EPI 5

1.9K 100 0
                                    



WACECE AYUSH?

Hawwa_jiddah(AYUSH)yar shekara 18 a dunia ya'ce ga justice kamal Ibrahim ,Chief Justice dake a customary court abuja,yana daya daga cikin manyan parliamentary judicial respectives membership na presidential villa dake a aso rock.mahaifiyarta kuma Doctor ce ta bangaren abinda yashafi Mata wato (gynecologist) dr husnah Bilal..sannan mahaifinta justice Ibrahim kamal yanada mata biyu ne dashi bayan mahaifiyarta sekuma dayar matar tasa Hajia ateeka sageer wadda ma'aikaciyace a administrative block dake government house.

Mahaifiyar ta dr Husnah bilal Tana tareda mahaifinsu a gidansa dake Abuja while kishiyar mahaifiyarta kuma Tana kano daxama.su uku ne wajen mahaifiyarsu babban wansu na'eem dake aikin journalism a daily trust Abuja ae Ayush da takare secondary sch dinta tasamu admission har biyu a university din Ahmadu Bello dake Zaria dakuma Nile university dake abuja.se karamin kaninsu bilal dake ss1.

   Step mom dinsu kuma ya'yanta 2 .hilaal dakuma neerah wadda age mate din Ayush ce.Ayush ba 'awajen mahaifiyarta takeba Tana wajen step mom dinta anan kano dayake a saint Louis(snt Louis)takare secondary dinta se university data cike abu dakuma Nile kuma duk tasamu admission.jira take kawai abbanta ya xaba mata wadda xatayi.while neerah half sister dinta(wadda suke uba daya)Buk tacike kuma tasamu.

  Ayush taka sance wadda bata kula samari Dan aganinta maxa duk halin su daya .saurayi daya take kulawa shima kuma tun a pri sch suke tare da aji daya yawuceta SA'EED.karamin yaro ne karami Wanda befi shakera 22 ba shiysa mahaifinta justice Bedau yaran da muhimmanci ba gashi har ankawo kudin neerah shysa babanta ya kudiri niyyar hadasu aure da neerah amma takawo reasonable mutum bade SA'EED ba.shysa duk soyayyarta aganinta tatafi ga saeed kuma tunda baba yahana shykenan aganinta tarasa soyayyarta....

   BAYAN KWANA GOMA SHA BIYU:

   Hajia Maryam mahaifiyar NAUFAAL xaune take Akan kujera NAUFAAL kuma yanadaga gefenta akasa a zaune,takalli Dan nata duk yabi ya rame tambayar dunia tamasa yace stress din office ne yasashi haka..tace son kafadamin gaskia nasan halinka Baka karya kafadamin meke damunka meye matsalarka?duk kabi ka rame bakacin abinci dubi yadda kaxama this is not like you..kasan abbanka 1mnth yabaka ka fidda matar aure amma yau saura kwana 2 da maganar ko suna Baka fada ba balle maganar iyayen yarinya toh kasani inma hakanne yasaka karame haka gwara kama dawo normal self Dinka sarai kasan halin abbanka danma yana Abuja ne.abinda kawai xanbaka shawara shine idan har abbanka yahadaka da wadda yagadama kayi hakuri kaxauna da ita haka Allah yaso idan yaso DAGA baya kaga wadda kakeso seka aureta tunda Allah ne yace ai mata har hudu tunda sunnar manxo SAW ce.kanajina NAUFAAL?

NAUFAAL yai saurin kada kansa naji ammi kuma xanki yadda kikace,sannan Wlhy Ammi Wata yarinya nagani sekuma yai shiru ..Ammi tace go on inajinka ai,sannan yace Wlhy Ammi toh kuma Dana danyi mata magana haka seta nuna min she's not interested kuma Wlhy ni inasanta fiye dayadda naso meerah.ammi tai tsaki and so what ,baseka rabu da ita ba ko ana dole ne.sau bakwai muna hadaka da ya'ya masu tarbiyyah da sanin yakamata amma kaki Akan Wata Meerah,ko ba ita bace wadda tarunga Maka yawo da hankali duk kudin ka yakare akanta DAGA karshe taxo Ma ta auri abokinka seganin katin biki Kai ko ba ita bace?NAUFAAL yace eh itace Ammi,tace to sekai hakuri ka fawwalawa Allah al'amuranka tunda kaikuma haka destiny Dinka yaxo seka daukeshi amatsayin faith kawai. NAUFAAL yai murmushi insha Allah Ammi.sannan suka Dan taba hirar uwa da da bata basshi hakaba seda ta tababtar da farin cikinsa sanann ta zubamai abinci yaci.

   

  ABUJA:

Justice  kamal Ibrahim da Alhaji kabeer suhaylu sune azaune akan irin kujerun nan kirar Royal.agidan na justice kamal.kowanne da ruwa da lemu agabansa Alh kabeer yakalli justice kamal tareda fadin toh kuma yaushe kasa ita bikin neerah din?justice kamal yadan ajiye takardar dake rubutu a gefe Wlhy wannan shashashar yarinyar nake jira data likewa wani SA'EED bayan nafada mata ko bayan Raina baxata aureshi ba.Alh kabeer yai murmushi yaran yanzu kam se ahankali amma why not in sunasan junansu ka kyale su kawai si auren akan abinda xeje ya Komo.

NAUFAL (THE CHARMING) (COMPLETED✅)Where stories live. Discover now