Ep:13

1.5K 93 0
                                    

118

PART 2

    It's all about love story between a charming handsome and a beautiful lady..NAUFAAL&AYUSH.congratulations perfect couple Allah yakawo healthy babies😂💕

     •⭐•⭐•⭐•⭐•⭐•⭐•

Koda suka koma gidah bawani abun akaiba shiri kawai suka sakeyi Sannan aka debi yan Uwa guda 10 including mommy datace xata koma gidah saboda aikinta.se mamaa dakuma aunties na both mommy da baabaa.karfe 11 Dede jirginsu yasauka a Nmandi azikwe dake Abuja Capital territory. 11:20 Dede suka Isa kofar gidansu AYUSH Sannan suka firfito Dan kai amarya se after magrib akace tunda yan uwan angonma se da rana jirginsu  xe iso.shiga sukai ciki Kai tsaye AYUSH tawuce dakinta tareda sakin wani kuka matsinaci shikenan ustax yagama da rayuwarta yasata ahalin tsaka me wuya batagama tunanintaba Nadia tai knocking kofar tareda shigowa .

Mata agidan NAUFAAL. AYUSH taja tsaki wannan kuma kekika sani waye NAUFAAL?!nadia tai murmushi sunan sound like melody ko?! Well sunan mijinki ne..tsaki AYUSH taja to me ruwana wai Ma meya kawoki dakina?! Nadia tadinga Daria harda rike ciki matar NAUFAAL yi hakuri mana nan dakin na Nadia ne itakadai yanxu ai kintashi daga medakin bankibade inkinxo haihuwa ko inyayi tafiya kya iya xuwa ki kwana.bari Ma kiga Sannan Nadia tadauki akwati guda daya tareda Jan daya tabude kofar Tana kiran su bilal su kwashi sauran xa'akai gidan amarya AYUSH.wani sabon kukanne yaxoma AYUSH tabi pink dakin nata da kallo medauke da posters din mufti isma'il menk.sannan tasaki wani kukan .nadia taturo kofar Tana waka taxama taxama taxama,taxama dakko riga taxama dakko wando taxama.bata gamaba AYUSH tamike tana huci,kafin tace wani abu Nadia tagudu Tana fadin kije inji baba Yana parlor dinsa na dakinsa.seda taci kukanta Sannan tawanke face dinta tanufi parlor din babanta.

Da sallamarta tashiga ciki,baban ya amsa Yana shan ruwan lipton gefe guda kuma snacks ne Akan plate..Baaba yace Yawwa mamana xokixauna mana. AYUSH takarasa Tana hawaye.baba yace a'a banasan kukannanfa haba mamana aure fa akai miki bawai saida ke xa'aiba. AYUSH tai shiru se ajiyar zuciya datake. Baba yace Yawwa mamana takaina dama alkawarin danadade damaki yau nacika makishi. AYUSH tadago jajayen idonta dasuka kumbura saboda kuka Tana kallon babannata. Baba yace dafarkode nextweek xakufara lectures ko?! AYUSH tai nodding kanta,baba yace toh munyi magana dashi NAUFAAL din yace ba matsala insha Allah xaki je.sannan Abu nabiyu kuma da sabuwar motarki xaki fara xuwa school din taki halak malak irin wadda kikeso benz red color right?! Ai AYUSH data dire wani tsalle tai hugging babanta seta nemi bakin cikin datakeji tarasa,tadade tanasan motar kanta amma baba yace a'a in lokaci yayi xebata,togashi yanxu yabata kuma dream car dinta benz lover ce dama gashi favorite color dindatakeso red.

Baba yaci gaba da cewa yauwa nasiya maku harda Nadia da neerah sede su ba Benz bane, Camry ce kowannensu ke saboda biyayyar dakikamin amatsayina na mahaifinki Dana xaba maki miji kuma kika yarda kika amince shysa namiki wannan babbar kyauta. AYUSH tai hugging mahaifinta tana hawayen white stomach*laughs* nande baba yamata fada sosai kantabi mijinta AYUSH kibi mijinki NAUFAAL kada kitauye masa hakkinsa na aure domin mala'ikun Rahama suna tsinewa duk matar datai haka ,hakade baba yaita bama AYUSH fatherly advice Sannan yace tatashi tashiga ciki kar anemeta Allah yamaki Albarka idan anyi servicing motar xa'akawo maki har gidah. AYUSH tai godia Sannan tamike tashiga ciki tana mewa Allah godia dawannan babbar kyauta da mahaifinta yai mata.sannan tafice xuwa nata dakin.

Nanta tarar da kanwar mommy aunty lubna da cup a hannunta madara ne dayasha zuma se slices na water melon(kankana) Yawwa AYUSH rike Kinga lokaci Yana tafiya shanye tsaf akwai abinda xami.bayadda AYUSH ta iya adole tasa hannu ta karba cup din tashanye duka Sannan ta mika Ma aunty lubna..aunty lubna tace Yawwa yar gari ga ruwan wanka can a toilet karki wasa dashi pls hadin gaf gaf ne ,itade AYUSH nodding kanta kawai tayi Sannan tashiga bathroom din tai wanka da ruwan kamar turare dan kamshi take jikinta Yaxama so smooth and silky. Futowatai sannan taxauna abakin gadon duk aunty lubna na tsaye itade AYUSH tsayawatai Tana kallon ikon Allah! Nanfa aunty lubna tadakko wani roba na mangashi kamshi yatashi da aka bude nan tadinga shafa mata agashin line by line yadda mrs nawarma tayarfa mata kitson yan maiduguri Wanda akayishi da allura dama ga gashin AYUSH din tubarkAllah har gadon baya! Sannan aunty lubna tabi duk wani lungu da sako na jikin AYUSH tashafe mata shi da turare dakuma mai medaukar hankalin Wanda yashaka kamshin..atamfa kirar super Sheraton red and black ne design din aunty lubna tadakkosu akan kambasa sunturaru da kamshi Sannan taba AYUSH rike kisa Sannan tadakko wadataccen mayafi red tamika mata tareda mika mata sarkan gold da bangles dinta da takalmi flat red shima..light makeup aunty lubna tama AYUSH Sannan tamike kigyara abinda beyi ba yanxu xakiga lokaci yayi.

NAUFAL (THE CHARMING) (COMPLETED✅)Where stories live. Discover now