16

343 27 0
                                    

Ashraf nagama parking d'in motarsa yashiga cikin gidan hannunsa d'auke da ledojin dayasiyo Kayan k'walam da mak'ulashe,shiga d'akunan yai yana duba Ina Ummi Aisha take d'akin karshe na cikin corridor yaganta k'udundune cikin bargo tana munshari,daria abin yaso yabashi yasan sarai ba bacci take ba yaga side lamps d'in gadon a kunne kaf futulin d'akin ma a kunne suke,k'arasawa yai cikin d'akin yana bin d'akin da kallo sosai yamasa Kyau komai na d'akin k'irar royal ne gawani k'amshi dake tashi na khumra da turaren wuta,yajima yana kallon santala santalan cinyoyinta da suka fito waje kad'an gashi ne ajiki a kanannad'e ga wani sihirtaccen k'amshi dake tashe daga jikin nata,dak'yar ya iya seseta Kansa yasa hannu yana d'an dukan k'afarta ahankali,yitayi kamar baxata farka ba tacigaba da munsharin k'aryarta,

"Ke!"ashraf yace da Ita yana cigaba da tashinta,

"Uhm uhm"tace hakan tana ture hannunsa,

"Wake up abeg ko kuma na hau gadon natasheki"

Ummi Aisha najin haka ta mik'e tana murza idanuwa kamar gaske,

"Ga abinci nan kitashi kici"yace hakan yana mata nuni da ledar

"Na k'oshi nagode"

Murmushi ashraf yai da ke k'ara masa kyawunsa yajima yana kallonta kafin yasa hannu a aljihu ya ciro wayarsa yafara danna nambobi da alama kira xeyi,Ummi Aisha naganin haka ta ware ido tana binsa da kallo murya narawa take fad'in

"Mekake shirinyi hakan?!"takarashe maganar kamar xatai kuka,

"Baffa xankira nagaya masa tunyanzu munfara gardama dake kafin akai ko'ina nasihar daya mana bata shiga kankiba"

"To to naji zanci,naga ba yunwa nakejiba shysa"

"Haba wa y'ammta seda ruwan ciki akejan na rijiya ai"yafadi hakan fuskarsa ba yabo ba fallasa,

Itade shiru tai tana tunanin maganar dayai yanxu take jikinta yafara rawa,ahankali tasakko daga kan gadon tasa hannu a ledar daddad'an kamshin aroma na kajin ya bugi hancinta,hannu tasa taciro cinya k'wara d'aya tafara ci ahankali dakyar tacinye tasa hannu tafara rufe ledar alamar ta k'oshi,

"what the fu.."ashraf yace hakn yana kallonta Sannan yak'arasa kusada ita yasa hannu a ledan yabud'e ta duka yasake tura mata gabanta,

"Nak'oshi wallahi"tace dashi a shagwabance harda langwab'ar dakai wai dukdan yaji tausayinta ,

"Wallahi kinsan Allah sekinci dayawa waxakiwa yanga?!sannan ki bud'e yoghurt d'innan kishanyenshi tatass ba wasa nake dake ba inkuma baxakici ba sena fad'awa baffa"

Bayadda Ummi Aisha ta iya haka tadinga d'urawa cikinta kajin tana korawa da yoghurt,ashraf dake gefe se dariar mugunta yake mata ahankali gashi ko d'an tausaya mata yak'i yayi,seda yaga taci sosai Sannan yace tabarshi haka,dakansa yad'au wanda tarage yasa acikin mini freedge d'in dake gefen gadon,sannan yashiga band'aki gaban Ummi Aisha se dukan uku uku yake,bejimaba yafuto yacanxa kayansa xuwa pajamas(Kayan bacci)kashe fitilun d'akin yai yabar side lamps 'din kawai dasuka bada dimlight,ahankali yakashe d'ayar saura ta b'angaren Ummi Aisha jikinta se kyarma yake,ya lura da hakan yana sane yahau kan gadon ganin haka yasanyata ja baya yasake matsawa takoma c'an k'uryar gado yasake binta,har jikin bango suka Kai ahaka numfashinsu yana dukan na juna,dede kunnenta yai kamar Wanda xe bata side kiss sekuma yafara mata magana a kunnenta cikin wata irin murya me dad'in sauraro ga k'amshin mint da bakinsa yake ,ahankali yafara fad'in;

"Stop thinking negative 'yammata,keda kika tab'a yi menene na tsoro ?!after all ni ba abinda xanyi maki"yakarashe maganar yana taune pink lips d'insa had'e da girgixa mata kai Sannan yasa hannu yakashe fitilar data rage ya mik'e tsaye yafita,

UMMI_A'ISHA (THE MAGNIFICENT)(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now