7

397 29 0
                                    

    •✨•✨•✨•✨•

"Yaya duk abinda kukace shiza'ayi Allah yasa hakanne yafi alkhairi amiin"

Yaya sameer ya ka'da Kansa "Toh shikenan xanyiwa haladu magini magana sesuje idan da akwai gyaran daxa'ai a part din daxata xauna sesuyi"

"Ehh baxa'a rasa ba musanman dayake bawani xama ake cikinsaba,nagode Yaya Allah yasaka da alkhairi"

"Babu komai adam Allah yakara hada kawunanku,idan aka gama gyare gyaren seta koma,bayan Allah yasauki hafsat din lapia se kuma asan yadda xa'ai inma takama tadawo nan din duk babu matsala"

Gwaggo taji da'di kwarai dagaske dan bata xaci abinda adam din xece ba kenan,"Allah yamaku albarka ,'dannan

"Ameen,ameen gwaggo nixan karasa can gidan"

"Eh gaskia to shikenan Allah yakaiku lapia ameen!"

Mikewa yai bayan yamasu sallama sannan yatafi gidansa,ransa duk badadi musanman maganar da akai masa yanxu,ahaka yai parking motar yashiga ciki,kamar kullum tana zaune a dogon couch din dake a gefen parlorn tana faman danna waya!

   Mikewa tai bayan yashigo tanufi inda yake tana murmushi"yaya adam,sannu daxuwa" tasa hannu xata rungumeshi yai saurin dakatar da ita "ina zuwa magajiya barinshiga ciki tukun"

Sannan yai wucewarsa daki yabarta nan tsaye,daki yashiga yai banging kofar hade' dasa hannu yadafe kansa dake barazanar ciwo kamar xe fado,daure zuciyarsa yai yashiga bandaki yadauro alwala yai sallah yana rokon Allah ya shigar masa gaba kan wannan babban lamari daya taso,

Magajiya na ganin yashiga daki tai wani murmushi sannan takoma kan kujera taxauna,"adam kenan xaka dawo tafin hannunane xanyi maganinka"wayar tace dake ringing a gefe ta katse mata maganar datake Ita kadai kamar zaucacciya ,saurin sa hannu tai tadauka ganin Wadda ke kiran tata surayyan gwaggo shine sunan dake rubuce boldly ajikin screen 'din ,tadanna answer sannan takara akunnenta tatashi tabar wajen taredasawa a handsfree

"Hello magajiya!"shine abinda surayya tace

"Na'am surayya yakike ya gwaggo?!"

"Lapia qlau,yanzu yaya adam yabar gidannan ai"

"Ohh haba nima bejima da shigowa ba"

"Ehh kinsan mun shawo kan gwaggo harma tayiwa yaya sameer magana,yanxu de in 'kar'kare maki zance yaya adam din ya yadda xaki koma kanon"

'Karamar 'kara magajiya tasaki tareda dedeta kanta"Ina godia fa,lalle kunada babban kaso idan nakoma kuwa"

"Tohm Muna godia ,se anjima"

"Nagode sosai"sannan  sukai sallama takashe wayarta takoma parlor tana murna,wayarta tajanyo takira munabi tasheda mata abinda ake ciki...





                •✨•

                  26

Bayan wata daya shirye shirye ake sosai agidansu hafsat na bikin sister dinta mjay,aranar aka kawo set biyu na akwati yan gaske babu abinda babu aciki,komai yayi akasa biki sati biyu masu xuwa inda xa'a kaita South Africa(capetown)!

Alokacinne kuma gwaggo ta tsayar da dawowar magajiyan nanda sati uku ma'ana idan anyi bikin mjay da sati daya kenan,,kulawa ta musanman gwaggon kebawa hafsat din musanman take aika mata da taliyar hausa dakuma waken soya mekyau,

Sosai yanxu cikin hafsat din yafito kamar Wanda yashiga watan haihuwarsa,tayi kyau abinta tana samun kulawa musanman agurin captain adam 'dinta,sosai takara shiga ransa ko lokacin daya mata magana kan magajiya xata dawo nan da xama bata damuba takuma nuna amincewarta akan hakan 'dari bisa 'dari!!!!

UMMI_A'ISHA (THE MAGNIFICENT)(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now