10

464 24 0
                                    

Azuciye tafara sauka daga stairs tana huci kaman zakanya,da sauri baby kay tabiyota tana magana"ummah bade wajen su zakiba ko?!"

Magajiya na huci take fadin"can zanje mana"tafadi hakan tana karasa sauka daga stairs din...da sauri baby kay tariko hannun magajiyan tana girgiza kanta"ki kyalesu ummah yanxu inkinjema yaya yahya(abokin baffansu) yana facing wajen da suke"

"To yaya kikeson nayi, kinasan nabar UMMI AISHA dawancen na wajen dayaxo a Benz?"tafadi hakan tana nuni da Inda suke da hannunta

"Ummah fault dinki za'agani its better kibari baffa yadawo seki san mexaki ce masa"

"Shikenan muje aiya kusa dawowa"

Haka suka koma saman suna shirya yadda xa'ai idan baffan yaxo

Bangaren UMMI AISHA kuwa tsayawa tai kaman statue of liberty mutumin se zuba yake shi kadai kamar famfo"Toh dafarkode kamn yadda nace maki sunana abdulshakur Mahmoud,asalina dan garin maiduguri ne dake jihar borno aiki ne yakawoni nan garin Kaduna inada mata ta daya da 'ya guda daya kuma tunda naganki baiwar Allah najikin kwantamin,ko xan iya sanin naki sunan?!"

UMMI AISHA tai shiru kamar me tunani da kamar baxatai magana ba sekuma tace"tohh malam abdlshakur ni sunana UMMI AISHA ina xaune anan tareda iyayena da yan uwana,sannan aji na biyu a secondary"

"Masha Allahu"yafadi hakan yana shafa cyboc dinsa "tohh malama UMMI AISHA naji da'di kwarai dagaske dakika bani hadin kai mukai magana dake ta fahimta,kuma tunda na'dora idona akanki bawai yaudara ba naji inasonki har cikin zuciyata inakuma fatan kizama matata uwar ya'yana"

UMMI AISHA tai murmushi hade da kallon lokaci ta fuskar agogon dake hannunta na hagu"well naji duk abinda kace kuma zancen gaskiya badan ka hadani da Allah ba walllahy baxan saurare ka ba,kuma mu ka'idar gidan muce se mun karashe karatun secondary muke sauraron mutane zancen aure ma kuma wannan bai taso ba domin mahaifinmu yanaso muyi karatu,kuma insha Allahu zamu cika mashi burinshi,ni xan wuce gidah"

Gaba daya se yaji UMMI AISHA takara kwanta mashi azuciya domin tanada kaifin hankali da basira daga ganinta,murmushi yai wanda yake kara fito da ainihin kyansa domin ba laipi kyakkyawane kuma baxe wuce shekara talatin da biyar ba a duniya"tohh shikenan gimbiyata yadda kikace hakan za'ai,barin kyaleki karmuyi laifi wajensu mama ko?!kar nazo nan gaba neman aure a hanani"

Itade UMMI AISHA daria kawai tai sannan ta masa sallama ta wuce cikin gidah bayan yayi yayi ta karba hasafin dayai mata na kudi taki,hakan ba karamin sake burgeshi tai ba domin ya lura da ita ba irin yammatan zamanin nan bace wanda suka zamto kaji seda 'tsaba,kaida kudinka suke ko kari kamar su dan neka su kwace,haka yajuya kan mota yai reverse cikeda kaunar yarinyar daya fara tozali da ita yaga kuma ta kwanta masa arai wato UMMI AISHA...



                   •✨•

                    43

____Tana shiga cikin gidah gabanta yafara dukan uku uku nasanin abinda xataje ta tarar ganin Baby Kay taganta dashi,da sallamarta tashiga cikin parlour din tayi mamakin rashin halin ko'in kula da magajiya da baby kay din sukayi mata,haka tashiga cikin daki tana mamaki dukkoda tasan akwai wata a 'kasa .....

Bayan sallar isha'i kamar kullum captain Adam yadawo se magajiya ita kadai a parlour tarairayar arxiki tayi masa dan yayarda da abinda zatace

Seda yagama cin abinci yahuta hankalinsa kwance sannan magajiya ta goce tafada mashi karya da gaskiya harda fadin wannan bashine karo na farko ba tanayin hakan tun captain adam najinta kawai harya yayarda tunda tafadi in karya take yatambaya abokinsa yahya yaji agabansa akai komai

UMMI_A'ISHA (THE MAGNIFICENT)(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now