17

91 8 0
                                        

*🤦🏼‍♀🙆🏼‍♀ILLAR RIƘO*
     _*('Yar riƙo)*_

            *Na*

_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_

_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_

_____________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*Dedicated to all my fans*

_*Wannan naki ne Naman Ali (Maye gurbi fans group) kyauta daga Mummy's friend kiyi yanda kike so dashi ba mai ce maku don me.*_

_*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_

_*Manzon Allah S.A.W ya ce : Shaidan bakauye baya halasta akan d'an birni*_

_*Page 17*_

      Bayan an tashi masu har aji Ruqayyah ta biyoma Bintu. A tare suka baro makarantar, hanyar gidan su Ruqayyah suka  dosa suna tafe suna hira har suka isa gidan,  gate Ruqayyah ta buɗe suka shiga.  Kallon gidan Bintu ta shiga yi a zuciyarta  ta ce " ga gida har amma..... "

Tab'ata da Ruqayyah ta yi ne ya katse mata tunanin da take, Ruqayyah ta ce " ke ta backyard zamu bi, bana son Umma ta san na dawo."

   Hakan kuwa aka yi ta backyard ɗin su biyo, wani matsakaiciyar daki suka shiga da sallama,  ɗakin ne da ya kunsa duk abubuwan more rayuwa sai dai kash! babu soyyayar iyaye wanda wani jigo a cikin rayuwa. Gefen gado Bintu ta zauna tana ƙarewa ɗakin kallo. Dan matsakaiciyar fridge ɗin dake ɗakin Ruqayyah ta je ta cirowa Bintu drink sannan ta zauna daga gefenta, ta ce " Bintu wannan shine ɗakina a ciki nake rayuwa ni ɗaya babu mai zuwa duba ni, duk lokacin da kika wani ya shigo nan toh ko sharri aka min gun Daddy ya gaza haƙuri ya biyo ni ko kuma aunty Jummai (sunar matar mahaifin Ruqayyah) ta biyo ni don ci mani mutunci amma koda zan shekara ina rashin lafiya babu mai zuwa duba ni."

Ajiyar zuciya Bintu ta yi tavce " Allah ya mana muwafaka,  ɗauki min maganin na tafi don na san aunty Jameela nan na jira na."

   Kan mirror Ruqayyah ta je ta ɗauko wasu kwalabe guda biyu sannan ta dawo ta zauna kusa da ita ta ce " ga wannan ki tafi dasu for a try, duk sanda kike cikin damuwa sai kisha sha kwalba ɗaya, zaki ji damuwar taki ya kau."

Cike da mamaki Bintu take kallon ta saida ta bari ta gama magana sannan Bintu ta ce " haba mana Ruqayyah wace irin damuwa zai sa mu mukai kaimu ga hallaka?, wannan  ai drug abuse, shaye-shaye kenan kike son na fara.  Kuma ki tuna fa Manzon S.A.W ya ce : duk abinda yake saka maye haramune, kuma ki sani dukkan tsananin yana tare da da sauki. Ki ji  tsoron Allah Ruqayyah ki daina domin illolin shaye-shaye yawa garesu."

Tashi ta yi ta ce "  ni na tafi kuma nagode da kulawarki gareni, sannan ta ajiye kwalaben gefen gado."

Miƙewa itama Ruqayyah ta yi jiki a sanyaye ta ce " Nagode Bintu da wannan tunatarwar. Bari na ɗan taka maki".

"Na yafe ki barshi kawai" Bintu ta faɗa a takaice sannan ta yi ficewarta daga ɗakin.

Haka Ruqayyah ta koma ta zauna ta faɗa duniyar tunani, jikinta yai matuƙar sanyi da kalaman Bintu, inama a ce tana tare da Ummanta da bazata faɗa cikin wannan halin da ta tsinci kanta ba, hannun tasa ta goge kwanlan dake zuba kan kunci ta sannan ta ce a fili " dukkan tsanani yana tare da sauƙi" miƙewa ta yi ta faɗa a bayi ta watsa ruwa ta ɗoro alwala tazo ta gabatar da sallah, nan ta shimfiɗe kan ta sani barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita.

