14

319 17 2
                                    

•✨•✨•✨•✨•✨•

Tunda captain adam yafice Ummi Aisha da Hafsat suka bude sabon shafin kuka,Ita Ummi Aisha kukan ta akan meyasa muhannad xe mata haka duk yardar da ke tsakaninsu amma yaci amanarta haka?!ita kuwa hafsat nata kukan tanayinsa ne kan abinda muhannad yaiwa tilon 'diyar tata da Kuma yadda rayuwarsu ke shiga halin tsaka me wuya,har lokacin bacci basu dena kukan ba sede suyi su tsagaita su cigaba babu me tausar wani dakyar Hafsat tadanne zuciyarta taiwa Ummi aisha nasiha me shiga jiki tareda bata wasu addu'oi daxata dingayi saboda kariya daga shaidan dakuma sharrin masu sharri..,

Bayan kwana biyu da abinda yafaru kafin kace me Ummi aisha ta rame tashiga damuwa tunma baga hafsat dinba itama tata ramar ta bayyana sosai sefa mama da mjay ne ke tausar su,Ummi Aisha ko abinci bataci kullum se amminta tamata dagaske sannan take iya tsakula taci yawanci tafishan oats shima dan bayadda xata yine,ko makaranta ta'ki zuwa aganinta kowa yanxu yasan xancen 'kawayenta sunxo sunyi kiran amma fafur ta'ki komawa, ashraf ma yakira ya kira taki 'dauka daga karshe ma kashe wayar tata tayi tun Hafsat na matsa mata kanta shrya taje makaranta Kar awuceta a abubuwa har ta kyaleta domin intace tajema kukan takeci gaba dashi ba ''kak'kautawa shiysa kawai ta kyaleta tasaka mata ido tana Kuma mata adduar Allah yakawo 'karshen wannan abu da yafaru,gaba 'daya tacanxa kamar ba Ummi aishan ta ta da ba ta rame taxama kmar wacce aka canxawa kamanni ,dama haka magajiya keso Itako zaman iddar dake kanta badamunta yaiba dukkoda saura wata biyu da 'yan kwanaki ta tattara tabar gidan,Ita kawai rayuwarta tafuso ta bu'de ido taga rayuwar Ummi Aisha da hafsat acikin ba'kin ciki(Allah ya karemu daga sharrin masu sharri)

A ranar muna_b taxo da safe lokacin baby kay nashiri xata makaranta bayan sun gaysa muna_b ke tambayar baby kay;

"Tana xuwa makarantar kuwa?!"

"Bata xuwa ko'ina ai ko 'kofar gidah"

"Ah'to dama ina xata da wannan abin kunya dole se xaman gidah ai,Yaya asharf din kuna magana kuwa?!"

"Ba lefi muna magana a matsayina na 'kanwar budurwarsa ba,sister in law yakecemin"

"Se ahankali xata fita ransa"

"Allah aunty kullum seya tambayeta fa wai yana kiranta bata 'dauka wai tama kashe wayan nata gaba daya lapia kuwa?!nace ai sunyi tafiya daxan gaya mashi abinda yafaru sena fasa saboda karma yace xezo gidah ya ganta yaji tausayinta"

"Gwara da kika fasa tunda anga yayar kice xa'ace da'di kikeji har sugano wani abin kibari ahankali xamu fitar da komi kowa yagani Kinga shima daga lokacin xata fita ransa"

"Sosai kuwa,barin tafi sch aunty"

Takarashe maganar tana gyara mayafin jikinta

"To Shikenan sekin dawo"

Baby Kay nafuta muna_b tadawo kusada magajiya,

"Yaya 'kawata lapia kika kirani bade jikinneba?!"

"Ai asibiti xaki rakani dubi gashina gaba daya ya xaixaye babu komi akaina"

Tafadi hakan tana bu'de 'kwanyar kan nata da babu ko silin gashi kamar kan namiji dayasha 'kwal'kwal,jimami muna_b ta mata na ganin yadda kan nata yaxama sannan suka fita xuwa asibitin standard dake kan titin tarauni,bayan likita yagama gwaje gwajensa kenan ya dago ya kalli magajiyan datai zuru da idanuwa 'can tace;

"Likita me result 'din yabayar?!"

"Dafarkode xan lissafo signs na ciwon ki duk Wanda kike irinsa seki gayamin ko?!"

"To dr"

"Ko kinajin new onset or change akan yanayin ciwon kan Ki?!"

"Sosai dr kusan kullum seya canxa"

UMMI_A'ISHA (THE MAGNIFICENT)(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now