*🤦🏼♀🙆🏼♀ILLAR RIKO*
_*('Yar riko)*_*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
_____________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com_*Dedicated to all my fans*_
_*My namcy (pretty Aisha) wannan fejin naki ne ke dai ki yi yadda kike so dashi.*_
_*Page 8*_
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
_*Page 8*_
Washegari da wuri Bintu ta tashi ta kammala aiyukanta sannan ta tada Rahma domin ta haɗa masu breakfast. Addu'ar tashi daga barci Rahma ta yi haɗa da miƙa, tana murza ido ta ce " wai Bintu har lokacin tashin mun daga barci ta yi ne ko?, ko Mummy ce ta tashe ki ki yi mata wani aikin kike son na taya ki?", " a'a anti Rahma ni na tashi da kaina yau ina son muyi saurin zuwa skul ne, kin ga har ma na gama aikina", " toh ya yi kyau ni bari na ɗan kwanta har lokaci ta yi " Rahma ta faɗa sannan ta koma zata kwanta, " lah antina lokaci ya yi fa yanzu haka ƙarfe biyar saura 2mins fa, har ma an kira sallah ko. "
Da sauri Rahma ta sauko daga kan gado ta nufi kitchen ta ɗora ruwa domin tun ranar Daddy ya yi mata magana kan taba Rahma girki, ta bar mata ragamar yin breakfast kuma koda zata makara bata taɓa taimaka mata da aiki sai Bintu take taimaka mata da wanda zata iya, ta ɗora da da sauri ta nufi toilet ta ɗora allola, a tare suka gabatar da sallah ita da Bintu. A gurguje take aikin saboda gudun kar samnakon Bintu ya tashi a banza.
K'arfe 7.15 suka kammala shirin sannan driver ya tafi dasu makaranta. Suna isa skul cike da zumud'i Bintu ta fita daga mota tana mai addu'a addu'a Allah yasa Maryam ta samo mata ma'anar kalmar.
Haka ya kasance a gun su Yusrah itama da wuri ta tashi ta yi aiyukan da ya kamata ko gigin tasar Luba bata yi domin ba tashi zata yi, ita kuma bata son yau su makara, domin yau suna da Maths test. Ƙarfe bakwai daidai suka idda shirin su, Luba sai zunbure-zunbure take yi , zuwa makaranta da wuri yana cikin abinda ta tsana a rayuwarta yanzu sai an wani tsaya a assembly duk sai mutum ya gaji da tsayuwa. Ita dai tafi son ta gan suna zagaye makaranta suna picking ɗin nan da ake saka late comers.
Bintu na shiga aji ta iske Luba zaune "lah yau duk sammako na ashe da wacce ta riga zuwa"
" Mtsw! ke dai bari ai duk Yusrah ce ta saka mu zuwa da sauri wai tana da test."
" Ai hakan ya yi kyau, tashi mu tafi assembly kafin uncle Kabeer ya fara koran mutane."
"Ki tafi abin ki ni babu inda zani ehee" Luba ta ce fuskar nan a ɗaure tamau.
" Haba mana ƙawata don Allah ki tashi mu tafi kar yazo ya same mu" da kyar Bintu ta shawo kan luba suka tafi assembly.
Da misalin ƙarfe 10am aka buga masu break; zaune suke su uku Bintu, Maryam da Luba suna cikin abinci. Bintu ta ce " yawwa Maryam ya alkawarin mu ta jiya?"" Kedai inda kika nacewa abu toh sai kin sanshi, wai ma meye dalilinki na neman ma'anar kalmar ne?" Maryam ta jefo mata tambaya.
" Ni dai ina son sani ne kawai " Bintu ta bata amsa cikin sanyin murya.
Tab'e baki Luba ta yi ta ce " sai ku bari har mu idda cin abinci ko."
Suna kammalawa Maryam ta tashi zata tafi wasa Bintu ta ce " Maryam wai har kin manta ne?"

YOU ARE READING
ILLAR RIƘO ('yar riƙo) sabon salo
Short StoryEdited version ɗin illar riƙo wannan labarin ba sabo bane illar riƙo ne nayi editing na sabon ta shi dan kuji daɗin karanta shi asha karatu lfy.