍬🍬🍬🍬🍬🍬
Cikin Makarantace Wacce ta tsaru upstairs ne tanada Hawa uku
Gefen varender mal Abdul ne zaune tareda babban abokinsa mal sadik
Mal sadik ya Kalli abokinsa yace
Kuma a hakan kana ganin Tana sonka?
Eh mana.
Mal Abdul Ya bashi amsa sannan ya Dora da kanin babantane matsalar..
Alh Ibrahim ne ya doso wajensu
Cikeda mutuntawa ya basu hannu sukayi musabaha..
Kallon mal Abdul yayi sannan yace
Mal neman ka nake tun dazu karatun jiya za'a taimaka a karasa mini..
Murmushi yayi sannan yace
To alh kaga ga mal sadik nan shima Ya tayani...
A haka suka Gama karatun sannan Kowa Ya tashi ya Kama gabansa..

Vote for me on my wattpad 13deeja

Mata Tagari Where stories live. Discover now