Bintoto

145 16 2
                                    

ZAHRA
GORGEOUS WRITERS FORUM
      G W A

Written by Fateema Adamu Gamawa

Wannan page din nakine Aishat yar Niger Ta Zahra fans sosai comments naki yakemin dadi

Page 13-14

Murmushinsa ya fadada wanda ya kara haskaka kyayunsa tare da sakin bulalar ya
kora mata manyan idano wansa farare kal sai Dan dokon bakin shima yaci sosai
Kunkuni tafarayi tana bubbuga kafa tana cewa " Ni kam Allah kadena kallona kodan kaga kafini kyau"sai kuma tafara kukan shagwaba"uhun uhun Allah ni kadaina kaga banaso" shi kuwa hakan datakeyi bakarmin kyau yamasa wannan nema yasa yakara shagala a kallonta, domin harya hangota a matsayin matarsa( tab lallaima Zahran ) fuska ta bata tareda juyawa zata tafi

  dasauri haryana tuntube yashagabanta tareda kama kunnensa yana cewa " kiyi hakuri mana mai kyau nifa kawai gani nayi kinkarayin kyau dakina magana  ,ammah kiyi hakuri kinji" gyada kai tayi tareda cewa "toh kana sona ko Balarabe"dariya yayi kafin yace "A'a,nikam bana sonki"yakarasa yana dariya, idonta ne yayi raurau tana shirin yin kuka "Balarabe bani da kyau ko shiyasa baka sona ko,......."sai  hawaye sharrr" kaima zaka tafi kabarni kamar yadda su Mama suka barni ko" sai kuma taci gaba da kukanta harda sheshsheka
Rasa ma yanda zaiyi yayi domin shi harga Allah baisan abin zai sata kuka ba 

Dokawa yayi a daidai tsayenta sannan yace "Kiyi hakuri beautiful wallahi ni wasa nake miki inasonki  sosai da sosai fa kuma bazantaba barinki ba har a bada kinji"
A take taji wani sanyi ya shiga cikin ranta

Kiran sallah akafara yi wannan ne yasa shi yace mata "Toh mai kyauna zanje nayi sallah kema kije kiyi kinji sai kimana addu'a Allah yasa  muyi aure"
Da sauri tarufe fuskarta tana cewa "nifa kabari kunya nakeji " murmushi yayi,nan take yaji takara shiga ransa, Addu'a yake Allah ya bashi ita a matsayin mata duk da irin kananan shekarun ta dagowa yayi yace "Insonki Mai kyau , I Love u so very much"ya fada cikin turancinsa irin na  Americans
Sai kuma abin yabata kunya kawai ta walwala da wani uban gudu sai da taje kofar gida sannan ta tsaya (sai ba Zahra)
Ta jiyo , shi ko tsaye yayi yana kallonta yana murmushi ga dimples dinsa son kara fitowa sosai ganin haka sai  itama ta taba nata dimples din tayi murmushi
Daga masa hannu tayi sannan tayi sauri tashige gida tana dariya

Alwala tayi tana yi tana murmushi ita kadai Wanda tunda aka dawo da bata tabayiba har sai da Innah laure ta tambayeta miya faru take ta murmushi
Tace babu komai nan kuwa bata san naciki na ciki ba

Sallah tazo tayi, harta idar saikuma ta tuna cewa malamin a makarantar islamiyyar su fa yace idan Mutum yana so Allah ya amsa masa Addu'arsa toyayi addu'a cikin sujjada, aikuwa take ta koma tayi sujjada tafara addu'a kamar haka
"Ya Allah ....." Sai kuma tayi shiru " Allah kasa nazama matar ,,,,,,,,,,"sai kuma takarayin shiru tana rufe fuskarta da hijabinta  saikuma tafara cewa"Haba Zahra kifada mana kidaina jin kunya(hhhhhhh)" "Toh ai ni kunya nakeji (I can't stop laughing wollah)  duk ita kadai  sai kuma tabata rai tafara cewa "Ya Allah kasa nazama ,,,,,uhum matar wannan ..........wannan dinnan ba,," sai kuma tayi murmushi kafin taci gaba da cewa" yawwa wannan Balaraben nan uhumm" sai kuma tasake rufe fuskarta "Ameen kuma Ya Allah kasa su Mamana, Abbana, Ya khalii da kuma lil fix dina sudawo su daukeni mutafi, kuma Allah kasa Wanda sukasa su Mama suka tafi su kone"

Ba'a ko ina Zahra taji wannan zancen ba sai a gurin su Innah laure ranar tana bawa wata munafukar kawarta labari (NOTE:bai kamata ana magana a gaban yaraba domin ana ganin kamar basu da wayo toh wallahi irin wadannan haddace magana suke yi so be careful)

Washegari da safe bayan ta karya tayi wanka harda kwalliya ta ranbada saboda Balarabenta(imagine) 
Fitowa tayi ta tsaya a wurin da suka hadu jiya ammah babu shi babu alamarsa har tagaji taje ta zauna a wani dan dakali a gefe

Kusan awarta biyu a wurin amma shiru ko mai kama dashi bata gani ba gashi ita ko sunansa bata saniba bare ta tambaya ammah barata gwada tambayar mutanen unguwar ko sun sanshi

Haka tayi tambayar mutane amma kowa ta tambaya sai yace mata bai sanshiba wasu kowa dariyama suke mata
Gefe takuma ta zauna tana ta tunani yanzufa shike nan Balarabenta ma ya barta kenan kamar yadda su Mama suka barta
Kuka ta farayi sosai harda majina tana cewa "Dan Allah balarabe na kadawo........

Allah sarki zahran Mama takuma zahran Balarabe
Ina team din John , yanzu kam munsamu wani iyyyyyyyyye rawa rawa rawa rawa

Dade datakke da sai kaga mai kudin garinmu wai baida waya yaturo  Ashe da tafi dadi  yanzu kudin yafi dadi
Rawa rawa rawa rawa rawa
( a song by nazir m Ahmad)

Love u Sweetie's
Fateegamawah

ZAHRAWhere stories live. Discover now