*🤦🏼♀🙆🏼♀ILLAR RIƘO*
_*('Yar riƙo)*_*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
_____________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com*Dedicated to all my fans*
_*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_
*Page 28*
Bayan Ammi ta dawo daga rakiyan Maryam makwabciyarta, kai tsaye ɗakin su Luba ta nufa, kwance ta same ita kaɗai a ɗaki tana karanta wani littafi, gefen gado Ammi ta zauna ta kira sunanta " Luba!"
" Na'am Ammi " ta amsa haɗe miƙewa daga kwance
" Tambayarki zanyi da fatan kuma zaki bani amsar tamabayata yadda ya kamata."
"In Shaa Allah Ammi" Luba ta ce a sanyaye.
Ƙura mata ido Ammi ta yi don son tabbatar da zarginta sannan ta ce " yaushe rabonki da ganin al'ardarki?"
Wani irin fad'uwa Luba ta ji gabanta ya yi don bata tsamci wannan tambayar ba, kame-kame ta shiga tana i'ina "em.., emm...wannan watan ma na yi. "
" Kin tabbatar?" Ammi ta ce har yanzu idanuwanta na kan Luba.
" Eh" Luba ta ce tana gyad'a kai.
" Amma idan ban manta yau kimanin wata uku kenan baki zo kin amshi kuɗin pad a guna ba, ko kina da mai baki kuɗin ne yanzu wanda bani da masaniya akai? "
"A'a Ammi dama da sauran na da bai riga ya k'are ba."
"Really! wai yaushe kika koyi ƙarya hakane?, yanzu pad gudu takwas ya isheki amfani har na tsawon wata uku?, keda kike al'ada na tsawon kwanaki shida , haba mana Luba dan Allah ki faɗan gaskiya kin ji " Ammi ta ƙarasa maganar da sigar rarrashi.
Mamaki ne ya cike Luba don bata taɓa tsamin Ammi tasan tsawon kwanakin al'adarta ba, ƙarya Luba tayi mata ta ce "Yusrah ce ta bani nata."
Murmushi Ammi ta yi ta ce " ya yi kyau. Wani mai kike shafawa yanzu? Ko kema kin fara shafa man bleaching ne?"
Zaro ido Luba ta yi ta ce " Ammi bleaching kuma?, nikam me zai haɗani da bleaching. "
"Na sani ko ke kin bi sahun 'yan mata yanzu domin shi suke yayi yanzu kuma gashi na gan kema kin fara haskawa" cewan Ammi, tana yi tana ƙara yiwa Luba kallo ko zata iya gano wani alamar daga gareta.
"Wallahi Ammi bana shafa komai. "
" Ok shi kenan " Ammi ta ce ta miƙe ta fita daga ɗakin.
Da yamma bayan Yusrah ta dawo daga School har ɗaki Ammi tai kiranta, tambayarta Ammi ta yi yaushe rabon da ta gan Luba ta yi al'ada.
" Ko wannan watan ma ta yi " shine amsar da Yusrah ta bata.
"Ok zaki iya tafiya."
Mikeywa Yusrah ta yi ta koma ɗakinsu inda Bintu ke jiranta tazo ta duba mata wani assignment da aka basu a school. Yayin da ita kuma Luba ta jima da barci dama aiki kenan yanzu bata iya yini guda ba tare da ta yi barci akalla sau uku ba ko ma fiye da haka.
Washe gari da safe Jabir ya shirya zai tafi gun aiki kenan har ya tada mota zai wuce Ammi ta aike Bintu tai kiran shi, a tare suka iso da Bintu ya ce bayan ya isa gunta " Ammi gani. "

YOU ARE READING
ILLAR RIƘO ('yar riƙo) sabon salo
Short StoryEdited version ɗin illar riƙo wannan labarin ba sabo bane illar riƙo ne nayi editing na sabon ta shi dan kuji daɗin karanta shi asha karatu lfy.