3

561 31 0
                                    

"Jirgi driver nagama parking a parking arena din gidansu na kaduna Capt Adam yasaka kafarsa yafuto tare da addua ,Sarai yasan yanxu merabashi da gwaggon nasa Se Allah,Dan haka kannen nasa suke ko abu sukeso agurinsa takan gwaggo sukebi dan sunsan bayai mata musu,bilkisu kanwar suce kawai halinta daban acikinsu shisa basa shiri da ita kwata kwata,da sallamarsa yashiga gidan yana murmushi,ganin bakowa a parlor din dake kasa yabashi damar sanin lalle gwaggon na parlor dinta nasama..

"Nandinma sallamar yai Sannan yasakai yashiga,"zaune dattijuwar matar take sosai Ta manyanta amma dukda haka ,tananan da kyanta jajir fatarta take,Sannan ga gashi nan har gaban goshinta,kamar baxata amsa sallamar ba sekuma Ta amsa,Sannan ta kauda kanta gefe,gefe daya kuma addah surayya ne da sadeeya suma suncika sunyi fam,kotakansu bebi ba yaxauna daf da mahaifiyar tasa ,Kansa akasa yake fadin"gwaggo barka da yamma,nasameku lpy?!gwaggo tai shiru murya adakile take fadin"lpia qalau..ahankali yakara cewa"gwaggo Hafsat tace tana gaisheku kafin tazo,itade gwaggo Shiru tai batace cikan kaba,

"Gwaggo tagutsiri goranta,sannan tadaga kai takalli Capt adam,tsugunne kusa da ita kanta akasa,ita kanta tasan dan nata yanada tarbiyya,"Sannan tace 'dannan,(dayake bata fadar sunansa dukkoda shine nabiyu dashida alhaji sameer dukbata fada shi alhaji sameer tana kiransa da"wannan yaran"kunsan Fulani da kunya,.."Capt Adam yace Na'am gwaggo,

"Gwaggo tace kabani hankalinka nan magana nakeso muyi dakai ,nakira wannan yaron(alhaji sameer)yace mani yanxu xexo shima,amma kafin yaxo inaso kafadamin menene dalilinka nadukan kannenka saboda matarka tanemi tahanasu shiga tana kokawo dasu,kaxo kasamesu ahaka kanemi dalili sunfara fada maka kadakatar,kayi musu dukan kawo wuka,nan sukaxo magana Ma kowacce daga cikinsu dakyar take,saboda azaba,Sannan kadarorin daka basu ka kwace abinka,sanin kanka Kasan ba'a kyauta akarba,shin menene dalilinka nayin hakan?!sarai Kasan ba'a canxa dan uwa har abada amma mata kuwa ana canxa ta,hannunka de baxe lalace kace xaka yarba,amma dukkayi watsi dahakan,tabbas wannan Hafsat nayi danasanin amincewa dakai ka aureta .."Capt Adam yai saurin dakatar da'ita haba,Haba gwaggo karkice haka Wlhy tlhy bahaka halin Hafsat yakeba,"wa'ennan yaran sunxo sunhada maki zance ne kawai gwaggo.amna Hafsat mutuniyar kirkice wallhy gwaggo tsahon shekaru kusan 20 kenan surayya da sadeeya ketattaro bakaken maganganu sujefa Hafsat dashi ,bama shikenan ba wallahy gwaggo harda duka ,ni bantaba saniba saboda Hafsat tace kada Wanda yagayamun dagacikin yan'aikin gidan,kuma satin da yawuce wallahy har gidah suka xo suka mata duka har goshinta yafashe,Sannan Jia Ma Wlhy surayya nasamu akan ruwan cikinta wannan ninagani da idona wallahy,itakuma sadeeya tasa charger tadaketa,

"Sannan agabansu nakira haule me aikinmu tafadi abinda tasani akai,hakama masu gadina,kuma duk basu musa ba gashi inna masu karya,sannan abubuwana Dana karba wajensu gwaggo dama ni bakyauta nabasu ba,wa'ennan yaran basuda mutunci gwaggo,"caraf gwaggo takarbe tana huci uhm uhm 'dannan karka sake cemasu haka,kaide kawai ita hafsatun tahadaka da kannenka taji dadi,amma intasan Wata ai batasan wataba ko?! Shide Capt Adam yai shiru sanin halin gwaggo dayai,

"Addah sadeeya dake gefe tai wani shu'umin murmushi ,tana wani karkada kafa,gwaggo Yaya fa baxe yadda da komai ba ingaya maki gaskia ,saboda wannan matar tariga tawanke tabashi yasha,"Capt Adam yace aibase tasha wahala tawanke tabani nasha ba,dakaina nake kafa kai nakesha Sannan yamaka mata harara,"tuni sadeeya tadubibice danbata xaci amsan daxebataba kenan,tuni ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da gashin dake jikin center Carpet din parlorn.

"Gwaggo tace toh Allah ya kyauta tunda haka abin yaxama kuma,"Capt Adam yamarairaice murya ,gwaggo Dan Allah kiyi hakuri nibada wani abin nafada haka ba,wa'innan yaranne gwaggo komai hakurin mutum sesun kaishi makura,suna cikin magana alhaji sameer yashigo kamarsu daya da Capt adam, sede shi becika fari afuska ba,sannan yamanyanta shima amma kyansa yananan,

"Sosai alhaji sameer ya tsugunna har kasa yagayda gwaggonsa,Capt Adam Ma yabashi hannu suka gaysa Sannan yakuma gaysheshi na musamman,su addah surayya ma suka kwasa gaisuwa gun Yaya babba,kamar yadda suke fada mashi ,dan baya wasa ,sharara masu mari agunsa ba abin wahala bane,

UMMI_A'ISHA (THE MAGNIFICENT)(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now