9

128 9 0
                                    

*🤦🏼‍♀🙆🏼‍♀ILLAR RIKO*
     _*('Yar riko)*_

            *Na*

_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_

_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_

_____________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*Dedicated to all my fans*

_*Quote of the day:*_
_*Experience is a hard teacher, she give the test first & the lesson later.*_

_*Gaisuwan ban girma da jinjinar k'asaita ga 'yan uwana:*_

*Aunty Hauwa*
_(Oum Waleed)_

*Aunty Aisha*
_( Oum Akram)_

*Aunty Fatima*
_(Oum Inteesar)_

*Zainab*

*Hajarah*

_*Kune na farko zuciyata, zama tare daku yana sanyani farin ciki, zuciyata ba zata iya jariyam rashin ku ba, domin ku wani jigo ne na rayuwata. Bakina ba zasu iya furta irin soyayyar nake maku ba, kun zama ni na zama ku. My sisters I love you whole heartedly❤❤❤. Allah kare mu daga sharrin shaid'an ya haɗa kawunan mu. I love you wujiya-wujiya sistos😘😘😘.*_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

_*An karb'o daga Abu Hurairah, Allah ya k'ara masa yarda ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya ce:Yana daga cikin ingancin musulunci mutum ya bar abinda bai shafeshi ba/ babu ruwansa a ciki. Hadisi hasanun ne.*_

  _*Tirmiziyy ya rawaitoshi……*_

_*Page 9*_

Haka Jameela ta ci gaba da dukanta domin ga zaton ta pretending Bintu ke yi saboda ta ƙyaleta, ko jini dake fita daga goshin Bintu bata lura dashi.

Hannu ta daga zata kaiwa Bintu wani zabgan sai ga Umar ya shigo da sallama da gudu ya ƙarasa wurin wanda ya yi daidai da saukan bulala jikinsa, " wash..." ya faɗa da dan k'arfi domin bulala ta shige shi sosai, sai a lokacin Mummy tasan da shigowarsa.

Haƙuri ya fara bata kan ta barta dukanta haka "Mtsw! zaka tashi kaban wurin ko sai na haɗa da kai?"

"Mummy don Allah ki yi haƙuri, wallahi bulalan da zafi fa."

"Toh ni ina ruwa da zafin ta, haka kawai yarinya ta sanya ni asaran plate daga fara anfani dashi, saboda bata san zafinsu ba."

Ido Umar ya zaro cike da  mamaki a zuciyarshi ya ce " yanzu saboda plate Mummy tayiwa Bintu irin wannan dukan" girgiza kai ya yi cike da tausayin Bintu sannan ya ce “ please Mummy dan Allah ki yi haƙuri."

"Biya na zaka yi da kake wani bani haƙuri?"

"A'a Mummy nidai don Allah ki yi haƙuri."

"Mtsw!"  taja tsaki kannan ta yi tafiyarta ɗaki. Tana wuce ya juya zuwa inda Bintu take kwance, sunan ta ya fara kira a hankali domin shima ga zatonshi ta yi haka ne sabida Mummy ta tausaya mata , har saura uku yana kira sunanta amma shiru bata amsa masa,sunanta ya kuma kira wannan karo murya a dage amma still babu amsa, girgizata ya fara yi yana kiran sunanta amma still bata tashi, ana cikin haka sai ga Rahma ta shigo falon da gudun domin tun a bakin gate zaka ji murya Umar yana kwalawa Bintu kira, da gudu ta ƙaraso inda ya Umar suke tana mai tambayarshi abinda ya sami Bintu, shiru ya yi bai amsa mata ba ganin haka itama ta shiga kiran sunan Bintu, jin bata amsa mataba ya sanya ta kai hannunta saman kirjinta. Zaro ta yi ta kalli Umar sannan ta ce " yaya bata numfashi fa, ko ta mutu..." bata ƙarasa zance ba kuka yaci karfinta da gudu ta tashi ta shiga ɗakin Mummy ta ce " Mummy! Mummy !! Bintu ta mut…" dam Jameela ta ji kirjinta ya buga, da sauri ta tashi daga kwanciyar da ta yi, tare suka nufa falo da Rahma.

ILLAR RIƘO ('yar riƙo) sabon saloWhere stories live. Discover now