2

558 35 0
                                    

    •✨•✨•✨•✨•✨•

Note;narubuta kanwar Capt Adam da SURAYYA a farkon page,pages na biyu Dana uku..inatasaka SAFEEYA,,wannan yafarune sanadiyar wajen typing Wanda wayata take samun haka..Ayi  hakuri pls,xandawo saka SURAYYA karnai confusing mutane.inafatan xaku gane🙏🏽

                   •✨•

"Karaf idanuwansa sukai tozali da Hafsat dinsa kwance akasa ga kanwarsa surayya zaune daram kan ruwan cikin Hafsat din,gefe daya kuma sadeeya Ce tsaye da wayar charger a hannunta.."bude idanuwansa yai yakara rintsewa shin wannan mafarki yake kokuwa dagaske ne?! Addah surayya  naganinsa tamike tana noke kai sosai saura kadan fitsari yaxubo mata Dan tsabar tsoro ita dinma sadeeya saurin sakin charger dake hannunta tai,suka koma gefe daya suka tsaya zuciyoyinsu Se harbawa suke abinka da marassa gaskia tuni idanuwansu suka firfito waje suna jiran abinda xefaru ..

"Capt Adam ya ajiye Kayan hannunsa Sannan ya fice waje bebi takansu sadeeya dasukai tsuru tsuru ba,Yana xuwa yace"modu ku kullemin gidannan da kwado kada kubude harse nabaku izini,Sannan xankiraku xaku amsa min wasu tambayoyi,bejira tacewarsu ba yajuya yasoma tafiya dayake da dan taxara  tsakanin gate din da kuma cikin gidan,"modu yakalla hannafi,yace yaufa xa'ayita kenan agidannan inaga watan sallamarmu ne yai shikenan,jar miya takare Se kuka koriya shar,kuma yau Se kauyen garin dau"hannafi yai shiru Yama kasa magana kwata kwata Se zare Ido yake musanman dayatuno kauyen na garin dau dayadda tuwo ne kullum ba fashi miyar nan koriya ko dandano babu,"yanxu kuwa saboda Allah yasaba cin jarmiya mehade da kaji..

"Kafin Capt Adam ya isa cikin parlor din,addah sadeeya takalla addah surayya dake faman xubar hawaye sekace tsohon famfon dayaki kulluwa.. "kede banxa ce wallahy Banda mukullawa shegia sharri,"addah surayya tasa gefen mayafi Tana share hawayen fuskarta tareda fyace majina",kyaleni sadeeya wannan duk baxeyiwuba kawai de Se abinda Allah yayi .amma yau me karbarmu a hannun Yaya Adam Se Allah!tana cikin magana "Capt Adam yashigo gurin Hafsat dinsa yanufa ko kallonsu beyiba,sosai yasa hannu ya ciccibi abarsa yakaita daki yabata agajin gaggawa dayake akwai first aid box agidan ..sannu ahankali tafarfado daga suman datayi Sannan yadan sa ruwan dumi  ya gaggasa mata jikinta ,"dakyar take magana hayatee yaushe kadawo ?!"capt Adam yajuya Yana goge hawayen daya xubomai dan bayasan tagani,sosai yau yatabbar da cewar wannan shine dalilin dayasa rannan daxe tafi yaga jikinta yayi sanyi ,kuma tabbas duk tsahon shekarunnan inde yatafi yadawo  yake ganin Hafsat dinsa kullum da sabon tabo da sabon ciwo ..sosai tabashi tausayi dakyar yagyara mata kwanciya bayan yaballi magani yatemaka mata tasha "ahankali yake fadin calm down my hafsat,dama nace maki baxanyi kwana 3 ba if you can recall,yanxu de kiyi bacci akwai abinda xanyi .."hannu tasa tarike rigarsa pls hayatee kakyalesu ni na yafemasu wallahy Dan Allah banasan abinda xehadani da gwaggo.."Capt Adam yaxaro Ido nakyalesu fa kikace?!axo har gidana agina wannan rashin mutuncin kice baxandau mataki ba,"my Hafsat muna Bawa junanmu shawara nidake muna dauka muyi amfani da'ita.."amma kiyi hakuri da rashin shawararki dayau xansa kafa nashureta,wallahy yau sadeeya da safeeya sesun gane gonar wasuka shigo!beko jira mexata ceba yasakai yafice,"Hafsat tasa kuka Dan batasan tashin hankali,kuma batasan ace itace sanadiyar hada yaya da kanne ,"gashi jikinta kwata kwata ba kuxari balle tace xatabi bayansa haka tahakura tafara yan'adduo'in kwantar da musibar datashigo gidan,harde bacci dadda'da yai awun gaba da ita..

"Capt Adam nakomawa parlor yanemi kujera three sitter yaxauna yaharde kafafuwansa kamar betaba Daria ba,sosai yatsura masu Ido Yana kallon yan'uwan nasa Wanda Sukai masa abinda ko amafarki betaba xatan yan'uwansa najini xasuyi masa shiba,"yai gyaran murya yace surayya kece babba,babbar banza babbar kwabo shashasha mekwakwalwa irinta kifi,wadda kanwarki taxauna Tana juyaki ubangiji Allah yakyauta,"Sannan yakalla sadeeya datai kasa da Ido sekace mumina,yace ke dago idonki karamar munafuka ,dama ke tunda annamimiyace..yanxu kafin Komi yakwana kafin inmuku dukan kawo wuka Wanda xaku gane wannan shine babban kuskuren dakuka tafka a rayuwa.."inasan kufadamin uban meye yake kawoku gidana shekara da shekaru kunacin mutuncin matata?!

UMMI_A'ISHA (THE MAGNIFICENT)(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now