*🤦🏼♀🙆🏼♀ILLAR RIKO*
_*('Yar riko)*_*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
_____________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com_*Dedicated to all my fans*_
_*Wannan fejin tukuci ne gareki my namcy @ Aisha( ILLAR RIKO GRP) kiyi yanda kike so dashi.*_
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
_*Page 5*_
_*RANAR LITININ*_
Yau da misalin ƙarfe huɗu da rabi Mummy ta tada Bintu daga barci kasancewan ta littini yara zasu tafi makaranta. Da tashin ta kitchen ta nufa ta tattara kwanukan da suka yi datti takai baki famfo gudun karda ta wanke su a kitchen mummy tazo ta yita faɗa ta ɓata mata kitchen. Waka take tana wanke-wanke tana kuma tunawa da Innarta, sai ga hawaye na zuba a fuskanta ta ce a hankali wanda idan ba kusa kake da ita sosai ba baka iya jin abinda ta faɗa " Allah sarki Innata yanzu ko wake tayaki aiki?, gani a nan sai bauta nak..." shiru ta yi batare ta idda zance ba sakamakon taɓa ta da taji anyi, a hankali ta juyo don ganin ko waye. Murmushi ta yi ganin Rahma tsaye, itama Rahman murmushi ta maida mata.
" Ina kwana anti."
"An tashi lafiya 'yar kanwata."
"Lafiya kalau antina. Kofi kike so na wanke maki?."
"A'a Bintu nazo ne na tayaki aiki."
Zaro ido Bintu ta yi cike da tsoro sannan ta ce " Anti na gode, don Allah ki bar shi kar Mummy tazo ta maki faɗa."
Tsugunawa Rahma ta yi ta amshi soson wanke kwanonin ta ce " ba zata ta dake ni ba, kema kuma bazata bugeki ba."
"Toh Anti " Bintu ta faɗa jiki a sanyaye domin ita har ga Allah tsoron Mummy take sosai.
Rahma na ganin haka ta ce " kwantar da hankali, ai Ummi na barci bata tashi ko ba kuma Mummy bazata zo nan yanzu ba, kinga kenan babu mai faɗa mata ina nan."
Murmushi Bintu ta yi cike da yarda da zance sannan ta ce " na gamsu antina."
" Yawwa ko ke fa. Maza muyi sauri mu gama kafin a kira sallah sai na je na tayaki shara." Suna gama wanke-wanke Rahma ta share kitchen ita kuma Bintu ta sharo falo da ɗakin su sannan ta ɗebo ruwan ta yi mopping, tana cikin mopping aka kira sallah da sauri ta ƙarasa suka tafi suka yi sallah ita da Rahma. Suna iddarwa Rahma tashe Ummi ta yi sallah sannan tai tafiyar ta kitchen don yau so take ta ɗora ko da ruwa ne kan wuta kafin Mummy ta fito domin inta fito ba zata barta ta yi ba, ta kuwa ci sa'a tana gama ɗorawa, sai ga Mummy ta fito daga ɗaki, daga nisa ta hangi mutum tsaye a kitchen, da gudu ta ƙaraso kitchen don gasgata abinda idonuwanta suka gane mata. Salati ta saki gani Rahma da Bintu tsaye gun gas cooker ɗinta ta ce da ihunta " Rahma gobara zaki sa mana a gida, wai bana na ce kar na kuma ganin ki a kitchen ba?."
" Mummy nafa iya, kuma duk cikin ƙawaye na ni ɗaya ce kawai ban iya girki ba, kullum sai sun min dariya " Rahma ta faɗa haɗa da turo baki.
Kusa ta ita Mummy ta matso ta ɗaga hannu zata buge ta kenan sai ta ji murya daddy yana faɗin " kar ki kuskura ki bugeta" Waigawan da zata yi ta gan daddy tsaye ashe duk abinda ya faru akan idonshi ne.
"Toh kasan abinda ta yi ne da zaka ce kar in taɓa ta, salon ka bata yarinya kawai" Mummy ta ce rai a ɓace.
" Duk abinda ya faru akan idona ya faru, dawowata daga masallaci kenan zan shiga ɗaki na ji muryarki ki na faɗa da sanyin asuban nan. To wai ke yaushe zaki fara barin yarinya nan tana koyan ayukan gida ne? ko sai lokacin da girma yazo maki kina son a tayaki amma saboda rashin sabo su ki yi, toh wallahi bari ki ji nasan kema kin sani a kauye kamar Rahma yanzu tana ɗakin mijinta, ko kin fison sai mu auradda ita mijin ya korata gida wai tazo ta koya girki?"

YOU ARE READING
ILLAR RIƘO ('yar riƙo) sabon salo
Short StoryEdited version ɗin illar riƙo wannan labarin ba sabo bane illar riƙo ne nayi editing na sabon ta shi dan kuji daɗin karanta shi asha karatu lfy.