Fadima bintu

401 22 1
                                    

Zahra
Page 2_3
Jiki bakwari haka na isa shagon, sallama namusu kamar yadda mama tace nayi,
Sannan na
mika masa kudin cikin sanyin murya nace "aban kati MTM(Hhhhh)" kudin ya karba ya shiga shagon don dauko min katin

Ina nan tsaye ina kalle kalle har ya fito yaana cewa "gashi zahran john" take na hade rai domin babu abinda na tsana kamar a hada ni da wannan kafirin(su john makwabtan mu ne amma Christians ne kuma shi john din irin marassa lfyn nan ne Wanda suna tafiya suna karkarwa suna zubda yawu, wai shine yake cewa yana sona, kuma duk inda ya ganni sai yayi tabina yanaa cemin "za...ra.. ....n..a... " nikuwa ji na ke kamar zan mutu Dan bakin ciki , shiyasa ina ganin sa zanfara gudu )

Karbar katin nayi ina harararsa najuya zan tafi,ai kuwa ina juyawa na hango john yana tafe yana karkarwa yana ta sauri domin yazo gurina
nikuwa ina ganin haka na falfala da wani uban gudu sai gida
ina isa ko
takan mama da takemin magana banbiba na shige daki na banko kofa , da gudu na nufi kan katifata na janyo bargo na rufe duk jikina( Allah sarki johnduk kiyayyar ce haka)

cikin tashin hankali Mama take buga kofar dakin kamar zata ballah kofar tana cewa na bude itama ta shigo, ita duk a zaton ta wani mummunan abun ne ya biyo ni(Hhh) tashi nayi jikina a sanyaye na bude kofar aikuwa ina budewa ta danno ciki tana shigowa ta danna sakata tana haki

, shiru mukayi dukan mu, kowada abinda yake sakawa acikin ransa, nikuwa ba komai nake sakawa ba sai irin dukan da mama zata min idan har tasan mai ya sani wannan gudun.

Motsi mukaji daga waje aikuwa kamar dama mama jira take kawai sai naga taruga da gudu tayi bandaki ta danna key,

tsayawa nayi nama rasa ina zan dosa ' shin waje zan fita na duba waye ne ko kuma gun mama data shige bandaki zan nufa?? , ganin tunani ba fishshe ni zaiyiba sai na nufi kofar dakin na budeta na fita don ganin Waye.

ZAHRAWhere stories live. Discover now