Zahara'u

293 17 1
                                    

ZAHRA
Fateema Adamu Gamawa
GORGEOUS WRITERS FORUM
G.WF
Home of gorgeous,intelligent and expert writers,We are the best among the rest
Page3-4

Cigaban labarin

Cikin barci nake jin mama tana tashi na nayi sallah
A hankali na bude ido na Wanda yayimin dauyi saboda kukan dana sha jiya , tashi nayi na zauna tareda yin mika sannan nayi addu'r tashi daga bacci, duk jikina ciwo yake min ga idona yayimin nauyi sakamakon dukan da ya khalii yamin jiya
wai na tsoratar masa da Mama (Ku jimin mutum saika ce mamansa ce shikadai, kato da shi .uhum babu abinda yake bani haushi sai Idan ya khalii yana zuba soyayyah dashi da Anty Rukayya har wani langwabar da kai yakeyi kuma yana wani kashe murya yanda kasan shine budurwar mtwst aikin banza kare da gudun layya) haka jiya yakama ni yayi ta tikata kamar kayan wanki har saida Maman su John ta za gayo ta karbe ni (akwai xumuci mai karfi a tsakinin gidan mu dakuma gidan su John, lil fix kam wata rana har kwana yakeyi a gidan amma fa banda ni domin ni tunda nayi wayo baifi sau biyu na taba Shiga gidan ba ko mama xataje gidan tofa bana binta sai dai nayi zama na a gida taje ta da dawo)

Tashi nayi na nufi banda ki nayi wanka sannan na dauro alwala na fito na saka uniform dina kasancewar yau Friday
Sannan nayi sallah bayan na idar ne na zauna nayi addu'o'i na sannan na tashi na dauki jaka ta na nufi tsakar gida.
Ban samu kuwa a tsakar gidan ba kasancewar da sassafe ne
Kitchen na nufa nadauko breakfast dina na fara ci
Ina nan zaune ina cin abinci na har Mama ta fito ta daurawa lil fix ruwan dumi domin yayi wanka kasancewar yana da pneumonia, har ruwan yayi dumi, yayi wanka ya shirya duk ina zaune ina cin abincina a hankali yanda kasan bazanciba
Bayan na kamallane naje ni dakin Abban mu na gaishe shi sannan na karbi kudin break dina nawuce makaranta
akalla nayi wurin minti talatin ina tafiya , tafiyar da bazata fi minti goma zuwa sha biyar ba
A lokacin Dana isa makaranta har an fara taran latti nikuwa babu abunda na tsana sama da a taba lafiyar jikana

Zagayawa na yi tabayan makaranatar kasancewar akwai wata Katanga data fadi, ta wurin na wuce nabi tabayan classes sannan na zagaayo zan shiga ajinmu aikuwa ina zuwa kofar class din mu naga Mallam Rabe tsaye abakin ajinmu da wata sharbebiyar dorina mai baki biyu,kallona yayi sannan yace "kingama zagayen na ki?"
Wai ashe tun lokacin dana zagaya ta bayan classes din nan yana kallo na shine yazo kofar ajinmu wai don ya jirani .
"Kawo hanunki masa "muryarsa ta daki dodan kunne na a hankali na mika masa hannu na ya zazzabga min bulalu na guda shida sannan ya kada kansa ya tafi ya barni anan ina zubda kwallah na Dade a wurin ina kuka daga bisani na taka a hankali na shiga aji

Karfe 12:00 dai dai aka tashemu a makaranta amma ni sai karfe daya na isa gida, saboda yadda nake tafiya a hankali
Kuma ina tafiya ina yan wakokina

A kofar gida na tarradda ya khalii dashi da Baban John suna magana kasa kasa ga damuwa shimfide fal a fuskarsu amma ni ban ma kula ba, gaishe su kawai nayi na wuce
A tsakar gida na samu mama tana zaune a akan tabarma ta rafka uban ta gumi ga idonta yayi ja alamar tayi kuka kenan gefenta kuwa lil fix ne zaune yana wasa
Dagowa tayi ta kalleni sannan tace " zahrana har kin dawo toh maxa kije ki cire uniform dinki kiyi wanka kiyi sallah ,kizo kici abinci kinji yar Mama" take na fara washe baki ina murmushi nace "toh Mamana" ashe ni bansani ba Mama tayi hakane kawai don ta kawar min da tunani a zuciyata

Bayan na kammala duk abinda Mama tace nayi, sai nima na zo na zauna kusa da ita muka fara wasa da kanina,
Ya khalii ne yashigo jikinsa a sanyaye kamar maral lafiya ya zauna a kusa damu Mamace naji tana cemasa "khalifa ya dai ansamu sun hakura"bantaba jin mama ta kira sunan ya khalii ba sai yau toh kuwa komiye ya ke faruwa tufa bakaramin abubane
Sharewa nayi muka cigaba da wasan mu sukuma suka shige daki suka ci gaba da maganar su sai can naga ya khalii ya fito yana kukarin goge kwallar data zubumasa