°°°°°°°°°°°°°°°°°

      Wata hadaddiyar mota ce ta yi parking bakin gate ɗin gidansu Yusrah.  Jim kaɗan sai ga wata matashiyar budurwa ta fito daga motar, ta banƙaro ƙirjin nan (chest out). Taku take a hankali kamar wacce take tausayi ƙasa ta zaga zuwa ɗayab gefen da mallakin motar yake zaune, kanta ta saka ta tagan motar wanda ya yi sanadiyar bayyana dukiyar fulaninta, ta ce "baby sai yaushe kenan?"

Hannu yakai da niyya shafan abinda idonsa ya gane masa.

Ta bige masa hannu ta ce " Wai meye haka Suwaid,  baka tsoron wani yazo ya gan mu ne?"

"Lubna me kike kamar wacce bata waye ba, meke ciki idan an gamu? Ina ruwa wani damu? anya kina ma sona kuwa?".

"Haba mana mai ya kawo wannan zance, a kaima sheda ne kan irin son da nake maka."

Wani mayaudarin murmushi ya yi, ya yi nuni da bakinsa sannan ya ce " prove it."

Waige-waige ta fara yi ta ce " tam rufe idonka."

Yadda ta ce hakan ya yi.

Ganin babu wanda yazo wucewa a daidai wannan lokacin ta sunbace shi ta kwasa a guje.

Buɗe idanuwansa ya yi yagan wayam babu ita babu dalilinta.  Hannu yasa ya shafa leɓensa ya yi murmushi kannan ya ce "yarinya da sannu zaki shigo hannu." Sannan yaja motarsa ya  wuce.

_*kuji tsoron Allah kusani duk  abinda kuka aikata ubanjigi na ganin ku. Karki biyewa saurayi da sunar wayewa ya kaiki ya baro. Soyayyar shan minti haramun ne.*_

    Daidai bakin ƙofar falon ta tsaye saida ta daidaita natsuwarta kannan ta shigo falon da sallama. Zaune ta iske Ammi da alamar ita Ammin ke jira don har ta fara gyangyaɗi.  Sadaf-sadaf ta yi kamar barauniya har ta kusa kaiwa bakin ƙofar ɗakinsu, turus ta ja ta tsaya sakomakon tambayar da Ammi ta jefo mata " Luba daga ina kike da wannan tsohon daren?"

Kai Luba ta daga ta duba time,  zaro ido ta yi ganin har ƙarfe 11pm ta yi,  kame-kame ta fara yi ta ce " uhm...daman gidansu...uhm."

" Hmmm luba kenan ki ji tsoron Allah a duk inda kike.  Kema dai kinsan idan Abbanku na nan yau sai ranki ya ɓace matuƙa."

"Nagode Ammi."

"Kar ki min godiya na kyaleki ne domin yau ne karon farko, ina fatan ya zame maki na ƙarshe " Tana idda zance ta tashi ta yi tafiya ɗakinta ta bar Luba tsaye a gun.

Tana tafiya Luba ta fara kwaikwayanta tana gamawa da ƙarasa da faɗin " wallahi matan nan badai sa ido ba, yanzu na gane dalilin da yasa Baba take mata wulakanci."  Tashi ta yi ta ƙarema kanta kallo ta ce " am good to go, wallahi fitan dare kuwa yanzu na fara."  Tsaki ta ja kannan ta yi tafiyarta ɗaki.

    Kwance ta same Yusrah sai shafan barci take hankalinta kwance tayi wani fresh da ita.  Tsaki Luba ta ja ta ce " wayuwa kawai,  ko yaushe zata waye da mutane?, In ba haka ace mutum yana jami'a ko nashinshini babu."


_Please don't forget to like_
_Share_
_Vote &_
_Comment_

_*Mummy's Friend ce😍*_

ILLAR RIƘO ('yar riƙo) sabon saloWhere stories live. Discover now