Bintu😇

143 18 1
                                    

ZAHRA
WRITTEN by Fateema Adamu Gamawa
GORGEOUS WRITERS FORUM
         G.W.F
Home of gorgeous, intelligent and expert writers,we are the best among the rest

   Page 5-6

Sauri tayi ta share hawayen ta sannan ta kakalo murmushin dole tace "don't worry my child, Maman ki tana nan kawai sun danyi tafiya ne amma sun kusa dawowa"
Mamaki ne ya kamani ina su Mama suka tafi kuma suka barni, hannu na ta rike ta kaini bakin toilet din dakin tace "ki shiga kiyi wanka ki yi alwala sai kizo kiyi sallah "
Shiga toilet din  nayi wow it looks amazing ga wani kamshi dayake tashi
wanka nayi na maida uniform din jikana sanan nayi alwala na fito, carpet naga ta shimfida min a tsakar dakin wurin na nufa aikuwa ina dora kafata akan carpet din naji kafata ta lume ciki, murmushi nayi na cigaba da tsalle akan carpet din ina dariya har ma na manta cewa sallah fa zanyi,
Mummy ce ta shigo dakin (sunan da yaranta suke kiranta dashi kenan) ganin
ina wasa ne yasaka ta dakata abakin kofa tana kallona tana murmushin jindadi
Kasan cewar bata taba haihuwar ya mace dama kuma yaranta biyu ne daga John sai Boma
Shiyasa take sona domin ko kasuwa taje idan taga wani abin yara  tofa zata siyamin  dago idona nayi kawai sai na ganta a tsaye tana murmushi, murmushin nima na mata sannan na daidai ta tsuyuwata natada sallah karasa shigowa dakin tayi ta zauna aba kin gado tana jira na
Har na idar da sallah na nade mata carpet din sai tace min nazo muje naci abinci da sauri na gyada mata kai saboda daman wata uwar yunwa nake ji
Hanuna ta kama muka fita Boma muka samu a parlour yana kallon football kollona yayi cike da tsokana sannan yace "zahran John yau hiran ce har gida" sai fa alokacin ma na tuna dacewa john fa yana gidan
Harararsa nayi tareda murguda masa dan karamin bakina
Mummy ce ta ja hannuna ta zaunar dani a daya daga cikin kujerun dake parlour sanann ta nufi downstairs don dauko min abinci
Muna nan zaune ni da Boma shi yana kallonsa nikuwa na sunkuyar da kaina kasa ina bawa cikina hakuri (lol)
Taku naji a stairs alamar ana hawowa kenan murmushi nayi domin na zata Mummy ce
"Zazzahraa"naji an fada da karfi juyawa nayi don gani waye John na gani tsaye yana ta karkarwa yana murmushi
Ihuuu na fasa tareda rufe ido da karfi ina kiran Mamana jinai yana cewa "zahra kiyi shiru, kiyi hakuri kinji zan tafi" yafada kamar zaiyi kuka, juyawa yayi yana tafiya yana karkarwa yana share hawaye,,,,, nikuwa kukana naci gaba dayi ina kiran Mamana
Boma ne naga ya tashi ya bishi, Mummy su nagani a tsaye tana kallona Ashe duk abinda nayi tana kallona zuwa tayi ta zauna a kusa dani tana rarrashina tana bani hakuri cemata nayi ta kaini gun Mama ni tsoron John Nakeyi
Murmushi tamin sannan tace "toh zankaiki Ammah sai kinyi shiru"
Goge min hawayen fuskata tayi sannan ta fara bani abincin a baki nikuwa ina karba ina ci harna koshi.. Cartoon ta kunna min nikuwa na gyara zama na fara kallo na

A can kuwa mangaren John yana isa dakinsu ya zauna ya cigaba da kukan sa.
Boma ne ya shigo  yafara lallashin sa ammah yanda kasan ma zigashi yake yi ,yana kukan yana maganganu" zaraa I love u I really do love"sai kuma yacigaba da kukansa
Boma kam tsayawa yayi yana kallonsa yana jin tausayin Dan uwan nasa domin yasan irin son dayakewa Zahra,  ita kuwa idan dai suka hàdu sai tadinga ihu tana gudu kamar taga wani dodo shi kuwa ranar kwana zaiyi yana kuka yana cewa su mummy su kaishi ko ina ne yasamu sauki domin zahra ta so shi
Fita yayi a dakin domin yaje yakira mum yafada mata halin da ake ciki a bakin kofa suka hadu kallonsa tayi tace "yafara ko?tafada cike da jima mi, kai ya gyada mata alamar eh
Dakin suka shiga a yanda Boma yatafi ya barshi anan suka dawo suka samishi yana ta karkarwan shi yana kuka wannan karon hadda miyau
Mummy ce taje ta zauna kusa dashi cikin tsananin kulawa tace "Haba Johnson, kasan yarinta ne yake damunta idan ta girma zata bari harma tadawo tana sonka"girgiza kai ya shigayi yana cewa "No mummy kawai saboda banida da lafiya ne takemin haka, I know she is a child but this is not how she treats Boma and the rest"yafada yana kara fashewa da kuka tausayinsa ne yakama Mum take ita ma idonta ya ciko da hawaye, cigaba yayi dacewa "Mummy please Ku kaini ko ina ne domin na samu lafiya nima nayi rayuwa kamar sauran muuutaneee....."kuka ne ya cikarfinsa. Tashi tayi tafita waje domin idan ta zauna itama kukan zatayi

  Da safe bayan na tashi nayi sallah nayi breakfast mummy  tabani wata riga mai kyau na saka sannan tace nafito zamuje wani wuri, daga ni sai ita sai kuma daddy da driver da suke gaba muka kama hanyar Garin iyayena,
sai yamma muka isa, direct family house din su Abban mu muka wuce aikuwa suna ganina suka faracewa ga Zahran Birni ga zahran birni
Part din yayan Abban mu aka kaimu 

An mana tarba maikyau Wanda aka kawo mana Danwake mai rai da lafiya Mummy kam zagewa tayi taci kayanta domin ko a gidan mu ne akayi sai an aikamata saboda yadda takesonsa
Bayan komai ya lafa ne naga su mummy da daddy sun shiga daki da  yayan Babana suna wata magana nikuwa ina kofar dakin a tsaye ina jiransu kasancewar bansan kuwa a gidan ba domin tunda nayi wayo ban taba xuwa ba ko wani abun aka yi saidai Mama tazo ita kadai haka suma ba sa wani zuwa mana sosai sai jifa jifa
Mummy ce tafara fitowa ga idanta yayi ja alamar tayi kuka, sai ga Baban Zaki da daddy sunfito suma duk jikinsu a sanyaye Baban zaki ne ya kalle ni sannan yace "Insha Allahu Fadimatou zan rike ki kamar yadda mahaifinki zai rike ki kuma zamu cigaba da yin Addu'a Allah ya bayyana su"yafada yana kokarin maida hawayen da suka zubo masa
Mummy ce kalle ni tana zubda hawaye tace"Allah ya rayaki diyata "sannan ta dauko dubu biyu ta ban sai a sannan nagane cewa wai barina fa zasuyi tabbbbbbb abunda bazai taba sabuwa ba kenannnnnnnnnn
................................................................................
While this page is dedicated to
Hauwa mu'awiyyah (besteee)
Asma'u Ahamd(Miss Ahmad)
Noordeen Muhammad Amrabat(deen)
Urs fateema Adamu Gamawa

Comments, vote &share through wattpad @FateemaAdamu

Fateegamawah

ZAHRAWhere stories live. Discover now