18

367 21 0
                                    

•✨•✨•✨•✨•✨•

Kodah Ummi Aisha tahau sama bata xame ko'ina ba se band'aki tana shiga tafara brushing bakinta tatass ta wanke tasake kuskure shi da mouth fresh sannan takoma parlor tanabin sandararriyar indomien tata da kallo,siririn tsaki tasaki tareda shiga d'akinta tad'akko madara datake had'awa da malt da daddare cikin sauri tad'akko cup a store d'in saman ta juye maltina da madarar aciki ta kad'a ta shanye,indomien Kuma tasa plate ta rufe da niyar anjima idan koma waye yatafi xata mik'awa me gadi..

    Jay nagama parking yashigo cikin parlorn da sallamarsa,hugging sukai da ashraf suka gaysa irin gaisuwarsu ta aminan juna,a parlor suka baje suna hira,jay ne ya waiga kaman me neman wani abun;

"Dude ina our wife?!,kasande sarai don Ita naxo"jay yafadi hakan yana kallon ashraf.

"Barin kira maka ita yanxu tahau saman bata xaci Kai bane"

"Yawwa isauri pls,sannan wa kakewa tallan 8 1/2 packs d'inka haka ko kyan gani babu??"

"Ina ruwanka?sannan 9packs ne ba 8 1/2 ba"

Daria jay yai me isarsa ashraf yajuyo ya hararareshi sannan yahau saman yana tafe yana karanta suratul baqra  ahankali har ya isa d'akin Ummi Aisha,batare da wani b'ata lokaci ba ya murd'a handle yashiga ciki,xaune Ummi Aisha take ga plate d'in indomien nan tarufe amma indomien ta fito ta gefe kana gani Kasan ba'a tab'a taba,idonta yakad'a yayi jajir da alama kuka tad'an yi,tsayawa yai ya jingina ajikin 3D d'in d'akin ya sak'ale hannuwansa yaxuba mata manyan idanuwansa yana binta da kallo,

"Ummi Aisha Adam Abdulrasheed!" Ashraf yace da Ummi Aisha haka da tad'ago kanta alokacin sekuma tai saurin mayardashi k'asa ganin haryanxu ba riga ajikinsa.

"Meyasa bakici indomien naki da kika mata had'i ba?!"

"Nak'oshi idan xakaci Kuma kad'auka gatanan nabaka"Ummi Aisha tace haka, ji take kamar tatashi ta shak'eshi don haushi

"Ewww,gross! Allah ya kiyaye kin tab'a ganin naci abinda kika dafa?!" Ashraf yace hakan dukkoda k'arya yake shi Kansa ba'asan ransa yafad'i hakan ba gashin tun d'axu ransa ke biyawa akan indomien ganin yadda tasha had'i wai duk dan karta gano lagwansa shi yasa yake mata haka,

Batai mashi magana ba shiru tai abinta tacigaba da kallon gefen d'akin,

"Ki shirya ki sakko k'asa jay yaxo xaku gaysa" yace hakan yana k'arasa fita daga d'akin,d'akinsa yawuce yad'akko shirt yad'ora akan wandonsa sannan yasauka k'asa,

"Haba dude daga kiran our wife kuma sekaje kashantake kamar wanda aka aiki bawa garinsu"jay yace da ashraf hakan wanda yasakko alokacin,

"Okay kana nufin dana hau kawai senace mata kisakko ga jay haba jay be matured mana"

Tsaki jay yasaki yana hararar ashraf dashima hararar tasa yake,kodah ashraf yafuta daga d'akin Ummi Aisha mik'ewa tai tashiga band'aki tasake wanke jikinta sannan tafito tat'saneshi tashafa mai da su turaruka ,doguwar rigar atamfa k'irar A shape tasaka me torches orange tayi light makeup,bakinnan yasha amber orange jambaki ta murza d'aurin ture kaga tsiya,harta d'akko mayafi tafasa ta ajiyeshi tasauka k'asan tareda plate d'in indomien nata,tun tana kan bene ashraf yake binta da kallo kamar ya cinyeta,kayan da tasa sun mugunta amsarta ga d'aurinta, uwa uba jambakin ya k'arba d'an karamin bakinta,cikin cat walking d'inta ta k'araso cikin parlorn sedata fara shiga kitchen ta ajiye plate d'in hannunta sannan tadawo parlorn taxauna akan hannun kujerar dake facing wadda ashraf ke xaune,

"Our wife"jay yace da Ita,

"Ina yini jay?! Yagida Yasu mama??"

"Lapiar su qalau Alhmdlh, naji tana xata saka rana taxo itama"

UMMI_A'ISHA (THE MAGNIFICENT)(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now