Teemah

130 20 2
                                    

ZAHRA
Gorgeous writers forum
G.W.F
Home of gorgeous, intelligent and experts writers, we are the best among the rest

Written
By
Fateema Adamu Gamawa
In dedication to
Bestee Hauwwii
My blood sis Maryam Adamu(Dadarest)
Balqees
Hanifa
My one and only Broo Umar Adamu Gamawa

Page 9-10

Bayan tafiyar zahra makarantar islamiyya da wasu awanni domin har mama ta daura abincin rana wannan Mummunan abi yafaru dasu haka suna ji suna gani suka bar gidan su da diyar su suka shiga uwa duniya,
Allah kashiga tsakanin mu da azzalumai

Back to the story
Cigaban labarin

Haka na wuni ina kuka sunyi rarrashin duniyar nan amma na ki yin shiru ina tacewa a kaini garinmu ai Mummy ta gayamin Mamana sunyi tafiya ne kuma sun kusa dawowa, haka nai tayi kasancewar bansaba da kowaba
dubu biyun da mommy ta bani kuwa suna hannuna na rike su gam

Da safe kuwa dakyar nayi breakfast sannan matar baffa na tamin wanka tasamin kayan diyarta tace naje waje nayi wasa da yara,
can muna wasa sai na tambayi daya daga cikin yara a ina a ke shiga mota sai wata yarinya tace mun natashi ta rakani haka muka kama hanya muka tafi

Da muka isa
suka tambayeni ina zani sai nace musu Azare suka nuna min motar da zanshiga sannan suka fada min kudin mota nabiya a cikin kudin da mommy ta bani sannan nashiga mota na zauna ko takan Wanda ta rakoni banbima
bayan mota ta cika muka kama hanyar Azare
(Toh sai muce Allah ya kiyaye hanya zahra).
Bayan mun isa kuwa direct unguwarmu na wuce, sai da nafara shiga gidan mu kamar yadda na barshi a haka na sameshi , haka najuya na fita na shiga gidan su John

ZAHRAWhere stories live. Discover now