Fatima

138 12 0
                                    

ZAHRA

Gorgeous Writers Association
          G. W. A
Home of gorgeous, intelligent and expert writers, we are the best among the rest.

Written by Fateema Adamu Gamawa

This page is for u Amarya Antiyo Allah ya Albarkaci Auranku
Page 11-12

Babu yanda su Daddy basuyi ba akan Zahra tazauna anan amma fir yan uwan
Su Abba sunki domin su a tunaninsu  babu yanda za'ayi su barta a gidan kafirai ai sai ta koyi dabi:'ar su haka suka dauketa tana kuka tana ihu amma babu Wanda ya saurareta ,
aikuwa da suka kuma haka akayi akayi taci abinci amma fir taki sai kuka(ohh poor Zahra)

Cikin kwana biyu ta rame tayi fiyau da ita tsabar kuka da damuwa abinci kuwa dakyar take shan tea
Bangaren Su Abba kuwa
Bayan sun fita gida tasha suka nufi suka shiga motar Lagos
Kwana sukai a hanya sai da yamma likis suka isa
Haka suka kwana suna tangaririya akan titi dakyar suka samu wata  gada(bridge) suka kwanta a kasanta kasancewar babu ruwa a gurin

Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya kullum Abba da Ya khali su suke fita suyi daku ko suyi Wani aikin karfi sai su siya musu abinci idan kudin yayi saura sai su sayi wani dan abin anfani irin su bargo, gidan sauro dadai sauransu,

Wata Rana Mama tana zaune ita da lil fix tana dinke gidan sauransu da ya yage wasu mutane suka zo daga alamu kuma  masu gyaran hanya ne
wani kakkauran mutumi ne yafara yin magana cikin wata irin kakkausar murya yace "ke dallah malama tashi anan, muna fukar Allah ta'ala, karuwar banza karuwar wofi,Anyi kwashe ko ankuma debo cuta ga yaro to chalama Allah shi kara,kuma kiyi maxa kibar nan wurin tun kafin nayi kasa kasa dake"yafada ba ko full stop balle comma
Wani siririn mutum ne daga cikinsu mai kama da zabiya yakara dacewa "Barta Mudi wlh irin su ne zaka gansu abin tausayi amma lumbu lumbu ne wutar kaikayi kana taba su ka kune "
Allah sarki Mama hawayene yayi mata sharkab a fuska wai yau itace ake kira da karuwa, inama tasan a garin dasuke data kuma gun diyarta da yan uwanta diyar tata data manta sunanta uhum duniya kenan

Tsawar da mutimin yadaka mata ce yadawo da ita daga duniyar tunanin data lula kayanta suka fara wawatsar musu suna tura su kamar wasu shara
Wani tashin Hankalin shine Mama bata San Inda zata fara neman su Abba bama

Babu irin rukon da bata musu ba akan su barta su Abba su dawo suna dawowa zasu tafi,amma ina babu Wanda ya saurareta harma suna kokarin dukansu
Haka sukafito suna tafiya suna kuka ta rike hanun lil fix kam,
Har yamma basu sami mafaka ba ga gajiya ga yunwa, gefen wani gurin saida abinci d
Suka samu suka zauna lil fix kuwa yayi kukan harya gaji, wata mata ce sukaga ta fito wurin zatayi wanke wanke ga abinci kala kala acikin kwanuka,Mama CE tazo ta tsugunna a gaban Matar tana cewa "Baiwar Allah ki dubi Allah ki bamu sauran abincin nan Dan Allah wallhi yaro ne da ni gashi sai kuka yake min"Shiru matar tayi sannan daga bisa ni tace "to ki dawo dashi inuwa sai kuci " abincin ta hardada musu sannan tamika musu hannu baka hannu kwarya haka suke ci abincin
Bayan sunci abinci ne ta basu ruwa suka sha
Tadi suka farayi da matar har tagaya mata sunanta saude kuma daga garin kabo take itama Neman kudine ya kawota nan lagos Mama ta fada mata dan tarihinta Wanda zata iya tunawa nan take saude ta fahimci abinda yake faruwa addu'a tamusu a zuciyarta Allah ya kawo musu mafita

Nantake suka saba har takaita gurin hajiyar su wata bayerabiya mai kirki sosai nan saude ta mata bayanin abinda ta fahimta game da Su Mama
Allah sarki Hajiyar tuwo harda kukan ta jin wannan labarin
Nan take taji Mama ta kwanta mata a rai
Kuma ta dauki alkwarin taimaka musu
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

Zahra ce sanye da wata bakar riga irin mai tsukewa ta sama ta kasa kuwa tabaje sai hajijiya take tana dariya itada sauran yara,
Ji kake timmmm tafadi kasa, aikuwa take sauran yaran suka fara yimata dariya wasu hard a rike ciki, ita kuwa kamar ta mutu dan bakin ciki, wata bulala ta hango aikuwa tayi kwafa ta tafi tadauko ta tafara bin yaran tana dukan su, kowa tasamu kawai duka take kai masa ko gani sosai batayi tsabar masifa taci ranta,
Jitayi an rike bulalar
dagowa tayi zatayi masifa kawai sai taga wani saurayi kyakykyaawa ajin farko fari sol ga hanci, sajensa kuwa baki kirin a kwance sanye da shadda fara kal Wanda takara haska shi kyawun sa ya kara banyana,gashi mai dan kiba kuma dogo, dayan hanunsa yana cikin aljihun wandon sa dayan kuwa ya rike bulala lar, murmushi yayi wanda ya kara masa mugun kyau said dimples nashi suka lotsa itama murmushin tayi tareda taba NATA dimples din
"Cuty kidai na fada, kinga kyawawa kamar ki bai makamata suna fada ba"
Wayyooo Allah dadi wani sanyi taji ya ratsa ta tundaga tsakiyar kanta har kafarta
Bata san sanda tace"balarabe dagaske ni ina da kyau kuma kana sona ko,to nima ina SONKA..................

Hey good peoples ya kwana biyu wlh   biking sister na akeyi shiyasa bakwajina kwana biyu
Ga exam wlh abu biyu ne suka hadu min

Alots Of love
Fateegamawah

ZAHRAWhere stories live. Discover now