1

2.1K 71 4
                                    

Tasss ta bata wani kyakkyawan mari me tafiyar da mutum lokaci daya.. Sannan dayar wadda suke tare itama tasa hannu ta tunkudeta ta fadi akasan tiles din dake a parlor din dagudu Wata yar'madedeciyar mata tafuto daga kitchen da alama me aiki ce tana fadin"aunty lapia naji kara haka?!tana isowa parlor din taja tai turus ganin wa'enda suke a parlor din Se huci suke inda sabo sunsaba xuwa suyi haka wani lokacin har ita suke hadawa siwa lilis sosai tabo na a dukkan jikinta na dukan dasuke mata baxasu irguba ,"murya narawa ta tsugunna har kasa tana gaishesu ina wuninku addah surayya da addah sadeeya?!wacce takira da "addah surayya tana wani sunce mayafin datai damara dashi a kugu Sannan ta yafa akanta tana huci kamar tsohuwar karya tareda kada idonta Ta aikamata da wata muguwar harara tajefawa yar'aikin. dabamu wuniba xaki ganmu yar'aiki?! Nayi tunanin yauma xaki shisshigin dakika saba kice xakisaka wannan hannun naki dayasha kanta kice xaki  rabiyar fadan wannan yar iskar tasa hannu Tana nuna matar dake kwance akan tiles da alama she's unconscious kila ta suma ma.wannan juyar (wadda bata haihuwa)dan kwa juya xance tunda bata aikin Komi sede taci Tasha tacika masai da kashi Allah ya isan wanmu daya auro Tama Wlhy kila kyanta da kalar datake dashi yarude shi dama mata sekace aljana Dan Kyau.. shekara kusan 20 ba haihuwa kullum jiya'i yau da ike angama dashi tawanke tabashi yasha ai yakasa Komi kullum cikin fadar basu cire rai... Bata karasa maganar ba wacce aka kira da "addah sadeeya tace enough surayya kina bata bakinki kina wa yar' aiki magana dallah xomu wuce mutafi dukan wani satin inya xagayo Ma seyafi wannan wallahi..Sannan suka fice ,itade yar'aikin bata tanka masu ba Se rufe kofar datai Sannan ta koma tana jijjiga matar dake kwance kan tiles din batako motsi"aunty,aunty..shiru kakeji bashiri tai kitchen tabude freedge tadakko ruwan gora me sanyi tabude ta yayyafa wa matar,,cikin ikon Allah kuwa matar tafara atishawa tana rike da kanta dan yadda yake sara mata kamar ze fado dan ciwo tarike kan tana salati Sannan tai addua tagoga akan.."dakyar tabude bakinta tace haule temakanni da pain killer cikin drawer jikin tv..da azama haule tamike tadakko takawo mata Sannan tace tadakko mata ruwa marar sanyi xatasha maganin dashi. Tasha maganin kenan tabude baki"tace haule temakanni nahau kan kujera Dan Allah .rufe bakinta keda wuya wani dattijon mutun yashigo ciki fari kyakkyawa yanada tsaho da jiki madedeci fuskarsa dauke da murmushi kamar kullum yashigo da dan trolley ahannunsa dakuma leda a dayan hannun "yadan daga murya Yana fadin Hajia Hafsat nadawo ai tafiyar nan baxata yiwuba yau..cak yatsaya da maganar lokacin da muryar haule me aiki ke reto akunnensa Tana fadin sannu da dawowa abba,ganin Hafsat dinsa kwance akujera goshinta yakumbura yayi suntum ga kuma parlor din yayi kaca_kaca da alama wani abu ya faru!

Bashiri yasaki trolley da ledan hannunsa akasa yanufi inda Hafsat din take Sannan yadagota yadora kanta a cinyarsa Yana duba goshin ga jikinta yadau zafi rau sosai daka ganta kasan batada lapia.."ahankali yace my Hafsat meya faru?!  dakyar "tabude baki tace hayatee(rayuwata,my life)bakomi bigewa nai da...setai shiru Tana naxarin da mexatace tabige Sannan tace ruwane yadan xube kan tiles shine na zume nikuma nabige da tiles dinnan Sannan Ta sunkuyar da kanta kasa Dan bata taba fadawa mijin nata cin kashin da yan'uwansa suke mata ba Sannan tace haule Ma karta soma fada sosai sunfi shekara 15 suna ci mata mutunci amma dede da rana daya bata taba fadawa mijin nata abinda ke faruwa ba.. Sosai yaji tausayinta Sannan "yace toh sannu my Hafsat kiringa lura pls shisa nace akaro wata wadda xata dinga kula dake kinki ,banasan kina wahala my Hafsat .."Hajia Hafsat tai shiru azuciarta Tana yaba yadda mijin nata ke sonta baya san ganin bacin ran nata ko kadan yawanci idan tai masa maganar ya'ya yakance ita yakeso ya aura bawai danta haihu ya aureta ba,hakade yake yawan fada mata kyawawan kalamai masu sanyaya zuciya. " my hafsat kinyi shiru' "Hajia hafsat tace haule Ma kadai Ta Isa hayatee ,Sannan tadanyi murmushi Ina tafiyar kuma naga kadawo ?! Yai Daria da dimples dinsa suka lotsa Sannan yasa hannu Yana gyara mata gashin kanta "my hafsat wallahi wakili natura Dan wani bangare na zuciana Yana cemin Kai mijin hafsat kakoma gidah your Hafsat ba lapia kawai naji baxan iya tafiya nabarki ba shiysa nadawo ashe ashe  dagaske ne bakida lapia wannan tiles din yazumeki,gobe xansa acireshi asa marbles ma..Hajia Hafsat tai Daria calm down hayatee baruwan tiles dinnan ruwane yaxube fa,haka kwanaki fa daga tv yajani seda kacanxa TV sets din duka uhm uhm hayatee nide kabarshi Allah Bakomi nawarke..sosai sukai Ta Hiran soyayyarsu kaman basu manyantaba  ya Allah kabarmu damasu sonmu!ledan daya siyo yadakko kaji ne ciki soyayyu sekuma bracelet na azurfa mekyau dashi anrubuta*my hafsat *ajiki.sosai Hajia Hafsat tayiwa hayatee dinta godia danbaya gajiya da faranta mata rai.hugging dinshi tai tana hawaye "I so much love you hayatee Allah yabarmun captain adam dina amin...

UMMI_A'ISHA (THE MAGNIFICENT)(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now