*🤦🏼♀🙆🏼♀ILLAR RIƘO*
_*('Yar riƙo)*_*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
_____________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com*Dedicated to all my fans*
_*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_
_*Wannan shafin naki ne ke ɗaya @ Khairat (illar riƙo fans group)*_
_*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_
_Manzon Allah S.A.W ya ce : zagin musulmi fasik'anci ne kuma kashe shi kafirci ne / yaƙarsa kafirci ne._
*Page 20*
Kayan Bintu ta kwashe ta fara wankewa. Tana yi tans tunanin amsar da zata bawa aunty Jameela dalilin aman nata ita dai tasan ba abinda aunty Jameela take tunani bane, hasali ma ko saurayi bata dashi, tun sanda anty Jameela ta mata duka fitar arziki sabida ya sayyadinsu yazo neman izini wai yana sonta.
Wanki take tana rawa sanyi hatta hakoranta rawa suke sabida wani sanyin da take jin yana shigarta. Tsame kayan ta yi haka don ko wankuwa basu yi ba ta zuba a ruwan ɗoraya, ta ɗoraye kannan ta shanya. Komawa ta yi kan kwanukan wanke-wanke take jibge a bakin famfo, famfon ta buɗe ta ta fara ɗoraye su kawai tana kifawa a kwando ba tare da ta wanke su ba, don burinta yanzu bai fi ta ga kanta a ɗaki kwance ba watakil ciwon zai ɗan sauka. K'asa cigabawa ta yi sakamokon wani irin jiri da taji yana ɗibanta, da
dafen bango ta ƙaraso falo har ta kusan shiga ɗakinsu kenan, aunty Jameela da ke kishingiɗe a kan cushion ta daka mata tsawa wacce ta razana Bintu domin bata yi tunanin da mutum zauna a falon ba, aunty Jameela ta ce cikin daka tsawa " dakata kina nufin har kin kammala duk ayyukan da nasa ki ne?"Girgiza kai Bintu ta yi alamar a'a.
"Good! shine kika dawo ciki, kema bari ki huta ki tunda nima na taho ciki ko? "
Kai Bintu ta kuma girgiza mata alamar a'a.
A hasale aunty Jameela ta tashi ta nufo Bintu. Bintu kuwa ganin aunty Jameela ta nufo ta , ta fara kiciniyar buɗe kofar ɗakin amma yaƙi buɗuwa sabida hannunta har rawa take yi, Bintu ta ce "na shiga uku " Innalillahi-wa-ina ilahi raji'un ta fara karantawa, domin Allah mai girma da daukaka Yace duk wanda wani musiba ya tunkaro shi ya lazimcewa faɗin haka. Shi Bintu keta nanatawa kuma tana ƙoƙarin buɗe kofar har aunty Jameela ta iso gunta bata sani ba saida ta ji saukan mari ta farga, take kwalla da suka taru a idonta suka fara sauka kan kumatunta, zuru-zuru ta yi tana kallon aunty Jameela kamar mara gaskiya. Aunty Jameela ta ce " guduwa kika so ki yi ne?"
Kai Bintu ta kuma girgizawa hawaye na bin kuncinta.
Mari aunty Jameela ta kuma kai mata a karo na biyu kannan ta ce " you are very stupid, ya za'ayi tun ɗazun ina maki magana baki amsa min sai dai girgizamin ka?"
Aman da Bintu take ta dannewa har ya hanata amsa anty Jameela ne ya kufce mata wannan karon Allah yaso aunty Jameela taba tsaya a gabanta da an kuma ta ɗazun. " Tabd'ijam! Watoh saboda ɗazu na kyaleki ban nakad'a maki duka ba shine kika sake maimaitawa ko?"
Bintu kam ko jinta bata yi sabida azaba, cikinta ta riƙe sai amai take, tsabar babu komai cikin nata aman har kore-kore ta yi. Juyawa aunty Jameela ta yi don ganin irin galabaitan da Bintu ta yi, nan take ta ji ta fara tausayinta, kafarta Bintu ta riƙo daƙyar ta iya magana ta ce " aunty don Allah ki taimake ni zan mutu.... "
Cak aunty Jameela ta tsaya jikinta yai mugun sanyi da kalmar Bintu ta k'arshe, tunani abin yi take gashi babu kowa a gida duk sun tafi school daga ita sai mai-gadi. Duƙawa ta yi kannan hannu ta cire hannun Bintu daga riƙon da ta yi mata ta ce a karo ma farko cikin sanyi murya " ina zuwa" tashi ta yi taje kira direba yazo ya kaisu asibiti.
Suna isa asibiti aunty Jameela ta ciro ƙaramin katin da suka saba zuwa dashi ta miƙawa record officer da yake wurin ya ciro masu file ɗinsu, nuni yai mata da wata mata da take zaune a kujeran ƙarshe ya ce " kuje ki zauna acen daga wannan matar sai ke" kannan yaje ya saka file ɗin a layi. Basu da ganin likita ba saida misalin ƙarfe 10:30 suda suka je gun tun misalin ƙarfe takwas, aunty Jameela ta ja tsaki yafi a jirga tana dana sanin zuwanta, tsaki ta kuma ja ta juya ta kalli Bintu wacce tunda suka samu wurin zama ta fara bacci ta ce" da nasani na haɗoki da direba, shegiya sai barci take faman yi yanzu dole idan na koma gida ni zan ƙarasa sauran ayyukan don nasan ko na barsu a gun har gobe ba yi Ummi zata yi ba", tana cikin maganar ne aka kirasu, tashin Bintu tayi daga barci suka shiga. Kujeran dake gaban likita suka zauna, ya ce " wacece mara lafiya?"
"Ni ce" Bintu ta amsa cikin sanyi murya.
"Ok! Meke damunki?" Dr. Ya tambaya, yana mai dubata.
Bayani Bintu ta fara yi mishi, tana yi yana d'an rubuce-rubuce, mikawa anty Jameela prescription sheet yayi sannan ya ce " wannan shine magunguna da zaku siya."
_Please dudes ku yi haƙuri ba zaku ɗinga samun kamar yanda kuke so ba. Please bear with me._
*Mummy's friend ce 🤩*

ESTÁS LEYENDO
ILLAR RIƘO ('yar riƙo) sabon salo
Historia CortaEdited version ɗin illar riƙo wannan labarin ba sabo bane illar riƙo ne nayi editing na sabon ta shi dan kuji daɗin karanta shi asha karatu lfy.