Fatsima😂

148 13 1
                                    

ZAHRA

GORGEOUS WRITERS FORUM
G.W.F
Home of gorgeous, intelligent and experts writers, we are the best among the rest

Written by Fateema Adamu Gamawa

Kuyi hakuri fans nasan irin yanda mutum yake ji idan yana karanta novel kuma aka tsaya, ina mai Baku hakuri sosai Zahra na gaishe ku kuma tana godiya
Wlh exam nakeyi ga course din nawa sai a slow kuyi hakuri fateegamawah loves u a lot

Page 15-16

Har akayi kiran sallahr Azhur Zahra tana wurin a zaune idanuwanta kuwa sun kada sunyi ja tsabar kuka, domin tayi kukan harta gaji tadawo kukan zuci
ganin har mutane sunfara Shiga masallacine yasa tamike ta nufi cikin gida inda taje tasamu Innah Laure tana ta ciki yarta(nemanta)
Inna Laure: "Zahra daga ina kike tun dazu inata nemanki,,, subhanallahi miyasamu idan ki diyata ko wani abune yashiga miki idon " tafada tana duba idon Zahra (bata san Zahra kam tafa kogin so bane hhhhh)
Shiru tayi tareda kallon kasa ganin tayi shiru ne yasa Innah Laure tazaci tana kukan ne a kan su Mamanta

Abinci taci tare da yin sallah sannn ta je ta zauna a kusa da Innah laure, can suna zaune innah Laure ta fara gangadi sai bacci
Farinciki fal ranta tamike ta dauki takalminta a hannu wai don kar Inna Laure ta ji takun tafiyarta
Kofar gida tafita aikuwa tana fitowa ta hango shi zaune akan wannan dakalin da ta zauna dazu
Rike yake da wayarsa kirar iPhone 7+
Sanye yake da wani farin yadi daga gani kuma yaji kudi,gashin kansa kwance luf luf irin na larabawa
A hankali take tafiya tana zuwa gurin da yake zaune fuskarta cike da murmushin jin dadi domin ganinsa ma datayi bakaramin dadi yamata ba
Haka ta lallaba ta je ta bayansa tare da leka fuskarsa sannan tace" balarabeeee "
Aikuwa da gudu ya tashi yana kokarin sa gudu sai yaji ta bayansa ana dariya saifa a sannan ne yagane mutum ne ya tsorata shi
Juyawa yayi domin yin masifa domin ya kudurta a ransa cewar ko waye wannan tofa mai rabasu sai Allah domin haryayi imaging irin naushin da zaima kowa ye

Ga mamakinsa wannan Mai kyau ya gani a tsaye tana mishi dariya sororo yayi yana kallonta wani kyau yaga tayi na musamman datake dariyar sai yaji inama karta daina domin shi ko shekara zaiyi yana kallonta a haka bazai gajiba
Itakuwa dakyar tasamu ta tsayar da dariyar domin har cikinta yafara ciwo

Zatai magana sai kuma taga shima zaiyi magana hakan ne yasata tayi shiru
Shima ganin zatayi magana sai yafasa tashi maganar yana jira tayi maganarta
Duk shiru sukayi kowa na jiran dan uwansa yayi magana
Ganin bashi da niyyar magana ne yasata cewa "Balarabe shine dazu kaki zuwa nayi tane manka narasa kuma idan na tambayi mutane sai suna min dariya suna cewa su basu san wani balarabe ba "Tafada cike da shagwaba
Murmushinsa mai tsada yayi mata Wanda yayi sanadiyyar wargaza tunanin ta na dan lokaci sannan ta dawo saiti(uhum ni fadima)
Cewa yayi" baby mai kyau ayiwa balarabe hakuri ya danje wani wuri ne da zun"
Fuska ta hade tace"baza ayinba sai kamin frog jump" ido ya zaro waje tareda fadin"baby frog jump fa, haba Dan Allah ayimin rangwame mana " yakarasa yana karkata kai gefe
Ita dariya ma yabata cewa tayi"toh kayi up and down " kai ya magale a kafada alamar A'a
"Toh kayi uhummmm"sai kuma tayi shiru tana tunani can tace" toh kafada min sunan ka"
"Sunana ABUBAKAR SADDIQ AHMAD DAMDAM" yafada sannan yace "kifa mi sunnan ki"
"Uhun nifa sunana maidadi ne fa kasan miye, FATEEMA M INUWA ZAKI amma Mama na tana cemin Zahra ai yayi maka dadi ko" " sosai ma kinga yazama Zahran sadiq ko"
Rufe fuskarta tayi da gefen hijabinta sannan ta gyada kai
Sunkuyawa yayi daidai tsayinta sannan yace "Baby Zahra zanje gida zamuje unguwa da dad dina Ammah bazan tafi ba sai kince kina sona" kara boye fuskarta tayi sannan tace " nifa kunyarka nakeji"
Tafada a shagwabe shikuwa cewa yayi
" haba Baby zàhrà please ko kina so nayi kukà" girgizà kanta tayi a hankali
"Toh tunda bakiso kice kina sona"
"Ka rufe idan ka toh, kuma ina fada zan tafi "
"Toh na yarda"
Siket din jikinta ta tattare tayi ready gudu sannan tace "Inasonka balàrabeeeee" sai gudu ffuuuuuuuuuuuuuuuu

Ina labarin su john me

Tun bayan tafiyar zahra john yashiga cikin wani yana yi ko abinci dakyar yake ci sai mummy tayi kamar zata masa kuka kafin yaci, ya rame duk yayi wani iri bangaren jinyarsa kuwa saima abinda ya kara gaba
Wannan ne yakara daga hankalin iyayensa musamman ma mahaifiyarsa, domin kullum tana kan hanyar zuwa gurin masu magani, church kuwa babu irin wanda basuje ba

Kwatsam ranar sai wani labari yazo musu cewa akwai wani gurin mai magani kuma idan dai aka kai shi tufa kamar ma ya warke
***************************************

Dan dan dan dan tofa shin wai John zai samu lafiya?
Shin kuma yaya zata kaya tsakanin Zahra da sadiq??
Ku biyo ni domin jin cigaban labarin

VOTE, COMMENTS AND SHARE THROUGH
WATTPAD@fateemaAdamu

Love uu

ZAHRAWhere stories live. Discover now