Ep:8

1.5K 104 1
                                    

⭐•⭐•⭐•⭐•⭐•⭐•

Karfe 11:45 jirginsu yasauka a birnin tarayya abuja..driver din baba ilyasu  ne yadaukesu a mota sanann yakaisu gidan na baba ilyasu ,matar baba ilyasu me kirki da mutunci ga kambama baki ita tatari me gidan nata da NAUFAAL da murnanta sannan aka sauki NAUFAAL awani katon parlor da bandaki aciki (kamar yadda aka fisani anfison da bako yaxo kafara xuba masa ruwa a buta kanuna masa bandaki ko kuma idan da pampo(tap)aciki kanuna masa sannan ya rage abinda ke cikinsa nadaga tafiyar dayai kamadaga fitsari ko bayan gida(bowel or stool).

Seda NAUFAAL yashiga bandaki yayo alwala sannan yafito parlor yai sallah raka'a biyu .yana xaune yana lazumi Wata yar budurwar yarinya davaxata fi age 16_17 ba tashigo sanye da katon mayafi tanada Dan kyanta ba lefi bayan tadan xauna a hannun kujera tana Bari ya gama lazumi.seda yagama sannan TA gaysheshi cikin Sanyayyar muryarta seda ya amsa sanann tace baffa(baba_ilyasu)yace ankai abinci dinning yana jiranka ,sannan tamike tatafi.tsayawa NAUFAAL yai yana naxari dama baba ilyasu yana da kamar wanann amma aka hadashi da Wata hawwa_jiddah,dukkoda bata Kai AYUSH Kyau ba shide da ita aka hada dashi Wlhy da yaxauna da ita.dawannan tunanin yamike sannan yafice xuwa dinning area din.

Bayan yaxauna akan dinning table ne yake cewa baba ilyasu sallah yakeyi lokacin da yaturo yarinyar dukkoda dama so yake yaji sunanta.baba ilyasu yai murmushi ohh NOOR ce ae.tayi saurin girma amma wani xuwa damukai kano da ita mukaje hartana kuka akace kakaita canteen(kanti)kasiya mata sweets. NAUFAAL yace ohh haba Wlhy banganetaba tab tayi saurin girma km.saukakken abinci sukaci Wanda baba ilyasu yace karsuci dayawa Dan justice kamal yace Dan Allah karsuci abinci yasa anmasu cima kala kala(varieties).suna gama ci sannan suka Kara kimtsawa suka nufi unguwar maitama dake Abuja gidan nasu AYUSH.

Yan mintina kadan danne suka kaisu gidan dayake bawani nisa tsakaninsu dayake shi baba ilyasun a wuse 2 ya.suna xuwa maigadi yamasu Iso,aka shiga dasu wani Royal parlor haddadde,kafin justice kamal ya Iso,seconds kadan justice kamal yasakko daga stairs cikin kaya na dattijantaka ,yana ta murmushi irin nasu na dattako da sanin ya kamata gaysawa sukai da baba ilyasu sannan NAUFAAL Wanda yasakko daga kujera yagayda sirikinnasa.bismillah justice kamal yace masu sannnan suka nufi wani katon dinning Cike da abinci kala kala Wanda xesa yawun mekaratu tsinkewa babu abinda babu tundaga kan dessert daxasu fara har abinci da drinks both local dana xamani ga hadin salad na musamman ,shide NAUFAAL tsakura kawai yake kunya yakeji gashi ga sirikinsa suna cin abinci.

Seda suka gama sannan dr Husnah tafuto suka gaysa da NAUFAAL dakuma justice kamal ,Wanda tayaba da hankalin NAUFAAL din kwarai ai bashi da abin aibu anan ga yaro kamili San kowa kin Wanda yarasa,bayan sun gaysa ne justice kamal yace takira Hawwa_jiddah su gaysa da NAUFAAL.dakin AYUSH tanufa Tana kwance Tana kallon wani movie,ta lulluba da bargo,dr Husnah tayaye bargon Tana kallonta sannu marar aikinyi sakarai wadda batasan abinda takeba to tashi tunda sokike kibawa mahaifin naki kunya tashi kafin kibatamin rai kishirya kisakko kasa guest parlor Wanda xe aureki yana jiranki acan sannan ki kashe wannan kallon kar indawo insameki a haka kinji nagaya maki.sannan tafita.

Da zumburar baki AYUSH tatashi sannan tashiga bandaki ta wanke fuskarta da ruwa ta fito ta tsaya Tana kallon closet Dinta dake cike da Kaya,se magana take a xuciarta Wlhy baxatasa Kayan dayake mata Kyau ba.sanann Tafada a fili Yawwa hade da sa hannu ta xaro wani material orange da baki datasan intasa anace mata baya mata Kyau tun a Kano acewarsu na fararene ita kuma bakace.bata damuba taxaro wani zumbululen mayafi baki sannanta yafa Batai kwalliyaba lip balm fari kawai tasa sannan TA nannaade kanta da katon mayafin hade da fesa turare sannan tasa flat takalminta yellow dukde Dan TA muxanta Wanda xe aureta tana cikin gyara mayafin Nadia tashigo Tana murmushi Inata sauri dama kinsani wannan lace din da akai mana da biki kikasa yafi maki Kyau hajiata.AYUSH tai tsaki Wanda akeso shi akewa kwalliya kinji sannan wanann Kayan nai ra'ayin sawa.nadia tace toh naji muje inganshi pls.AYUSH tace Wlhy bangama abinda nakeba kidau lemo da ruwa kikai masa seku gaysa tanan.nadia tace toh har anfara mana rowarsa kenan?AYUSH tace wani rowa kuma wannan ai namiki haka dankwi hirarku mai isarku kafin inxo Kings idan naxo baxesake yai maki magana ba.feel free and criticize me agurinsa..Nadia tafice Tana Daria .nadia nafita,AYUSH tajanyo locker tadau nikaf dinta sannan TA boye a hannu seda taga fitar nadia daga parlor wurin NAUFAAL sannan tai murmushi hade da saka nikaf dinta tanufi parlor din seda TA gyara shi sose a corridor Dan karya xame sannan tashiga ,dokkoda shima NAUFAAL din kafin takaraso sunglasses dinsa yaciro a aljihu yasaka bame ganin fuskar Dan uwansa.sannan tai sallama tashiga !!!!

NAUFAL (THE CHARMING) (COMPLETED✅)Where stories live. Discover now