Har magariba muna nan zaune muna wasanmu
Mama kuwa bata fito ba
Ganin duhu ya fara shiga ne yasa nacewa lil fix ya tashi mutafi gun Mama
A kwance muka sameta tana kuka Ammah tana ganin mu tayi sauri ta goge hawayen fuskar ta tana kallan mu tana mana murmushin yake tace "Zahra kunyi sallah kuwa"girgiza mata kai nayi alamar A'a
"Toh maza kuje kuyi alwala kuyi sallah"
Ina kokarin cemata ba haske aka kawo wutar nepa sai a sannan ne naga yadda fuskar mama ta kumbura ga idanuwanta sunyi jawur kamar gauta ganin irin kallon danake matane yasa tayi saurin cewa "kuje kuyi sallar kunga ankawo wuta ma"
Juyawa mukayi muka fita daga dakin mukaje mukai alwala
toh anan ne fa mukafara gardamar waye ne liman shiyana cewa ai ko a masallaci namiji ne yake jan sallah nikuma ina cewa A'a ai kawai babbane yake jan sallah haka mukai ta chachar baki muna ture ture Dakar ya yarda cewa idan zamuyi sallar isha to shi zai jamu
Gaba na shiga shiko ya tsaya a baya sannan na jamu sallar(yarinta things)
Bayan mun idar sai muka zauna muka fara labarai
can lil fix yace min wai shifa yunwa yake jii cema sa nayi tashi muje gun Mama mufada mata
A zaune muka sameta akan sallaya sai ya khalii dake zaune a bakin gado yana ce mata"Wlh Mama munyi munyi dashi ya bar wannan shari'ar amma yaki yanzu ma dakar Baban su John ya lallabashi yadawo in yaso gobe a karasa kuma wlh Mama idan kinji abinda mutanen nan suke fada hmmmm.,......."sai kuma yayi shiru Mama ce takalle shi idonta cike tab da kwalla tace "khaleefa misuka ce " sunkuyar da Kansa kasa yayi kasa sannan yace "wai fa cewa suka yi wai idan dai harsuna raye zaman garin nan ma sai ya gagare shi, kuma wai ......."sai ya kuma yin shiru cike da fargaba da tsoro Mama take cewa "kuma wai mi kafadamin man khalifa"
Kallanta yayi nadan lokaci cikin karayar zuciya da jimami yace "cewa sukai idan dai harsuna raye daga shi har iyalansa babu mai kara kwana a cikin garin nan.,,,,,,,ni Mama tsoro na daya karfa sumana kurciya"ya kara sa maganar yana share kwllar data zubo masa
Mamace ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ganin haka yasa nima na fara kukan
haka mukai tayin kukan mu babu mai lallashin wani
Sautin kukan mu ne ya fito da Abbanmu daka dakinsa
Tsayawa yayi abakin kofa ganin yanda muke kuka daga bisani kuma sai yayi murmushi sannan ya shigo dakin ina ganinsa na nufi wurinsa ina kuka inacewa "Abba kace Mama ta daina kuka "hannuna ya rike sannan ya share min hawayen fuskana yace "Zahra kiyi shiru kinji Mama ma zatayi shiru itama"yafada yana murmushi
Hafix ne yace "Abba yunwa muke ji" kama hannun mu yayi muka nufi kitchen ya hada mana complex yabamu muna sha yana mana tadi muna dariya
Bayan mun gama muka kuma daki ya dauko mana sleeping dress dinmu mukasa sannan ya kwantar damu yana mana tadi har mukai bacci.
Bankara sanin miyake faruwa ba sai da safe da Mama tazo ta tashe ni nashirya na tafi islamiyya kasan cewar lil fix yatashi baya jin dadi
Karfe Biyu aka tashemu tafiya nake ina layi saboda yunwàr dana keji, da sallama ta nashi gida amma shiru babu wanda ya amsa, kara sallama nayi nan ma shiru dakin mu nashiga wai ko suna ciki amma babu kowa aciki, dakin mama na duba still babu kowa haka nayi ta dube dube amma babu ko alamar su zama nayi a tsakar gidan ina jiran dawowarsu amma har karfe uku babu Wanda ya leko gidan ga yunwa duk ta galabaita ni, kuka nayi tayi har na gaji nayi bacci

A hankali na fara bude idona maimakon na ganni a tsakar gida sai na ganni a kan wani gado mai uban laushi dube dube nafarayi amma dakin babu kowa
ina nan zaune ina kalle kalle naga an turu kofar dakin an shigo Maman su John ce ta shigo sai a sannan nasan cewa a gidan su John nake xuwa tayi ta zauna a gefe na ta ruko hannu na cikin kulawa tace "daughter kin tashi sannu kinji" tamabs yanta nayi ina Mamana sai kawai naga tafara hawaye....

............................................................................
Waishin ina su Maman zahra???
Ya zahra zatayi yau gata a gidan su Aljani John?????
Ku biyo
Fateema Adamu Gamawa domin jin yazata kaya
VOTE, COMMENTS & SHARE THROUGH
WATTPAD@fateemaAdamu
This page is directly dedicated to Aunty Wahila Maman Al Ameen and Addana Maman zaid
Loves u fanss

ZAHRADonde viven las historias. Descúbrelo ahora